Hausa Novels and Stories

Hamrah Hausa Novel Page 2

Sponsored links

Sun had’u ne ta sanadin wani problem daya taso ma fareed a company d’inshi wadda yake bukatar lawyer asalin lawyer d’in mahaifinshi wadda ya zama nashi be kasa shine ya had’a shi da suhailah, anan tazo tayi iya kokarinta har suka shawo kan problem daga nan ya fara sonta be yi nauyin baki ba ya fad’a mata, dayake bata da wani wulakanci da ji da kai duk da kyaun da Allah ya mata sbd mahaifinta ta d’auko, duk da fareed d’inma ba baya ba duk kyaun mahaifiyarshi ya kwaso bata wani ja lokaci ba ta amince……

Ansha buki sossai duk da ‘yan uwan angon kad’an kawai suka zo daga chad, zaman lafiya sukeyi kowa na aikinshi, har aurensu ya shekara 7 suhailah bata ta’ba ko ‘batan wata ba, abun ya fara damunta amma se fareed ya kwantar mata da hankali da “haihuwa ai na Allah ne, in da rabon haihuwan se kiga kin haihun karki cire rai ga rahamar ubangiji”……

Kullum nasiharshi kenan a gareta, kwatsam se ga ciki, soyayyar duniyar nan gabad’aya suka d’aura akan cikin nan, ba karamin gata aka tanada ma babyn da be ma san sunayi ba, bayan wata tara ta santalo ‘yarta kyakyawa wacce tayi karo karo na kyau se tazo tafi iyayen nata da suka tsammata kyaun, anyi shagali sossai inda yarinya taci sunan mahaifiyar fareed “HAMRAH” sam ya ki a boye mata suna……..

Anan Abuja tayi daga nursary d’inta har secondary daga nan ta wuce India tayi first degree d’inta anan ta gamu da simra ‘yar india ce ba musulma bace lokacin da suka had’u ita ma ba baya ba wajen kyau haka mahaifinta ana ji da shi a india kuma yana tashen kud’i, bayan ta gama ta koma gida se simra tayi mata maganan masters da farko tace baza tayi ba se kuma ta chanza ra’ayi zama sukayi suka za’bi university da suke so…..

Oxford suka za’ba ba’a b’ata lokaci ba aka sama musu suka wuce duk department d’insu d’aya inda suke karantar business, tana dawowa nigeria ne mahaifinta ya sakar mata ragamar company d’inshi tana son mahaifinta kaman ranta, a lokacin ne kuma kawarta simra ta musulunta, sam bata samu matsala da iyayenta ba sbd sunga takai ta zabi addinin da take so…….

Nigeria tazo ta musulunta tana zaune gidansu hamrah d’in, dr. Fareed ya kawo mata babban malami tana d’aukar karatu a gurinshi sossai ta mai da hankali akan addini wani lokacin hamrah d’in ke daura ta kan hanya don hamrah ba baya ba wajen ilimin addini sossai take da ibada sede tana da dan banzan wulakanci mussaman akan samari ita har yanzu bata ga wadda ya dace da aurenta ba kowa low class ne in kuwa kayi gigin furta mata se ta tsiga maka abunda har ka mutu baza ka manta ba….

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button