Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 134

Sponsored links

Mamaki hade da al’ajabi ne ya mamaye Iffah lokacin da suke fita a cikin jirgin hannunta cikin nasa. Wasu zuka-zukan motocine na alfarma da tawagar masarautar Saudiya, yayinda Sultan a Saudiyya ne da kansa yazo tarbar Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed Ally Qutb ba sako ba. Cikin farin ciki sarakunan biyu masu karfin fada aji a duniyar musulinci suka tarbi juna. Sam Tajwar Eshaan bai saki hannun Iffah ba har suka rungume juna da Sultan din. Bayan sun saki junan ne ta dan rissinar da kanta alamar girmamawa ga Sultan din.Fuskarsa kawance da murmushi yay mata kallo daya da musulunci ya shardanta ya dauke kansa. Ya fai mata barka da zuwa DAULAR MUSULUNCI cike da mutuntawa a gareta duk da yasan zai iya haihuwarta. Dan manyan yaranta maza twins guda biyu suma bazasu wuce 20years ba karnar Iffah’r..

A hankali ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe idanunta jin sanyin ac da kamshi mai shegen dadi ya ratsa hancinta lokacin da suke shiga daya daga cikin manyan motocin da sukazo tarbarsu. Dubanta Tajwar Eshaan yay tare da rungumota jikinsa da kyau. Tako late kamar yar mage tana shakar daddadan kamshinsa. Ashe Iffah ba komai ta gani a airport din nan ba. Sai da suka shiga babbar daular da lissafin dukiyar cikinta ma da kawatuwa bata lokacine. Tabbas tasan Daular ruman ta had, irin haduwar da babu wanda zai shiga bai yi santi ba. A tunaninta da anya akwai makamanciyar irin daularsu a duniya? Amma a yau ta tabbatar akwai, dan duk da daular Saudiyya bazatafi tasu ba, suma tasu bazata fita ba, dan nan clin ma dai badaga baya ba Dan in za’a baka zabima zaka ya kasa banbancewa ne tsabar shiga

an daga su sai turarrukansu sukazo kasar. An sake gaisuwa irin ta manyan attajirai masu mulki da karfin iko, sannan a nutse sukai buda baki mai sauki (ba irin na su bily ba da sai anji ciki yay nak babugurin tura kosai 🥱), Karancin lokaci ya saka sarakunan biyu mikewa zuwa gabatar da sallar isha’i. Suma kuma su Iffah suka kora bedroom din uwarg/klan Sultah suka gabatar da tasu. Suna idarwa basu zauna ba, dan tafiya tsakanin nan da Madina akwai nisan gaske, dan ma lafiyayyun motocine. Sai lokacin Iffah ta san ashe tare da Sultan din da matar tasa ma zasu wuce. Tofa wayaga in da ranka kasha kallo, dan kuwa dal acikin zukekiyar motar da zasuyi tafiyarma dai an shirya musu abincine, ga an shiryar motar daga aiki kamar wani daki ha musamman. Iffah dai da al’amarin ya zame mata sabo ga kauyanci ga son nuna class t3, haka mutunivar tamu akaita basarwa kamar komai ba komai dai kun gane ai 😉(Kuka yarda naje gurin nan alkur’an sai na nuna hali, dan kowa sai yasan Bilyn Abdull daga 9ja nazo 🤣😆🚴).

An musu tarba ta mutuntawa da tsantsar girmamawa, tare da masauki dan gaske da ko’a kasarsu iya abinda zasu iyama kansu kenan. Tattare suke da gajiya, musamman I/fah daba sabawa tai ba ga kuma azumi, saukin ma farkon farawa ne. Da kyar ya lallabata tal dan wanka ta kwanta. Kafin kace mi barci yay awan gaba da ita.

 

 

 

Bata samu kanta ba sai la’asar, shima da kyar ya tadata sanda zai wuce massalaci. Bayan ya dawo yace ta shirya zasu wuce madina ne da ansha ruwa, da ga haka ya fice ita kuma wasu mata sukazo mata da kaya inji matar sultan. Sun jirata ta shirya sukai mata jagoranci zuwa sashen matar sultan din, inda ta samu tarba ta mutuntawa da har ta dinga jin kanta ya kara girma itama a yau. Dan duk da matar sultan din ta girmeta sosai janta ta dinga yi a jikinta cike da kulawa harda cewa itafa tana so ta saki likinta da ita ne dan sun zama kawaye. Murmushi kawai Iffah tayi mai sanyi. Ta wani nutsu kamar ba Iffah’r nan mai shegen surutu ba mai addabar Tajwar Eshaan. Magana ma an koma amsata ne dai-dai cikin nutsuwa da kamewa ita a dole ga matar Shahan-shan na kasar ruman (Ashe akwai a inda bakin Iffah zai mutu haka (😂). Suna a tare har aka sha ruwa, a tare suka gabatar da sallar magrib sannan suka fito kayataccen falo karami na musamman da aka shirya musu kayan alatu na shan ruwa. Daga ita sai uwargidan Sultan da Shahan-shan din ta. Sai wani irin binta da kallon nan nasa na kasan ido yake kamar zai hadiyeta dan ta masa matukar kyau cikin kykyawar bakar abayar data haske farar fatarta ga walwalin fararen duwatsu da akai mata ado dasu. Itama dai uwargidan Sultan irin kayanne a jikinta. Haka shima da Sultan din kayansu iri gudane.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button