Hausa Novels and Stories

King Zaid Complete Hausa Novel 2

Sponsored links

Chuchu rike Laila ta yi tana fadin “Laila mu gudu”

Zaid na kallon Laila cikin tsananin sha’awa ya ce relax ‘yan mata, Karki tayar da hankalinki

‘Kokarin juyawa Laila ta yi zata gudu Zaid ya yi saurin rike mata hannu yana fadin “Ina zaki je kuma?”

‘Kokarin fisge hannunta ta shiga yi tana fadin “ni ka ‘kyaleni, an ce maka ni shasha ce da zan baka jikina?”

Mikewa Zaid ya yi yana kallonta sannan ya ce mecece ke Idan ba shashasha ba, kin manta kinsa kanki a chacha kuma na cinyeki, yanzu dake da jikinki duk mallakina ne, abinda na ga dama shi zan yi dake

Cikin fushi ta ‘kwace hannunta daga nashi, Kallonshi take yi da jajayen idanunta da hawaye ke fita daga ciki, nuna shi ta yi da yatsa ta ce kai Kasan ni wace ce? Har kai ka isa ka mallakeni, ka fadi ko nawa kake so zan baka amma Ba za ka taba samun jikina ba

Kallon tarin kudade da diamonds da sauran kayan da suke tebirin chacha ya yi, tura mata ya yi zuwa gabanta yana fadin “ga kudadenki, ga wayarki, ga diamonds da makullin motarki bana bukatarsu, what I want is you, i just wanna fuck you bitch”

Cikin ‘bacin rai ta daga hannu zata koda masa mari ya yi saurin rike hannun, kallon kallo suka shiga yi a tsakanin su

“Ko a mafarki Kar hannunki ya yi kuskuren taba fuskar Zaid” Zaid ya fada yana kallon idanun Laila

“Kaima kada ka ‘kara dangantani da karya”

‘Karamin dariya Zaid ya yi ya ce to me ce ce ke Idan ba karya ba, karuwa mara tarbiyya, kina da sunan daya wuce wadan nan dana lissafo?

Wani irin kallon ‘kiyayya ta shiga binshi dashi, ji tai duk duniya babu wanda ta tsana kamar shi…batare data ce komai ba ta juya tai hanyar barin Club din, Chuchu na biye da ita

Zaid kalmasa hannayensa ya yi a bisa ‘kirjinsa yana binta da kallo, yanayin yadda take juya duwaiwukanta na ‘kara tayar masa da hankali, cikin wani yanayi ya kalli Yusuf yana fadin “gaskiya ta hadu sosai, ita kawai nake bukata”

Yusuf ya ce amma ya zaka barta ta tafi free

Zama Zaid ya yi yana fadin “ka manta wanene Zaid kenan, ai tunda na ji kwadayinta dole saina sameta, nasan zata yi dadi sosai”

Zaid da Yusuf suka cigaba da harkokinsu

Chuchu da Laila katafaran gidansu suka wuce, Laila dakinta ta shiga cikin tsananin ‘bacin rai, kai tsaye ta je ta bude durowa ta dakko fodar ibilis (cocaine) zama ta yi kan kujera ta zuba fodar ibilis a table sannan ta shiga shaka tana samun sauki daga radadin da zuciyarta take mata, haka ta cigaba da shakar fodar har bacci ya dauke ta a wurin

Washegari da sassafe Chuchu ta shigo ta sameta kwance kan kujera, tashinta ta shiga yi

“Laila! Laila!”

Bude ido Laila ta shiga yi a hankali, idanunta sun yi jawur, kallon Chuchu take yi sannan ta rike kai tana ‘kara tuno abubuwan da suka faru jiya

“Ki tashi ki shirya mu tafi makaranta” Chuchu ta fada tana kallon Laila

Girgiza Kai Laila ta yi ta ce A’a babu inda zan je, ki tafi kawai

“For how many weeks bama zuwa makaranta, kin manta munyi alkawarin Ba za mu ‘kara maimaita shekara ba”

Laila mikewa ta yi tana fadin “I’m not in the good mood, babu wanda ya taba cina chacha, koda yaushe ni ce a sama, amma wannan dan iskan matsiyacin ya zo ya dawo dani ‘kasa, sannan ni yake kira da karuwa mara mutunci”

“Ki manta dashi Laila, shi matsiyacine, bai san wacece ke ba, Karki ‘bata lokacinki a kanshi”

Wasu hawaye suka shiga zarya daga idanun Laila tana fadin “da ciwo a kira mace da karuwa, ni da ban taba sanin wani da namiji ba a duniya shine sai ya ce min karuwa, Kinsan dai duk rashin jina ko saurayi ban taba yi ba”

Cikin tausayi Chuchu ta jawota jiki ta shiga rarrashi “ki yi hakuri Laila, please ki kwantar da hankalinki, kada kisa wannan tunanin a zuciyarki, Kinsan dai a kowani lokaci Ina tare dake”

Haka Chuchu ta cigaba da rarrashin Laila har ta samu ta kwantar da hankalinta sannan ta je kitchen ta hada mata breakfast ta kawo mata, Bayan Chuchu ta kammala breakfast bathroom ta shiga ta yi wanka bayan ta fito ta shirya cikin wani ‘karamin riga mara nauyi da tsawonshi ya tsaya dai dai rabin cinya, fadawa ta yi kan gado ta kwanta

Chuchu ce ta turo ‘kofa ta shigo

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button