Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 4

Sponsored links

Har rige-rigen fitowa suke daga ɗakunan barcinsu sakamakon fitar sautin razananniyar ƙarar data karaɗe gidan mai ban tashin hankali. Su duka huɗun suka rufu a kanta kowa na ambaton sunanta da kai hannu jikinta. Duk da sanyi da akeyi jike take sharkaf da zufa ga illahirin jikin nata daya ɗauka zafi. Ummu ta rungumeta tana mai sakin hawayen da ke kwance a cikin idanunta. Ta riga ta farka dan haka itama ta ƙanƙame Ummun tana fashewa da nata kukan.

Ba yau ne karan farko da Iffah ke shiga irin wannan tsoron ba sakamakon firgici a mafarki, sai dai na kwanakin nan yafi razanarwa da saka ruɗani a zukatansu. Babiy ya kai hannu ya shafa yalwataccen gashin kanta, murya a raunane yake ambatar sunanta.. Kanta ta ɗago a hankali fuskata sharɓan da hawaye, ta dubi mahaifin nasu da Yayansu Hanash da Fariha, sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da haɗiye sauran kukan tana tashi zaune daga jikin Ummu ta share hawayen dake jiƙe da fuskarta. Matsawa tai jikin mahaifinsu tana mai kamo hanunsa.

“Babiy inajin tsoro, matuƙar tsoro a wannan mafarkin fiye dana kullum. Babiy itama Nina Arfa kashemana ita zasuyi kamar sauran matan daya aura?, itama zamu rasata na gani a mafarki na…”

Da sauri Hanash da dukkan rauninsa ya bayyana a fuskarsa ya shiga girgiza mata kansa cikin aro jarumta. “Mafarki ba gaskiya bane Iffah, ki kwantar da hankalinki Arfa na cikin ƙoshin lafiya tamkar mu insha ALLAHU…”

“Amma Akh Hanash nawa yasha zama gaskiya, a daren da Nina Arfa zata bar gidan nan irin wannan mafarkin nayi a kanta, yau ma shine na maimaita da ita babu banbanci a cikinsa na rantse maka”.

Har ƙasan zukata zancen nata ya dake su, ganin bayyanar rauni a fuskokinsu ya saka Babiy yin murmushin ƙarfin hali yana shafa kanta. “Shaiɗanu zasu iya dawo miki da makamancin sa ai Ibnati, dan haka ki kwantar da hankalinki Arfa na lafiya a gidan aurenta”.

Bazata cigaba dayin jayayya da su ba, amma tana cikin matsanancin damuwa tamkar yanda take hango tasu akan fuskokinsu. Maimakon komawarsu barci sai duk suka miƙe zuwa tsakar gida, alwala suka ɗauro, suka koma can runfar dake matsayin falon iyayensu suka fara salla da miƙa kukansu ga UBANGIJIN talikai da fatan hana tabbatuwar abinda zukatansu ke cikin tsananin fargaba. Haka suka kasance har sallar asubahi gaban mahaliccinmu, bayan idar da sallar asubahi maimakon kwanciya sai suka riski kansu a zaman jugum-jigum na jiran tsammani. Har fitowar rana babu wani yunƙuri daga ɗayansu. Sai ko ga isowar abinda suke fargabar ya riskesu ya iso garesun. Shigar bugun gidan a cikin kunnuwansu ta sakasu miƙewa a zabure gaba ɗaya kuma a lokaci ɗaya, kowanne cikin rawar jiki da fidda tsammani. Babiy ne yay jarumtar ƙarasawa ga soro cikin jan ƙafa. Tunda yay tozali da hadiman masarauta zuciyarsa tai wata irin masifar wulƙitawa…..

“Kun kasheta itama ko?!”.

Da shi da hadiman suka riski muryarta a cikin kunnensu a bazata. Sam babu tsoro ko shakka irin wadda akema duk wani mai alaƙa da masarauta a ƙasar cikin idanunta a yau. Sun soye sunyi jazur irin na tashin hankali. A harzuƙe cikin hadiman ɗaya ya daka mata tsawa da faɗin, “Hattara ɗiyar talakawa, bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane”.

“Idan yaron ya kasance rago ba!!”.

Ta bashi amsa itama a tsawace. Shimfiɗeɗiyar bulalar hanunsa ya ɗaga zai zuba mata Babiy ya kare cikin rawar jiki yana mai zubewa ƙasa a kan gwiyawunsa. Sosai a zaba ta ratsashi, ya rimtse idanu cikin aro dakiya da jarumtar dole, “A gafarceta ita ɗin yarinyace masu nasara”. Ya faɗa cikin rawar murya saboda azabar tasirin shigar bulalar.

