Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Chapter 17

Sponsored links

Wuce azmee tayi dakinta agajiye saboda ta samu ta huta, yayin da tabar sehrish tana faman kwashe dishes ɗin izuwa kitchen, bayan ta kammala wanke komai ta mayar dasu inda suke ta jera,

Sannan ta kama hanyar futowa daga kitchen ɗin, sam bata lura dashi ba sai dae taganshi agabanta kamar Aljani,

 

Tsorone ya kamata jikinta ya shiga kerma, dariya haroon yayi tare da cewa “Ina son ganinki baby da yaushe zamu haɗu ne,”? Ya tambaya yana kashe mata ido,

 

Murya na rawa sehrish tace ” Zuwa anjima yanzu agajiye nake, inaso na huta,”

 

Jinjina kai yayi tare da cewa “Okey, ki tabbatar kin kawomin kanki ɗakina, zan jira ki anjiman,”

 

“Insha Allah,” ta faɗi tare da bi ta gefenshi ta wuce hankali atashe, tuni hawaye sun soma zarya a kuncin ta ,

tana shiga bedroom ɗinta ta shiga yarfa hannu tana safa da marwa, damuwa iri iri daga nan sai wancan, babban tashin hankalinta a yanzu batasan da wata manufa haroon ke nemanta ba, runtse ido tayi tare da faɗin “Ya Allah ka tsare ni daga sharrin wannan bawan naka, Ya ilahi ni ynx bansan ya zanyi ba, gashi yace nakai mashi kaina ɗakinsa,” ta ƙare maganar tana mai jin bugun zuciya da fargabansa,

 

Daker ta tsagaita da zagaye zagayen da take yi a ɗakin nata,

 

gefen bed ɗinta ta hau ta ɗan kwanta eyes ɗinta na facing ceilling thinking abt many things, a haka har bacci 6arawo yayi awon gaba da ita, tasha bacci Ssae, dama ga weather ɗin is so comport,

Ba ita tafarka ba sai around ƙarfe 2 da mintuna har time ɗin sallah ya haura, tashi tayi tana dafe ƙirji domin kuwa har mafarkin haroon sai da tayi wai yace zai tona mata asiri wurin babban yayansu, da ta tabbatar da cewa mafarkine sai ta sauke ajiye zuciya tare da furta “Thank God it was a dream,”

 

Da hanzari ta shiga toilet tayi wanka ta ɗauro alwala, sannan ta fito ta nufi wardrobe tayi dressing kanta cikin riga da wando, sannan ta ɗauki hijab ta sanya, ta janyo sallaya ɗinta dake a saman murfin wardrobe ɗin dama nan take hanging ɗinta sometimes hada hijabin sallanta,

Shimfiɗawa tayi sannan ta kabbara sallah, a natse take yin ibadarta ta, bayan ta kammala sallar ta zauna saman carpet ɗin ta lankwashe ƙafarta, ta ɗaga hannayenta ta shiga jero addu’a, ta jima hada hawayenta domin tabbas tana ji aranta akwai wasu ƙalubalen da zata fuskanta acikin watan nan, tana roƙon Allah ya bata ikon cinye koma wata irin jarabawace sannan yabata damar tsallake duk wani ƙalubalen da zata fuskanta,” 😥

 

Bayan ta kammala ta miƙe tare da naɗe sallayar ta ninke ta sannan ta cire hijabin ta ninke ta itama ta tura su cikin wardrobe dukansu,

 

Hayaniya taji daga harabar gidan alamar ana buga ball daga wajen murmushi tasaki tabbas tasan su junaid ne ke wannan, wasan,

Ji tayi tana marmarin itama ta kalli wasan ball ɗin nasu wataƙil ta rage ƙuncin da take ji a zuciyarta,

 

Da azama ta ƙarasa jikin window ɗinta ta naɗe curtains ɗin sannan ta zuge glass ɗin ta tsaya tana leƙensu,

 

Su 6 ne acikin ragar filin ball ɗin dake acikin gidan , shi da wasu daga cikin soldiers ɗin dake tsaren gidan,

 

time ɗin da ta aza idonta akan junaid sai da taji zuciyar ta ta buga, sanye yake cikin kayan kallonsa riga da gajeran wando dai dai guiwarsa kana ganin waɗannan fararen ƙafafun nasa na rainon madara abun ba’ace wa komai,

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button