Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 26-27

Sponsored links

Kwashe kayan karton Cele tayi tare da na Maheerah sannan ta Kama kunnen kwarton tace wato Kai kunnen kashi ne dakai matar wani kake bi har gidan mijinta Kai ga tsohon bunsuru,kasa magana yayi ya hade hannaye biyu Alamar bada hakuri Cele ta Kama gashin gemun ta yanke rabi ta bar Masa rabi tace kana motsawa Dan ubanka wlh sai na tsaga ma jikinka,bai San me tace ba ya mike zai gudu ta zabga masa duka a dokin wuyansa tace zauna,So yake ya kwaci Kansa shi ba lusari bane gani yayi da gaske Cele zata wulakantashi ya tashi ya kwaci kayansa ta karfi Yana zage zage,ya duka Yana kokarin saka wandonsa Cele tasa kafa ta daki duwawunsa ya tintsira Saura kadan ya fadiya juyo a zuciye ya Mari Cele sabo da kwallon Dan Iska ne bashi da mutunci,Cele haushi yasa tasa Rezar ta tsaga Masa bille kato a barin duwawunsa daya, larabawa da kwailo ihu ya saki ya kwalla Kara ko wandon Bai karasa sawa ba ya fice da gudu,Ahsan Yana Palo yaga kwarton ya fito da wando a hannu da riga Yana Kare gabansa, Maheerah Cele ta kalla ta fada toilet da gudu ta kulle da key Cele tace Zaki fito ne wallahi ko ba yau ba kafin na bar gidan Nan sai na Miki billen Yan fulani.

Maheerah ta tsorata yanda taga Cele ta tsagawa Saurayinta duwawu cikin dare ta fice daga gidan gaba daya ta tafi gidansu Kai Kara gwara a dauki mataki akan cele gaskiya ta gaji.

 

Ahsan ne ya shigo dakin Cele da lalube Yana so zata bashi shayi ta fito da wanka zata Yi Shirin bacci ta ganshi zaune a gefen bed dinsa tace gaskiya makafi da basira suke ji yanda ya gane Yana iya zuwa da Kansa,ganin baya gani Cele tace su Saluhu ba a gani me Zan zauna Ina wahala ta cire towel din ta jefar sintir da ita,Ahsan dariya ta kamashi ya boye ta a ransa ya sake zooming idanuwansa Yana ta Shan kallo a hankali yanda baza ta ji ba ya furta Astagafurillah,Cele taje jikin mudubi harda karewa kanta kallo tayi girgiza tace Kai cika fa nake duk na bude sai kiba nake kalli jikina ga cikina tumbini ko cuta ce oho, Abubuwa haka Kai Cele kinfa hadu sai babban Alhaji, Ahsan ko kyafta Ido bayayi ya manta shi makaho ne,Jin zaiyi loosing control ya rufe idonsa har Cele ta shirya ta gama komai ta saka kayanta Riga da skert sannan tazo gabansa tare da rike Masa hannu tace Allah sarki Dan makahon Maheerah,Idonsa ya Bude a hankali yayi wani ja,Cele tace Kai Kuma lafiya uhm ta ja shi ya mike tsaye,Mutumin ba hakuri hannunta ya fisgo ta fado kirjinsa ya rungumeta sosai abinda bai taba ba,Cele tayi lakwas tana shakar kamshinsa,kanta ta dago a hankali tana kallonsa tace Haram,Kamar ta tsikara Masa Allura ya matsa da sauri daga jikinta yana istingifari,dariya ya bata yace uhm ta rike hannunsa Suka fice.

Washe gari Ahsan ganin Maheerah bata gidan komai Cele sai taga Yana yi da Kansa normal ya dawo Yana gani,Ido Cele ta zaro Murmushi ya saki ya nunawa Cele da hannu Wai Yana gani dama amma tayi Shuru da bakinta,Cele tunawa tayi jiya ta gama tsirara a gabansa Takaici ya kamata da kunya ta tashi ta gudu daki ta buya tana cewa wayyo ya ga komai nawa shike nan,dariya Ahsan yayi yasan me ta tuna.

