Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 40

Sponsored links

A hankali ta matse fuska sai kuma takai hannu kan shafaffen cikinta dake mata zafin yunwa. Rabonta da abinci tun yammacin jiya, dan ƙin cin abincin da aka kai mata da dare tai a kurkuku. Zamewa tai a hankali ta kwanta a gadon tana cigaba da matse fuska. Dubanta ta kai a karo na biyu kan kofin shayin da ya bata ta ɓalla masa harara kamar shi ya hanata abincin, sai kuma tai juyi ta maida fuskarta ɗayan side ɗin tana ƙara cure jikinta waje guda hanunnta na kan cikinta..

 

A hankali ya tura ƙofar ya shiga idanunsa da hankalinsa gaba ɗaya na kan wayar hanunsa mai shegen ƙyau da ɗaukar ido kamar wani glass. Ciki-ciki yay sallama a ƙasan maƙoshi, batare da nuna alamar tuna yabar wani a ɗakin ba ya nufi ƙyaƙyƙywar kujerar zamansa ta musamman ya kai zaune a ƙasaitance. Wani kalan zaman isa da izzar mulki yay har lokacin idonsa akan wayar da alamar serious abu yake yi. Sassanyan ƙamshin turarensa dake ratsa mata ƙofifin hanci ya sata buɗe idanunta sannu a hankali. Har sun canja kala alamar barci ya fara ɗaukarta. Juyowa tai sannu a hankali batare da tunanin shi ɗin bane da gaske, dan indai ƙamshin sa ne ya riga ya gama kama duk bedrooms ɗin da yake amfani da su tsabar yanda yake wanka da turare kamar ruwa. Akan ƙyaƙyƙyawar farar fuskarsa da haske

wayan ya ɗan haska baƙin sajen siɗik ɗin gashinsa na ƙyalli ta sauke, yanda akai masa gyaran fuskar da wani irin haɗaɗɗen style yay matuƙar ƙara masa ƙyau. Sai taji tana buƙatar cigaba da kallonsa kawai, wani abu data kasa banbancewa na tsikarar ƙasan zuciyarta.

A jikinsa yaji ana kallonsa, dan haka ya tsaya cak da ga sarrafa wayar da yake faman yi cike da ƙwarewa. Sai dai bai ɗago ba har tsawon kusan minti ɗaya. Sai da yay bala’in shammatarta a bazata ya ɗago nasa kaifafan idanun sai cikin nata dake tsaye ƙyam a kansa. Da wani irin sauri ta fisge kanta gefe cike da pretending ta riƙe ciki tana murƙususu ita a dole bata da lafiya ma. Idanun nasa ya kaɗa kamar wani mai zuƙota ta cikinsu, sai kuma ya yamutse fuska da sake tsuketa ya ɗauke kansa shima. Ci gaba yay da sarrafa wayarsa batare da ya sake kallonta ba, hakan ya bata damar sake satan kallonsa ta ƙasan ido tana sake ƙaƙaro kukan ƙaryanta. lips ɗinsa ya ɗan ciza kaɗan batare da ya bar abinda yake ba a hankali can ƙasan maƙoshi ya furta, “What happend?”.

Baki ta tura gaba kamar bazatace komai ba. Sai kuma cikin kuka-kuka da kai tsaye za’a kirashi na shagwaɓa tace, “Ni dai kayan cikina zasu naɗe, yunwa nakeji ga headache, ga ciwo jikina namun ko’ina da ina”. Ta ƙare maganar tana ƙara tura baki.

(Yarinyar nan ko…) Ya faɗa a cikin ransa idanunsa na wani binta da kallon slowly kamar mai zooming ɗin ta a cikinsu. Dan can ƙasa-ƙasa yake mata kallon da ita sam ta ɗauka hankalinsa na kan wayar ne baya ganinta saboda ganin yanda yake cigaba da sarrafa wayarsa bai dakata ba. Babu alamar zai sake tanka mata har tsawon kusan mintuna huɗu data cika tai fam da haushinsa. Tsabar son ƙular da shi sai ta fashe da sabon kuka ta shiga wani murƙususun tana kiran “Wayyo cikina Ummu yunwa zata halaka miki ni, nima kasheni zaiyi kamar yanda ya kashe ku. Abbiy ka shirya tarbana gani nan a hanya inda kuke. Ni wlhy garama a kasheni da wannan azaba da akemun, wayyo wo wo wo!!”.

 

Tamkar wani gunki haka ya cigaba da zuba mata ido yana kallon ikon God, shi kam bai taɓa ganin Fitinanniyar yarinya irin yarinyar nan ba a rayuwanshi. Sam batajin magana, ga shegen tsiwa kamar wata babyn roba mai battery. Da ƙyar ya iya ɗaga ƙafa inda take ganin bata da alamar barin kunensa ya huta, yay tsaye a kanta kamar wanda aka dasa, sai wani binta yake da kallon ƙasaita. “Mike ciyon?” ya faɗa a fisge kamar ba shine ya tambayeta yanzun nan ta bashi amsa ba. Ɗan zabura tai da jinsa gab da ita dan batai zato ba, ta yunƙura da sauri zata tashi ya maidata. Sai kuma ya kai zaune gefenta har jinkinsu na gogar juna. Sake zaburar taso yi ya sake maidata yana tsatstsareta da mayun idanunsa masu kaifi. “Ni dai ya warke barshi” ta faɗa da sauri tana ƙoƙarin ture hannunsa dake jikinta. Ko gezau baiyi ba, sai ma ɗorasa da yay saman kanta ya zare towel ɗin da ya naɗa mata tun ɗazun. Dogon gashinta mai alamar lema har yanzu dake faman ƙyalli ne ya bayyana, ya ɗan tsirama gashin ido na wasu sakkani kamar mai nazari, sai kuma ya janye yayo ƙasa da su kan fuskarta. Da sauri tai ƙoƙarin kauda fuskar, sai dai ya hana hakan ta hanyar taro fuskar tata cikin tafin hannunsa ya sarƙe idanunsa cikin idanunta ta ƙarfin tsiya. Wani irin tashi tsigar jikinta ta farayi, cikin rawar lips kamar zata saki kuka ta ce, “Nifa na warke nace”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button