Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 114

Sponsored links

Idanunsa da ke lumshe tun sanda ta daura hanunta saman fuskarsa ya bude a hankali, sunyi zajur fiye da yanda ya shigo da su a dan birkice. Hannun ya kamo yana kallonta, cikin tsananin kasala ya daura lips dinsa a tsakkiyar tafin ya sumbata. Sai da ta matse jikinta tsabar la jininta yay wata irin yamutsawa har brain. Yunkurawa tai da nufin tashi a jikinsa ya hanata hakan, sai ma fuskarta da ya kamo cikin tafukan hannunsa ya manne lips dinsu waje guda. A tare suka saki ajiyar zuciya Iffah na rumtse idanu da karfi. A tsorace take matuka,amma ta danne ta karfin tsiya domin taimaka masa ya samu nutsuwar zuciya kamar yanda Mammy ta mata nasiha akan a duk sanda taga ya shigo da fushi tai kokarin gain ta cire masa wannan fushin da damuwar ta hanyar jansa jikinta da hira da raha ko nasiha. Idan kuma ya nuna bukatar wata hidimtawarta ko ita ta fahimci akwai abinda ke sakashi shagala ko kwaranyewar damuwarsa da wuri to tazama jaruma wajen aikatawa kota bashi hadin kai. Tunanin a iya abinda yake yi din baza’ai gaba ba ya sata sakar masa jiki harta fara bashi hadin kai. Gaba daya ta sake rikita masa lissafi, dan abune da bai zaton samu da ga gareta ba anan kusa haka. Tuni idanunsa sun rufe ya juyesu a gadon ya shiga yamutsata yanda yake so cikin nutsuwarsa, dan a rayuwa komai na Tajwar Eshaan babu gaggawa a ciki, koda kuwa yana a wani yanayi ne da zai iya canjawa sai kaga a zahirance babu wanna canjin a gaggawa garesa. Dan nutsuwa da kasaita a jinin jikinsa take yawo da harbawar bugun zuciyarsa. Jin al’amarin ya fara zarce karamin tunaninta tuni ta fara son kwatar kanta. Sai dai kuma babu hanyar samun wanna damar da ga jarumin ,Shin yaya lafiyar giwa da ma. Balle kuma ita da kanta ta balle likin. Duk yanda taso tuna masa dinkin dake a tare da ita babu alamar yana ma iya jinta balle fahimta. Burinsa kawai yake kokarin cimmawa a cikin rufewar idanu..

Da karfi, karfin karfi yake buga kansa a bangon dakin kurkukun mai tsananin duhu da ta iya karamin windown kawai ake iya gain dan ziririn haske. Gaba daya zuciyarsa ta bushe, zafi

yakeji a cikinta mai tsananin tururi dake kona zuciya. Shi shi Jasim ibn Abdul-majeed Aliy Qutb ne wata karamar yar iskar yarinya yar cikin cikinsa tai sanadin kawowa cikin kurkuku. Shi Arshaan da ya koya sanin kansa a wajensa zai yima cin amana? Shi hadiminsa da ya dauka tsahon shekaru yana kyautatama zai ci Amanarsa a gaban makiyansa. Wace irin wannan, mai tsananin duhuwa da babu lissafinta a cikin duka lissafe-lissafensa. Ta yaya shi Jasim in Abdul-majeed Aliy Qutb zai yi irin wannan faduwar bakar tasan a gaban karfin ikon dan makiyansa kuma makiyinsa

Cigaba da buga kan yake da karfinsa yana ihu mai tsananin karaji da ya saka masu tsaron dakun kurkukun nasa da Tajwar Eshaan ya bada umarnin bama tsar mai tsananin tsauri tsora.Cikin karfin hali daya a cikinsu ya dan leko, ta dan hasken da ya hasko da ga karamin windown ya hango fuskar Miran Jasim da tai wani irin jage-jage da jini dan ya fasa goshinsa.A zabire yay baya yana zazzaro idanu. Yan uwansa ya sanarma, babu bata lokaci sukai kiran shugaban jami’ai suka sanar masa dai-dai da yanke jikin Miran Jasim da jini ke rinjayarsa va fadi kasa….

Rungumeta yay tsam-tsam a cikin jikinsa idanunsa a lumshe. Jin kukanta yake har tsakkiyar zuciyarsa. Dan kuka take sosai fiye dana daren shekara jiya kasancewar yau fami yay akan ciwo.

Ta fada cikin kuka. Yanda tai magana tana sake barke masa da kuka ga hawaye shabe-shabe harda su majina ya sa yaji dariya na yunkuro masa. Kamar ba yanzu ta gama iyayi a kotu ba,dan duk abinda ta dingama Miran Jasim akan idonsa ne tsaf. Amma jiba yanzu a dan abinda bai taka kara ya karya ba ta koma abin tausayi.Ya fahimci sai ya dage matukar dagewa akan dorata a irin layin da yake bukata ta hau inba hakaba ragguwa za’ai, bakinne kawai cike da zance da tsiwa. Bashi da burin sake wani auren bayan ita, dan haka dolene ta shirya karbarsa a duk sanda yazo. Murmushin da ke neman kufce masan ya hadiye da kyar da saka hannu yana goge mata fuskar data kwabe da hawaye. Cikin dadisashiyar muryarsa data kara komawa can kasan makoshi a fusge ya furta, “Am sorrybazan kara ba”

“Wlhy zaka kara, ranar ba sai da kace bazaka sake ba amma yau ka kara, ni bazan sake zama a sashen na a kasheni kwana na bai kare ba”. Ta kara barke ma sa da kukan tabara.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button