Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 16

Sponsored links

Idanunta da suka kaɗa jajur tai ƙoƙarin ɗagowa, sai dai ta maidasu da sauri zuwa ƙasa. “Uwa amma kin faɗamin na cinye jarabawa ta biyu da zarar ya aura cika makin matansa shine matakan nasarata, yanzu haka akwai su su biyu da suka rage ɗauke da aurensa a kansu, zasu miƙasu garesa a karshen watannin nan kamar yanda na samu tabbaci. Taya zamu shigo da wata bayan aikin ya cika. A yanzu ya rage kawai samun cikar burina na ƙarshe ne a kansa. Miye dalilin shigowar wannan yarinyar abinda bai shafeta ba? Mizai hana ai mata wani hukuncin daya dace da ita?…

Hannu ta ɗaga mata cikin tarar numfashi da ƴar hasala-hasala, da kakkausar murya tana mai nunata da ɗanyatsa “Amma har yanzu ban sanar dake wadda ta dace ba, kuma damun san cutarwace na umarninmu gareki bazamu ce ta shigo ba”.

“Hakane Uwa, a gafarce ni. Sai dai Mahaifiyar Zak…….”.

Ta faɗa da alamun shiga tashin hankali mai girma, amma kallon da Uwa ta watso amata ya hanata ƙarasawa.

Bata tanka mata ba, sai dai yanayinta ya nuna a hasale take, dan cikin kaushin murya da zunzurutun jin zafi ta kaɗa ƙahon hanunta mai kama da kwarkwaron gidan dodon koɗi. A take haske ya gilma, sai ga farar takarda a hanunta. “Ƴar shila burinta shine ɗaukar fansa, domin biyu a cikin masu ɗakin Malik-alMuluk da suka shuɗe jininta ne. Burinta shine bin kadin jininsu ta hanyar bayyanama duniya ko kawar da shi. Bayyanawar tata kafin cikar burinki faɗuwarki ne, a yanzu haka kuma ta haɗu da mai taimaka matan harma sun gama magana”.

Sosai zuciyarta ta ƙara harzuƙowa. Amma sai batace komai ba saboda ganin Uwa a hasale take da ita. Cikin yin ƙara ƙasa da kai tace, “Da ace bayan cikar burina ne kauɗi da ƙudirin ɗaukar fansar wannan yarinya ya shigo haske ne ga cikar burina. Dan zata ƙarasamin aikin ƙarshe da zanyi. Amma tunda ta shigo a tsakkiyar labarina dolene ta fuskanci hukuncin daya dace da ita. Idan ita bazata mutun ba shi a kawar min da shi mana Uwa”.

“Hakan mai sauƙi ne, sai dai shima babu buƙatar mutuwarsa, dan zai iya mana amfani a gaba. Sannan shi rabata da shi shine mafi ƙololuwar hukuncinsa. Dan haka daga nan zuwa safiyar kowace juma’a ta ƙarshen shekarar nan ki tabbatar an zarga igiya tsakaninta da Malik-alMuluk, a dakatar da kai masa matan da suka rage a kaita garesa bayan tarewa, dan da ita zamu cigaba da amfani har samuwar cikar burinmu ga kowa!!.”

Da sauri ta ɗago kai jin muryar nayin nesa da ita, sai dai kafin ta iya furta wani abu Uwa ta ɓace daga ɗakin tamkar guntun girgijen hadari a tsakkiyar fararen gizagizai. Zumbur ta miƙe tana mai dafe kanta dake sara mata, wani irin tuƙuƙi da ƙaiƙayin mai zafafa ruhi zuciyarta ke mata. Sai dai sanin wacece Uwa ya sata jin ɗan sassauci kaɗan, amma ruɗani mai ɗauke da abubuwa masu matuƙar yawan gaske da fassarasu a ɗauka shekara dubu bisa dubu ba’a kammala ba na neman danne wancan ƙwarin gwiwar. Taya ruhin ƴaƴan sarakunan ƙasar Ruman basu bata matsala ba sai ƴar talakawa ƙasƙantattu? Dolene yarinyar nan ta ɗanɗana kuɗarta na hukuncin shiga gonar daba tata ba ƙwarai da gaske, sai tayi wasa da ita a tsakkiyar titi wasa irin na ɓera a hanun mage, dan ko ita Malikat bata isaba..

(Tofa masu karatu, ita kuma wannan wacece ita? Iffah fa ta taro match ɗin da babu players. Kumuje zuwa dai muga yaya wasan zai kaya🚴🏼…)

A ɗan firgice ta buɗe idanunta tare da tura hannu ƙarƙashin filon data tada kai ta sake danne wayar dake faman ɓurari cike da tsoron kar Ummu ta jiyo, dan tasan Babiy da Hanash basa gidan. Ajiyar zuciya ta sauke mai matuƙar ƙarfi da zaro wayar, cikin rawar jiki ta dannata a silent. Tamkar jira kiran ya sake shigowa kuwa. Idanunta masu matuƙar girma da haske ta waro sosai ganin mai kiran, ai batama bari tayi ring na biyu ba taa ɗaga tare da kaiwa kunnenta tana direwa a gadon.

“Kina jina?”.

Aka faɗa daga can. Kanta ta jinjina masa tamkar tana gabansa dai-dai tana leƙawa tsakar gidansu. Daga can gefen da Babiy ke kiwon tsuntsaye ta hango Ummu, dan haka ta sauke ajiyar numfashi da fara magana cikin raɗa.

“Ina jinka Sir! Ta samu ne?”.

“Babu lokacin dogon magana Iffah, kiyi ƙoƙari daga nan zuwa awa ɗaya ki sameni, dan kuwa mun tsinta dami a kala Ajmal ya shigo Ruman, kuma a yanzu haka mun gama magana da shi sai dai ban sanar masa ainahin zancen ba, ya kuma buƙaci haɗuwa dake…..”

“Ya ALLAH! Alhmdllhi. Naji daɗi matuƙa wlhy Sir. Insha ALLAHU duk yanda zanyi kuwa zan fito ka saurare ni”.

“Okay”.

Kawai ya faɗa yana mai yanke wayar. Itama shiri ta shiga faman yi a gaggauce, tare da tattare takardun dukkan bayanai data tattara waje ɗaya. Bakinta ɗauke da addu’ar samun nasarar amincewar Ummu abisa ƙaryar data shirya akan fitar ta fito. Daga inda Ummu take tako zubomata ido na alamar tuhuma. Gareta ta ƙarasa cikin danne komai da karsashin data aro. “Ummu kiran gaggawa na samu daga Ikram. Inaga dai abinda muka jima muna jirane ya fito”.

“Amma Iffah….”

“Ummu dan ALLAH kar kice a’a”. Iffah tai saurin tarar numfashinta cike da marairaicewa. “Ni ba hanaki zanyiba, sai dai wannan yawan fitar taki a kwanakin nan bana zuwa makaranta ba ya fara damuna Iffah. Shin kin manta halin da muka shiga da wanda zamu iya shiga a yanzu? Ina jin tsoro wlhy, matuƙar tsoro a duk sanda kika fita koda makaranta ne”.

Sosai tausayin Ummu ya sake mamaye zuciyar Iffah, ta haɗiye hawayen da suka taru mata a ido tana ƙaƙaro murmushi. “Insha ALLAHU Ummu babu abinda zai faru, wanda ya farun ma a baya bazamu taɓa mu yafe ba. Fita ta kuma ta daina baki tsoro, tunda kinga duk sanda zan fitan ina suturta dukkan jikina”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button