Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 104

Sponsored links

Yau kam da alama shari’ar zatai zafi. Dan kotun tacika fie da zaton mai hasashe. Abinda Kuma zai birgeka duk ahalin masarautar ne.Cikin wani irin takun kasaita da izza da ya jawo hankalin duk wanda ke cikin kotun Iffah ta shigo da shi. Ga hadimai na take mata baya. Tayi matukar kyau cikin shigar jikinta, ga wani irin kyawu da fuskarta ta kara sai shining takeyi fiye da hasken tauraruwa zarah. A zahiri ita tafiyarta takeyi normal, amma ga masu kallonta babu abinda suke gani tattare da ita sai tsantsar izza mai ban mamaki. Wani abin birgewa da tai ya kayatar da was a wajen shine kai tsaye inda Malikat Haseenat take ta nufa. Takai kasa cike 17:42

yanzu bayan Tajwar Eshaan da Malikat haseenat sama da ita a duniya.

Shigowar mai gayya mai aiki tasa tunaninsa katsewa…. a take kotun tai tsitt kowa ya mike domin girmamawa. Taku yake cikin tsantsar kasaita da izza data zame masa jinin jiki. Ga wani irin kamshinsa mai kada zuciyar mai shaka na tashi. Yammatan wajen da suka dade da folawa a sonsa tuni zukatansu suka shigar narkewa, duk da babu abinda ake gani bayyane a fuskarsa. Dan ya sakayata hatta da idanunsa saye suke cikin eyeglasses dake nuna blue daga waje. Addu’ar neman tsarin ALLAH da ga duk wani abin cutarwa ya karanto lokacin da yake kaiwa zaune a hadaddiyar kujerar da ke a mallakin zamansa. Ya dan saci kallon sashin da yake tunanin ganinta. Tana a wajen kuwa, sai dai abin mamaki ita sam bama shi din take kallo ba.Ajiyar zuciya ya dan sauke a hankali wadda ko amintaccensa da ke gefensa da masu tsaro guda hudu haggu da damansa basu isa ji ba.

Bayan an tabbatar da kowa ya natsa Sayeed Hanifud-Din ya mike ya dubi jama’a.

“Alhamdullahi muna godiya ga ALLAH da ya sake dawo damu zama na uku akan wannan shari’a. A zaman daya gabata wadda ake kara ta amsa laifinta, sai dai ta Bama wannan kotu mai adalci damar bincike mai zurfi akan tushen shugaba na wanna daula. Inda wannan kotu mai adalci ta amshi korafinta har ta bada dama ga masu bincike. Matsala ta ratsa ta yunkurin son halaka Zawjata-almilk da akai, inda dalilin haka aka samu tazarar daga wanna zama har sai da ta samu lafiya. To yanzu dai alhmallh, wanna zama a wanna gabar duka zai ta’allaka ne ga jin bayani da ga bakin shugaban jami’ai da aka danka wanna bincike garesa. Shugaban jami’ai bismillah”.

Sai da ya mika gaisuwa ga Shahan-shan cike da girmamawa kafin ya juya ga jama’a. “Assalamu alaikum kamar yanda aka bamu damar bincike a gaban wannan kotu mai adalci mun gudanar. Mun bibiyi tushen samuwar madara da kaita sashen Zawjata-almilk. Inda bincikenmu kuma ya kaimu har ga wanda ya shigo da wannan madara mai dauke da dafin macizai a ciki. Karna cikaku da surutu waka bakin mai ita tafi dadi. Ina rokon alfarmar wannan kotu da ta bani damar gabatar da Dafiq in Ghalib a gabanta”.

Kallon juna Miran Arshaan da Miran Jasim sukai suka saki murmushi. Sai kuma sukai saurin duban wanda jami’ai ke kokarin shigowa dashi kirazansu na wani irin mummunan harbawa.Kokarin mikewa Miran Arshaan yay da sauri Miran Jasim ya danne masa hannu jikinsa na rawa. Iffah da ke kallonsu ta saki murmushi,cikin Sa’a kuwa suka hada do da Miran Jasim.Ido daya ta kashe masa da dauke kanta tana dan wani cizar lips cike da salo.

Dattijo da jami ‘ai suka shigo da shi bazai wuce shekaru hamsin da takwas a duniya ba. Cikin nutsuwa ya gurfana gaban Shahan-shan yay gaisuwa, bai o motsa ba da ga zaman kasaitarsa. Dattijo Dafiq in Ghalib ya gyara tsaiwarsa yana fuskantar kotu. Dubansa Sayeed Hanifud-Din yayi ya ce, “Dattijo waye kai?”.Cikin dan rawar harshe ya ce, “Dafiq ibn Ghalib. Ni masanine akan macizai. Ina zaune a kauyen Bansh”.

“Miye alakarka da daular ruman?”.  “Alakata da Daula ruman alakace irin ta kowanne dan kasa. Wato fadan shugaban kasata adali”.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button