Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 51

Sponsored links

A sashen Malikat Haseenah ma an gama shirya komai na tarbarsa, tun daga kan abincin da yake ci tare da kakar tasa har zuwa tsaftar sashen ma a yau ta kasance ta musamman duk da a kullum a tsaftace yake. An shirya kalolin abinci da ƙamshinsu tun duhun magrib ya cika ko’ina na sashen har maƙwafta ma na iya jiyowa. Abincine da Daneen Ammara ta girka sa da kanta saboda kar a cutar da shi ta hanyar girkawar, sai taimakon ƙanwar Malikat Haseenah da suke kira Yumma.

Gab da ƙofar fadar Malikat Haseena lafiyayyar motar da yake ciki ta tsaya, cikin rawar jiki ɗaya daga cikin Hadiman ya buɗe masa, sauran kuwa tuni sun zube ƙasa kan gwiyawunsu kawunansu a ƙasa domin girmamawa a garesa. Yaja fin mintuna biyu bai fito ba duk da an buɗe masa, sai da ya mula dan kansa sannan ya ziro ƙafarsa fara tas dake a cikin ƙyaƙyƙyawan blue ɗin takalmi mai tsananin taushi da ɗaukar ido da zai iya birge duk wani mai kallo, half cover irin na masu sarauta, kusan sakan biyar a tsakani sannan ya ƙara zuro ɗayar cike da ƙasaita. Tashin ƙamshin turarensa da takun sawayensa ya tabbatar ma Malikat Haseenah isowarsa. Da hannu taima dukkan amintattun hadimanta dake zagaye da ita nunin su fice. Har rige-rigen bin ƙofar da zata kaisu falon farko dazai fiddasu ta ainahin ƙofar sashen nata suke. A nutse tsohuwar ta ɗago idanunta ta sauke a ƙofar dai-dai shigowarsa. Tar-tar yake kallonta a cikin hasken ƙwan lantarkin daya haske falon kamar yanda itama take kallon ƙyakyawar fuskarsa dake a tsuke. Tai murmushi da jan numfashi ta fesar a hankali lokacin da yake isowa gabanta. Farin hannunta da fatar ta gama tattarewa saboda tsufa ya ɗan rissina ya kamo tare da kai tausasan lips ɗinsa ya sumbata.

“Amincin ALLAH da yardarsa su tabbata ga managarcin tushe mai cike da tsaftatacciyar yabanya”.

Idanunta ta lumshe a hankali da sakin murmushi a lokaci guda, sai kuma ta buɗesu tare da buɗe masa hannayenta. Rungumeta yay shima yana sakin ƙasaitaccen murmushi a karo na farko. Tsahon sakan talatin suna a haka kafin su saki juna ya dago amma bai ɗaga daga ranƙwafen ba. Hannunta ta ɗaura saman tausasashiyar sumarsa da a kallo guda zaka tabbatar da kuɗaɗen da take lashewa bazasu kasance na wasa ba.

“Aminci da yardar UBANGIJI ta kasance tare da kai kaima farar yabanya abin alfaharina”.

Idanunsa ya ɗan ƙankance da jinjina kansa yana murmushin da ita kawai ke iya ganinsa kai tsaye a fuskarsa kamar haka, sai ko Malikat Bushirat. Daga haka ya miƙe da ƙyau ya zauna ƙasan tattausar dardumar da aka shirya musu abinci, zama yay irin zaman sarakai da suka isa suka tumbatsa. Idanunsa ya zubama kakar tasa da murmushi ya gagara barin fuskarta, dan duk wannan ranar tanajinta rana ta musamman ne a gareta, sakamakon tuna mata da mijinta da ɗanta da takeyi da kuma tsananin ƙaunar jikan nata a yanzu.

ta a yanzu.

 

“Nannah Kina lafiya?”.

 

“A zahiri dai lafiya nake, amma a baɗini cike nake da kewarka da ƙishirwar son ganinka a idaniyata Hafeedi”.

 

“Uhhm!” ya faɗa da ɗan lumshe idanunsa ya buɗe a lokaci guda. “To ki koma sashena mana, in har da gaske ne kina mun irin wannan buƙatar a kusa da ke”.

Yay maganar da yanayin zolaya, sai dai fuskar a kame take babu alamar hakan tattare da shi. Itama murmushi tai batare da tace komai ba dai-dai tana miƙa masa kofin data zuba madara.

“Kwana biyu mike faruwa da kai?”.

Yaja wasu sakanni kafin ya girgiza mata kansa alamar babu komai. Idanu ta cigaba da tsura masa har hakan ya ɗan sakashi tsarguwa ya kauda kansa gefe. Itama ɗauke natan tai gefe cikin rashin bama yanda yay ɗin muhimmanci. Sun kwashe kusan mintuna uku a yanayin shiru kafin shi ya katse hakan.

Idanunsa masu girma da haske ya tsira mata. Kanta ta ɗauke gefe dan tasan kalmar (Suna zuwa) ɗin ce yake nemawa amsa.. Shima janye nasa idanun yay cike da basarwa da ƙasaitarsa ya ɗauka kofin data zuba masa madara……

 

 

 

A dai-dai nan Daneen Ammarah ta shigo da sallama hanunta riƙe dana Iffah dake cikin ƙyaƙyƙyawar doguwar rigar abaya baƙa datai matuƙar amsar jikinta, Shirine na musamman da Daneen Ammarah ta zauna domin yinsa gareta da kanta. Cikin ƙanƙanin lokaci sirrintaccen ƙamshin jikinta ya shiga rige-rigen isa hancin Malikat Haseena da mai gayya mai aiki. Shaƙar ƙamshin turaren da zaton Daneen Ammarah ce kawai mai shigowar ya sashi ɗago idanunsa, cikin Sa’a kuwa ya sauke su a kanta. Murmushi Daneen Ammarah da suka haɗa ido ta sakar masa, yayinda shi kuma fuskarsa ke nuna tsananin ƙaunar da yake mata a zahiri.

 

Haka itama Malikat Haseena murmushi ne ƙawace a fuskarta idonta akan Iffah da kanta ke rissine taƙi kallon komai. Ƙara riƙe hanun Iffah Daneen Ammarah tai da ƙyau kamar za’a ƙwace mata suka cigaba da takowa a nutse. Malikat Haseena taima Daneen Ammarah nuni ta zaunar da Iffah a kusa da ita, sai ya zam suna facing juna da Tajwar Eshaan, sannan kuma a tsakkiyar su shi da Malikat Haseena ɗin..

 

Gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ga Daneen Ammarah tamkar baiga tana tare da wata ba, “Amincin ALLAH da rahamarsa su tabbata ga Mamy na!”. Ya faɗa akan laɓɓansa kamar bashi yay maganar ba, dan ko Iffah da Malikat Haseena ba jinsa sukai ba sai ita Daneen Ammarah da takai zaune kusa da shi. itama ta sake sakin murmushi da kaɗa masa kanta. “Tare da kai Abni, Amincin ALLAH da rahama da kariyarsa su tabbata a gareka. Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya da nutsuwar zuciya?”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button