Hausa Novels and Stories

Idon Naira 4

Sponsored links

Daga haka ta fice daga ɗakin ba tare da ta sake cewa komi ba maryamah na bayanta.

Bayansu hafsatu tabi da kallo ƙwalla na taruwa a idanunta sbd tana kaunarsu Kuma tana Jin inama Suma zasu Dan kaunaceta su dukan zuciyoyinsu su huta da wannan zaman quncin dasukeyi su dukan.

“Hafsatu ki yi haƙury da halin abokiyar zamarki da ƴar mijinki ki rungumi ƴarki ta zama abokiyar hirarki da shawaranki idan Allah ya raya miki ita Ba lalle sai kowa ya soka a duniya za ka rayu ba

bai zama lallai sai waɗanda ka ke tare da su sun nuna maka ƙauna ba

ki godewa Allah ba cutar da ke suke yi ba kawai dai basa shiga sha’aninki ne kuma basa maraba da ke a cikin gidan Kuma Inshallah wataran hakan ma saikiga ya wuce Kun zauna cikin walwala kaman baayiba

don haka ki yi haƙury tunda ke ma gashi Allah ya baki rabo sai ta zama abokiyar ɗebe miki kewa.”

Iyah ta yi maganar tana duban yadda hawaye ke gudu a idanun Hafsatu

ta cigaba da rarrashinta da kalamai masu daɗi har sai da ta tabbatar Hafsatu ta samu nutsuwar zuciya.

Kwanakin da suka biyo baya gaba ɗaya Iyah ce ke shigowa tana hidimar kula da Hafsatu tunda bata da kowa a garin Kano bata da wani sauran gata da dangin da za su iya yo tattaki tun daga Adamawa su kula da ita ba.

Ranar suna Jaririya ta ci suna ZAINAB sunan mahaifiyar Malam Adamu da ta jima da rasuwa ba wani taro aka yi sosai ba daya wuce maƙwafta da jama’ar arziƙi da ya ke huɗɗa da su a unguwar Sabida shi ma zuwa ya yi garin Kano don kasuwanci, amma asalinsa ɗan Lokoja ne ba shi da ƴan uwa sam a garin sai dai abokan kasuwanci da maƙwafta kawai.

Iyah ita ta dinga kulawa da Zaynab da Hafsatu har suka gama wanka

sam bata taɓa gajiyawa ba tamkar jikarta ta jini haka ta ɗauki Hafsatu shiyasa Hafsatun ke jin cewa bata da tamkar Iyah don ta maye mata gurbi da dama waɗanda danginta na jini ne kawai za su iya mata hakan.

Har kawo wannan lokacin da suka gama wanka koda wasa Maryamah bata taɓa shiga ɗakin Hafsatu ta ga ƙanwarta Zaynab ba tun ɗaukar da ta yi mata ran da aka haifeta bata sake daukantaba saidai lokuta da dama idan Hafsatu tafito da zainab din haka zata ringa kallonta tanajin rashin nutsuwar zuciya.

Daga Iyah sai Malam Adamu su kaɗai suke nuna soyayyarsu ga Hafsatu da jinjirarta Zaynab harsun Saba.

Watannin Zainab shida da haihuwa ciwo me zafi ya kama Hafsatu aka wuce da ita asibiti kwananta tana jinya Ubangiji ya amsa rayuwarta ta bar jaririyarta Zaynab.

Faɗin irin tashin hankalin da Malam Adamu da Iyah suka shiga ba zai faɗu ba, don rumgume gawar matarsa ya yi yana kuka me asalin motsa zuciyar duk wani me saurarensa.

Har aka kai Hafsatu makwancinta Malam Adamu baya cikin hayyaci da nutsuwarsa tun yana kuka da idanunsa har ya koma na zuci wanda yafi na fili illah.

Daga Hadeeza har Maryamah mutuwar Hafsatu ya doke su matuƙa sbd halayenta masu sanyi da hakuri duk da kusan su dukan sunada hakr sosai sai dai lokacin da aka watse zaman makoki sai kowa ta koma sabgar gabansa Iyah me ƙosai ita ce ta sanar da Malam Adamu cewa za ta riƙe masa Zaynab har zuwa lokacin da za ta cika shekaru biyu ko uku sai ta bashi abarsa ya baiwa matarsa riƙonta Sabisa ta san Hadeeza ba za ta raini Zaynab a yanzu ba Ranar Malam Adamu yayi sabon kukan rashin hafsatu dukkanin ƙauna da soyayyar da ya ke ma Hafsatu sai ya dawo kan Zaynab har ma da ƙari.

A kwana a tashi Zainab tafara wayo yar kyakkyawa da ita da kamanninta na uwarta na sake bayyana matuƙa kamar yadda kullum kwanar duniya ake sake ninka ƙaunarta a zuciyar Malam Adamu Koda wasa Umma da Maryamah basu taɓa cewa za su shiga gidan Iyah su ga Zainab ba tun Iyah na mamakin ƙarfin halinsu har ta daina ta cigaba da kula da Yarinyar har ta cika shekara guda tana gudunta ko’ina Duk in da suka shiga da Zainab sai an yabi kyawunta shiyasa Iyah ke dagewa wajen yi mata addu’a sabida gudun bakin mutane.

Zainab na cika shekaru biyu da rabi Iyah ta tattaro kayanta ta dawo ma Malam Adamu da ƴarsa hannunsa domin ta so cigaba da riƙon Zaynab amma sai aka aiko cewa mahaifiyar Iyah babu lafiya dole za ta tafi jinyarta acan gida ƙauye Hakan shi ya tilasta dawo ma Malam Adamu da riƙon ƴarsa Zaynab hannunsa wannan ne kuma ya zama silar da riƙon Zainab ya dawo hannun Umman Maryamah wacce daga ita har Maryamah ba su taɓa nuna so ko qi wa zainab ba.

Kasancewar Malam Adamu tsayayye kuma jajirtacce a gidansa shiya sanya Umma ta kasa cewa ba za ta riƙe masa Zainab ba

Don haka ba don ranta ya so ba ta amshi riƙon Zainab.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button