Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 3

Sponsored links

Cikin ƙarfin hali Babiy ya zabura hanyar soro domin dubawa duk da halin ciwo da yake ciki. Baya yaja da sauri saboda cin karo da suka kusayi da tawagar jama’ar Daular Ruman dake ƙoƙarin shigowa suma. Kansa ya rissinar alamar girmamawa a garesu. Hanash da Ummu ma a kusan tare suka zabura. Cike da girmamawa mai haɗe da matsanancin tsoro Babiy ya zube bisa gwuyawunsa. Hakan da su Ummu sukaga yayi ya sasu zubewar suma tare da risinar da kawunansu, jikkunansu na matuƙar tsuma dan abune da ba’a taɓa gani kojin labarin faruwarsa a tarihin ƙasar Ruman ba. Babban mutum dake jagorantar tawagar ya tsaida idanunsa akan Babiy. “Ya kai wannan talaka dake a ƙarƙashin mulkin daular ruman, munzo da babbar magana ne gareka bisa umarnin daular ruman”.

Ƙasa Babiy ya ƙarayi da kansa, tare da haɗe hannayensa waje guda. “Ina mai matuƙar farin cikin ganinku tare dani, ni mai biyayyane ga kowanne umarninku”.

Duk da maganar Babiy ta musu daɗi babu alamar hakan a fuskokinsu. Ya miƙe cikin rawar jiki zuwa ɗakin Ummu. Mintuna kaɗan ya dawo da babbar tabarma sabuwa ƙal data saya domin auren Arfa zai shimfiɗa a gabansu. Dakatar da shi Shugaban tawagar tasu yayi cikin ɗaga hannu.

“Munzo nan ne domin isar da saƙo ba zama ba ya kai wannan talaka dake a ƙarƙashin daular ruman. Umarni a gareka daga daular ruman, taga iri a gidanka kuma tana buƙata. Muna mai tayaka farin cikin zama ɗaya daga cikin surukan tarihin daular ruman”_*.

A matuƙar firgice Babiy da iyalansa duka suka ɗago cikin zabura da matasanancin rikicewa. Sai dai basu da ikon koda motsa bakunansu balle neman ƙarin bayani. Kasancewar ba amsa dama suke buƙata ba mutumin ya janye idanunsa daga Babiy ya maida kansu Arfa da suka ƙanƙame hannayen junansu.

“Wacece babba a cikinku?!”.

Kalamai huɗu masu ƙarfin razani da neman fasa zukatan mai saurare da har abada bazasu bar amsa sauti cikin zuciya da ɓargonsu ba suka fita daga bakin ɗaya daga firɗa-firɗan samudawan dake zagaye da mutumin. Babu wanda ya iya motsawa a cikinsu, dan kuwa sake dulmiya suke a cikin duhuwa…..

Saukar sautin wata zabgegiyar bulala mai adon jikin zakanya a jikinta ya sakasu zallo baki ɗaya. Babiy ya zube a ƙasa saboda azaba na raɗaɗin shigar wannan bahaguwar bulala a jikinsa, ganin basamuden mutumin dake riƙe da bulalar ya sake ɗagawa zai zuba masa Arfa ta miƙe tana mai fashewa da kuka jikinta na karkarwa tace..

“Nice!”.

Cikin daka tsawa basamuden hadimin yaba Fariha da Iffah umarnin suma su ɗago. Ɗagowa sukai jikkunansu na karkarwa ga hawayen tausayin mahaifinsu ya wanke musu fuskoki. Idanu ya zuba musu kusan na sakan goma, kafin ya janye ya maida ga shugaban tawagar tasu…. “Zancenta nakan gaskiya ALLAH ya ƙara maka lafiya”. ya faɗa cikin girmamawa ga shugaban tawagar tasu. Shugaban ya gyaɗa kansa shima idanunsa akan Arfa “Mahaifinta da ɗan uwanta zasu zama waliyyanta”.

