Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 57

Sponsored links

★Tunda suka shigo ko sau ɗaya Iffah bata iya ɗaga kai ta kalla ko ɗaya a cikinsu ba. Saɓanin su da duk suka zuba mata ido cike da jin ƙaunarta a rayukansu. Cike da nutsuwarta ta karasa garesu, maimakon kujera da duk suke zaune sai ta kai ƙasan lallausan dardumar…

“Haba Ibnati tashi ki hau sama mana”.

Jasrah tai yunƙurin dakatar da ita. Kai Iffah ta girgiza da ɗan murmushi a fuskarta, “A’a nanma ya isa”. Cike da sha’awa da jin daɗi duk suke dubanta. Ta juya ta gaishe da Malikat Haseena, da fara’a da kulawa ta amsa mata tana mai sanya mata albarka. Cikin jin daɗi ta juya gasu Malikat Bushirat ta gaidasu suma. Suma da kulawar suka amsa mata, dan duk ƙasaita da jin kan Malikat Bushirat sai ta tsinci kanta da murmushi da sauƙaƙawa akan yarinyar saboda kwarjini da tai mata. Shiru na wasu ƴan sakkani ya biyo baya, kafin Daneen Ammarah ta katse shirun ta hanyar kiran sunan Iffah.

Ta amsa mata da girmamawa sai dai bata iya ta ɗago kanta ba. Daneen Ammarah ta sake kiran sunanta da faɗin, “Kinga ɗago ki kallemu”. Da ƙyar ta iya dauriyar bin umarninta. Dan duk rashin jin Iffah tana da wani hali na girmama duk mai nuna mata ƙauna koda bai cancanta ga sauran mutane ba. “Ibnati nasan nan zuwa yanzu duk kin sammu ko?”.

“Eh Mamy”.

“Amma baki san matsayinmu ba?”.

Nanma tace “Eh Mamy”.

Kamar yanda nasan kikaji Mamma a garemu mahaifiya ce, itace ta haifi Hama (Suruki) ɗin ki, da ni dama wasu biyu da zaki sani anan gaba sai dai ɗaya ya rasu”.

“ALLAH ya gafarta masa”.

Ta faɗa cike da rauni. A tare suka amsa mata da Amin. Daneen Ammarah ta ciga da faɗin, “Wannan da kike jin ana kira Malikat Bushirat itace Hamah (Suruka) ɗinki data haifi Shahan-shan na yanzu kuma mijinki da yazo nan jiya……”

A razane Iffan ta waro idanu ƙirjinta na wani irin harbawa kamar zai wantsalo. Cikin subutar baki ta ce, “Shahan-shan! Na jiy…..” sai kuma tai shiru ta haɗiye sauran maganar saboda tuna a inda take…

“Kin sanshi ne kafin jiya?”.

Malikat Haseena dake nazartarta ta jeho mata tambayar a bazata. Da sauri Iffah da zufa ta jiƙema dukkan jiki, ta girgiza kanta. Kasancewar ta gwanar wayo tai saurin faɗin, “Mamma ina mamaki ne dai, ban zaci ganin Shahan-shan ɗin nada sauƙi kamar haka ba”.

Kusan a tare suka saki murmushi saboda hango tsantsar ƙuruciya a maganar tata. Sai dai malikat Haseena tsaf ta gama karantar Iffah waskewa tai. Amma kasancewar ta tsohuwa mai dattako sai ta dake itama ta shiga jerin ƴan murmushin.. Daneen Ammarah ta cigaba da faɗin, “Wannan ƙanwa ce ga Malikat Bushirat, Khaalah (Aunt) ga mijinki. Na baki ne a dunƙule iyamu da muke anan saboda muhimmancin abinda zakiji a yanzu”.

Kai Iffah ta jinjina mata da alamun gamsuwa. Jasrah ta cigaba daga inda Daneen Ammarah ta tsaya.

“Ibnati dalilin miki wannan dogon sharhin a kammu shine fara aikinki matsayin Zawjata-almilk a wannan masarauta. Alhamdullah tunda kinji sauƙi zaki koma sashenki kamar sauran Zawjata-almilk guda biyu, sai dai zaki samu horo daga wasu amintattunmu matsayinki na Zawjata-almilk. Mun zaɓeki ne saboda nutsuwarki da tarbiyyarki. Basai mun zaman sharhi akan abinda ya faru ba a baya kasancewar kema ƴar kasa ce kin san komai na dangane da mutuwar matan Shahan-shan da suka gabata.”

Iffah ta haɗiye kududun baƙin cikin daya tokare mata maƙoshi akan famin rasa ƴan uwanta da tai da ƙyar ta jinjina kanta.

Malikat Bushirat ta amshe da cigaba da faɗin, “Ibnati kece zaki zama mutum ta farko a rayuwa da zan nema alfarma a gareta, hakan kuma ta faru ne saboda jinki da nake a cikin raina da kallon da duk muke miki anan matsayin wani haske da insha ALLAH zai haska mana duhun da muke ciki. Muna son ki shiga jikin Saiful-malik domin binciko mana ainahin minene matsalar, saboda dukkan waɗan can matan da aka rasa daga kaisu turakarsa ne ake samun matsalar. Mun miki alƙawarin baki dukkan kariyar da bazamu bari ki cutu ba….”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button