Ƙasa Iffah takai durƙushe gaban Babiy tana mai fashewa da kuka, kafin ta ɗago ta dubesu zatayi magana Babiy yasa hannu ya rufe mata baki jikinsa na tsuma. Jikin nata itama tsumar yakeyi, sai dai ita bana tsoro bane na tsananin baƙin ciki ne da bushewar zuciya. So take ta amayar da abinda ke bakinta an hanata. Batare da hadiman sun sake bi takantaba suma suka isar da saƙon dake tafe da su.

“Kasancewarka mai biyayya da bin umarnin masarauta a karo na biyu an sake baka damar halartar jana’izar ɗiyarka kai da zuri’ar ka. Mun barka lafiya”.

Innalillahi wa-inna’ilaihirraji’un. Babiy ya shiga ambata, kusan a tare Ummu da Fariha suka saki razananniyar ƙara wadda ta jawo hankalin maƙwafta da mutanen dake tsaitsaye a ƙofar gida tun wucewar hadiman masarauta. Dan sun san dai labarin gizo bazai wuce na ƙoƙi ba……..

Dole ne zuri’ar mal. Zayyan su ambaci rasuwar Arfa da kalmar WASA FARIN GIRKI a jerin zaren ƙaddarar da ta kutso a rayuwarsu mai ɗauke da almakashin da ya datse farin cikinsu. Sun rasata tamkar labarin hikayoyin marubuta ko wasan kwaikwayo na film. Ta tafi tafiyar da bazasu sake ganita ba, tafiyar da babu wanda aka bawa damar yin cikkakkiyar sallama da ita a cikinsu hatta mahaifansu. Ta shuɗe a ƙaddararsu tamkar yanda ruwan damuna kan tafi da duk wani yayin dakan tare masa hanya a lokacin wucewa. Komai ya faru tamkar ba’aiba. Babu mai iya koda tari balle bin ba’asi. Iyakarsu kukan idanu dana zuci wanda muryarsu kan tsayane kawai iya filin gidansu ko katanga basu isa bari ta haura ba. A yau ma dai Babiy da Hanash ne sukaje domin jana’izarta. Suko aka barsu da amsar gaisuwa a cikin gida wadda mutanensu talakawa na zuwa musu itane a ɗarare…….

 

Kwanaki sun cikagaba da shuɗawa tamkar ba’ai komai ba, yayinda ɗayar matar Tajwar da aka aura masa tare da Arfa itama dai ta mutu bayan wasu watanni. Bayan su Arfa ba’a sake jin Tajwar yayi wani aure ba, sai dai mutane na raɗeraɗin a duk randa aka kaisu domin ziyartar turakarsa babu fashi gawarsuce take fitowa. Hakan yasa kowa ke danganta mutuwar matan da tsafi yakeyi dasu

.Wata huɗu da sati ɗaya cif tarihi ya sake maimaita kansa, dan kuwa Fariha ta sake faɗowa a jerin matan da aka ɗaurama Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed aure da su. Batare da wani shawara ba a safiyar alhamis suna zaune kira ya riski Babiy daga masarauta, babu wanda bai shiga tsoro da firgici ba a cikinsu, sai dai babu wanda ya isa hana hakan a duk faɗin ruman. Sunaji suna gani babiy yay shiri ya amsa kiran. Tafiyarsa da awanin da basu gaza biyar ba sai ga hadiman masarauta sunzo sunma Fariha ɗaukar amarya itama babu wani bayani daga garesu. Ranar dai kam Iffah bata gazaba kojin tsoro wajen gwada musu hauka, dan bata bari an fita da Fariha ba har sai da basamuden nan ya zabga mata bulalar dorinar hanunsa data sakata zubewa, bata tashi dawowa hayyacinta ba sai bayan wucewarsu da kusan awa guda. Zuwa lokacin har Babiy ya dawo. Kamar dai Arfa itama Fariha an ɗaura mata aure da sarkin da kowa yake masa inkiya da fir’aunan wannan ƙarnin. Sai dai a ɓoye wannan suna ke fita a bakunan talakawan gari irinsu Iffah. Sakamakon bulalar da aka zabga ma Iffah bayanta yay mugun fashewa har akan mazaunanta, ga wani raɗaɗi mai azaba na ratsata har ta kasa riƙewa sai da ta saki ƙara. Babiy da Ummu suka rufu a kanta, hawaye suke suna jeramata sannu, Hanash na gefe zaune idanunsa jajur alamar tsananin ɓacin ran da babu ƙarfin ɗaukar mataki……

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button