Ya faɗa cike da cika umarni yana mai nufar hanyar fita batare da wani ƙarin bayani ba……

Har aka tafi da Hanash da Babiy babu abinda su Fariha suka fahimta, balle ma Iffah da kallon kowa kawai take. Kukan Ummu ne ya dawo da su hankalinsu, gaba ɗayansu sukai kanta. Ummu dake kuka kamar ranta zai fita ta haɗasu su duka ukun ta rungume jikinta na wani irin rawa……

Tafiyarsu da kamar awanni uku Babiy da Hanash suka dawo gida da doki ɗaya da tarin kayayyaki, sai rakuma guda uku. Fuskokinsu cike suke da firgici mai tsayawa a zukatan masu kallo. Ba abinda sukazo da shi bane a gabansu Ummu, burinsu susan mike faruwa? Kawai. Basu samu amsa ba daga garesu har bayan shuɗewar wasu awanni, kafin Babiy ya basu amsa cikin dakewa….

“Na bada aurenta ga *_Shahan-shan_*, bamu baro ba sai da aka ɗaura musu aure, wannan raƙuman da dokin sadakinta ne”. Ya ƙare maganar idonsa akan Arfa.

Tamkar saukar aradu mai tarnatsa haka furucin ya isa cikin kunnuwansu, Ummu tai baya zata faɗi Babiy ya riƙota, kansa yake girgiza mata alamar kartace komai, suma yaran ya juyo garesu yay musu nuni da shiru ya jata suka shige ɗaki. Umarnin mahaifinsu shine mafi girman biyayyarsu garesa matsayinsu na waɗanda ke rayuwa a ƙarƙashinsa, badan sun so ba suka zaɓi shiru, sai dai shirun nasu bai hanasu haɗe kai a ɗaki suyi kuka ba su ukun. Kuka irin wanda za’a kira kuka a duk idaniyar da zubar hawaye ke kwaranya na rashin lissafin ƙididdiga. Mintuna sun shuɗe, hakama awannin da suka ƙarasa kalmashe wannan yinin. Bayan sallar magrib saiga motoci da tawagar hadimai tare da wasu hamshaƙan mata huɗu wai sunzo ɗaukar Amarya Arfa. Kuka suke tamkar ransu zai fita, haka sunaji suna gani suda iyayensu aka shirya Arfa cikin shiga ta alfarma aka wuce da ita Daular Ruman

Dare ya riski zukatansu cike da damuwa, yayinda sai ɓarawo mafi iya satane ya samu nasarar sama musu nutsuwar wucin gadi wato barci. Sun wayi gari kunnuwansu a buɗe na jiran jin labarin mutuwar ƴar uwarsu, sai dai babu wani alamar hakan har sake shuɗewar kwanakin zuwan ranar bikin al’ada.

Babu fashi aka gudanar da bikin al’ada na ƙarshen kowace shekara. Sai dai su a zuri’arsu babu wanda ya leƙa koda ƙofar gida. Anyi an gama, kamar kowace shekara an samu rashin rayuka a wasanni daban-daban, da kuma haɗarin mota dana mashina suma a tituna daban-daban saboda cinkoson jama’a dalilin garin shine babban birni da Daular Ruman ke ciki. Bikin al’adar ƙasar ruman kuma yana ɗaya daga cikin biki mai tsananin ƙayatarwa da mutane daban-daban suke halarta daga sassan duniya ta ko ina. Shahan-shan ya fito zagaye tamkar kowace shekara cikin shiga ta alfarma, bashi a karan kansa ba hatta keken dokinsa ma abin kallo ne, sai dai a wannan karon ma babu wanda zaice ga kamanin Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed ɗin.

A haka lokaci ya ƙara turawar da kwanaki suka zama watanni kusan uku. Shuru na waɗannan watanni bai sama musu wata nutsuwa ba, dan a kallon farko da mai gani zaima gidansu zai san akwai matsala tattare dasu. Komai ya sauya, sauyawa irin wadda ƙaddara ta shigo cikin tarihinsu. Babu mai walwala a cikinsu, komai na ƙarfin hali sukeyi, abinci ya gagara ciyuwa yanda ya kamata a koda yaushe garesu, sai cin ƴaƴan itatuwa, tunkan a sanar musu alamominsu sun tabbatar da zaman makokinsu. A haka duhun wani dare na cika watanni uku da kwana uku da auren Arfa ya sake riskarsu, suka sake zama ƙarƙashin mulkin mallakar ɓarawo mafi iya sata koda shiri ko babu wato (barci). Daren da yazo ma Iffah da wasu irin munanan mafarkai masu firgici daban tsoron.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button