Tunda ta buya bata fito ba sai da me karatu tazo Hajiya Hauwa tazo ta koya Mata ta rubuta sosai ta tafi ta bar Cele da hadda.

Baffa Yana zaune ya hakimce,takun mutum yaji ana taga steps a hankali,wani kamshi na musamman ya daki hancinsa,a hankali ya juya Suka Yi Ido biyu da Mami,Ido ya zuba Mata ta wani tsare gida wai aji ita,Sallama tayi Masa ya amsa da fara’a ta zaune ta wani kame, ko gaisuwa babu ne Baffa ya tambaya,Mami Fuska ta yatsina ta dauke kai, Haba ranki ya dade tuba nake yi har yanzu baza ki yafe min ba ne, haba my Uniform ko Ina Zan Shiga sai dake,me farar aniya, idan ba ke a rayuwa ta bazan taba rayuwa ba cikin Jin dadi,shifa tuwo duk darajarsa sai an Sanya miya,bazan sake rikon ki da Wasa ba har abada,kece me sharen min hawayena bazan sake saka ki kuka ba,Dan Allah kiyi hakuri ki yafe tunda na ganki karfin da nake ji ko Zaki albarka, bazan Kuma rike ki da Wasa ba,Zan baki komai da kike so sabo da kece farin cikina,a kanki na San Mene so ma Kuma daga ke bazan sake ba na rufe kofa,waccen ma kaddara ce amma idan badan ma barbade aka min ba ta ya za ayi na iya juya Miki baya,Ina tabbatar Miki asiri aka Mana Ina ji a jikina to wallahi karyar makiya Yan bakin ciki Allah ya sake hada mu har abada Muna tare, kiyi hakuri ki yafe min dan Allah ki sai na sake durkusawa Baffa ya zube gwiwoyinsa a kasa,Mami kanta ya wani Kara girma,Baffa yace haba yar budurwata…Mami duk yanda ta Kai da danne dariyarta ta kasa Wai budurwa Murmushi tayi ba tare data shirya ba,ya sake cewa My Baby,the love of my Life, Sweetheart,my Angel,my Sugar cake,Mami sai dariya take tace Ni dai ka zauna karka dameni,Kin bani dama na zauna ya tambaya? tace ae yace ato idan baki bada dama ba nayi ta Zama a Haka Zan iya kwana ma..

Mami ce ta Fara magana cikin salo da kashe murya ka tsaneni babu dalili,na soka na kaunaceka babu misali Amma Kai baka ganshi ba,ba irin rokon da ban maka ba Amma kaki min uzuri sai da ka sakeni ka dinga sakina har igiyoyina Suka Kare wannan wanne irin cin mutunci ne,idan za ayi sulhu ba a tuna baya Salma,dan Allah Ni dai na gane kurena naci kwal ubana na horu haka ki yafe min idan ba so kike zuciyata ta buga ba to ki hakura a bar zancen tuna baya yanzu mu maida auren mu ko ya Kika ce,Harararsa tayi tace ya wuce kawai badan halinka ba sai dan yarana,yace naci albarkacinsu hakan ma na gode Allah ya biya,Mami ta mike tace Ina zuwa ta Shige kitchen,Baffa tana kulewa yace yessss….Finally Alhmdllh,kayan ci da sha data shirya Masa ta kawo Masa ta jera sai kallonta yake yace Allah ya Kara Miki lafiya da tsawon rai,Ameen Mami ta furta tana cewa saura ka kara bata min rai dan ma dai Kawai ka samu Ina sonka,soyayyarka a zuciyata ta Zama ciwo shi yasa,Baffa yace ai ko babu kafa na tako da gudu wajenki Matukar kece, ya dai kamata ka sani so ba kudi ne ba bare ka debo ehe,Baffa yace na tabbatar Yana bude abincin,ta zuba Masa yace ai Baki Isa ba tare zamu ci,spoon ta sa suna ci tare suna hirarsu kamar Matasa.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button