Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 26

Sponsored links

Da kallo ya bita yana mamakin Ramewar da yarinyar tayi tome ke damunta?Ya girgiza kan shi yana mai juyawa Ya fita da Iman A hannunshi Wajan motar shi ya nufa ya Buɗe tare da aje Iman aciki ya zagaya ya buɗe Gate sannan ya koma ya fitar da Motar Sannan ya dawo ya rufe Gate Ɗin ya Koma Cikin Mota yayi mata key yaja ya bar layin.

Kai tsaye wani ƙaramin Private Clinic ya kaita wanda Nurse suka karɓi Iman domin su duba Hannun ta kamar yadda yayi Musu Bayani Rintse Idanu yayi yana jin zafin yadda Ƴar ƙaramar yarinyar Keta tsala Kuka Lokacin da Nurse ke gyara mata Hannun nata wanda tace masa Buguwa ne tayi bayan an gyara aka shafa mata magani a wajan Ya biya Kuɗi sannan ya Shiga Mota sai da ya biya ta wani super market ya sayi madara ta Jarirai ya tambayi yadda ake haɗawa tare dasu pampers dasu Pida sannan ya ƙara Saya mata Riguna masu kyau sai yayo Gida.

Lokacin daya ƙaraso Gida tuni an soma ruwa da sauri ya shigar da Motar ya Kulle Gida sannan ya fito da Iman da kayan daya siya yayi ɗakinsa da Gudu gudu, Batare daya Bi takan Amatullah ba bare ya kai mata yarinyarta so yake yaga Gudun ruwan Haukanta……..

Bayan ya shiga ɗakin ya rufo ƙofar shi ruwan zafi ya haɗa yay wanka ya Rage daga shi sai Guntun wando da singlet Itama Iman Tawul ya Jiƙa da ruwan Ɗumi ya goge mata Jikinta tas sannan ya sauya mata kaya wajan saka pampers ne yaci wahala dan har Gumi sai da ya haɗa yana gama shiryata ya Haɗa mata madara a pida da ruwan Ɗumi ya ɗaga kanta yana bata Cafkewa tai tana sha tana ajiyar Zuciya Har ƙwallar tausayin yarinyar ce ta tarar masa a idanunsa tas ta shanye Madarar dake ƙatuwar Pidar Ya kwantar da Ita saman Ƙirjinsa yana shafa kanta mai cike da suma Kafin wani Lokaci tayi gyatsa ba jimawa Bacci yay awon gaba da ita sai Fitar Numfashi mai ɗumi take.

Anan ƙasan Carpet yaja Pillow ya kwantar da kanshi Shima da yake Gajiya na Cin Jikinsa bai Minti Biyar ba bacci mai Daɗi ya kwashe Shi Batare daya yi Tunanin kaiwa Amatullah Yarinyarta ba………

The end

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button