Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 19

Sponsored links

Haka ta dawo Gida tana cigaba da mita Ita kam Amatullah batai mata magana ba tana fama da Iman wadda har hannun nata ya Kumbura sosai yayi kamar jan ruwa ( subuhanallahi )

Da Yamma ta koma gidan sabuwa suka ɗauki hanyar Jambulo dan kaita gidan aikin nata……….

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za’a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko uwargida ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.

BINTUS-SPA-ND-MORE… na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

Cikin shigar Kakin sa na sojojin Nigeria Army green yake saukowa daga step ɗin Jirgin, Idanun shi manne da ƙaton baƙin glass sai ƴar ƙaramar jakar dake hannun shi a nutse yake saukowa fuskar shi babu yabo babu fallasa kamar koda yaushe

Tattaki yake a tsakanin filin jirgin wayar shi daya Kunna yanzu ya ɗauko yana Kiran Kamal wanda tuni sun iso Domin ɗaukar shi daman jiran saukar Jirgin suke yi.

“Kamal nafa sauka kana ina ne?”

Sanin rashin haƙurin Yayan nasu ya sanya Kamal Fitowa daga cikin Mota da sauri da wayar a hannun shi yana Cewa.

“Muna wajan ai Yaya Tun ɗazu Muka iso”

Juyawa yayi batare da yay magana ba suka haɗa idanu da Kamal wanda ya tawo da sauri ya Zube a ƙasa yana gaisar da Yayan nashi kana ya amshi jakar Hannun shi suka Nufi Mota.

Gidan Gaba Kusa da driver ya buɗe ya shiga Bakin sa ɗauke da Bisimillah ya zauna yana mai zare Glass ɗin dake Manne a idanunshi.

“Yaya Barka da dawowa ya hanya?”

Muryoyin Naja da surayya da Ameerah ne suka cika Kunnen shi Cikin Mamaki yaɗan Juyo yana kallon su ta cikin madubin motar.

“Daku yazo kenan lafiya?”

Ya faɗi a taƙaice.

“Yaya wallahi Mama ce tace a zo dasu”

Cewar Kamal.

Bai kuma magana ba ya jingine kanshi da jikin seater Motar ya lumshe Idanun shi gaba ɗaya Jikinsa ciwo yake masa Tsananin gajiya ce Cike a jikin nashi.

Har Kamal yaja motar Bai kuma cewa komai ba kuma daman Tun fil azal shiba mai yawan maganar Bane ba.

Ameerah ta kafe shi da idanu ta cikin madubin Motar gaba ɗaya ya tafi da dukkan Imanin zuciyarta Tsananin son shi na kuma fisgarta Jitake kamar ta dauwama a haka tana ta kallon shi Jinta take tana yawo acikin Duniyar gajimare Wata biyar Ɗin da yayi bai zo gida ba Taga yaƙara cika da kyau Hutu ya kuma ratsa shi kamar ba soja ba.

Tana jin ko a mace ta Huɗu ce zata zo masa Indai zai aure ta bata Biyu ba.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button