Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 105

Sponsored links

Sai a kira na biyar sannan Deen yaji wayarsa na ringing, kamar ya share kawai ya fito da wayar, ganin Dad ne yasasa daukan wayar da sauri……

Tinda ya dauka yake zazzaga masa masifa akan rashin daukan wayarsa da wuri, yana sauraransa amma bece komai ba saboda abinda yake damunsa yafi karfin masifar da Dad yake, shiko jin abinda yake cewa bayayi dan hankalinsa baya wajan……

Baki sake suke kallonsa ganin ya fasa waya haka kawai dan sudai basuji yayi wata magana me tsawo a wayar dayayi ba hasalima su mami basu gane dawa yake waya ba, eesha ce tayi kokarin zuwa ta dauke masa wayar Umm ta rukota da sauri tana fadin;

“Kar kije, ku koma ciki”….

Dan tasan tsap taje saiya iya ball da ita be saniba yanda yayi fushin nan haka…..

Hanyar gate ya nufa ze fita daga gidan, mai gadi ya taso da sauri yana tambayarsa baze fita da mota bane……

Wani wawan mari ya daukesa dashi sannan ya hankadesa ya bude gate ya fita……..

Har ya danyi nisa da gidan zuciyarsa ta shiga saka masa abu akan batan yarinyar dukda bacin dan da yake ciki, juyawa yayi ya koma ya nufi gidan, saidai ba main gate yayi ba zagayawa yayi ta gate din baya, rike kansa yayi sosai yanajin kamar ya buga kansa a bango ko zai samu salama, haka kawai zuciyarsa taki amince masa ya wuce be duba gate din baya ba, gashi kuwa alamu sun nuna tanan tabi ta fita, wato ta gane ba zaa barta ta fita ta main gate ba kenan, amma abun tambaya anan shine ya akayi ta samu key din gate din?…..

Juyawa kawai yayi ya cigaba da tafiya ko sanin insa yake jefa kafarsa bayayi……

Da sauri su Umm sukayi kan mai gadi da bakinsa yake fitar da jini ga goshinsa daya fashe shima…

A take akasa driver da wasu securities biyu sukayi rushing dinsa to the nearest hospital kafin su mami su karaso……

Bayan fitarsu Umm ta sauke ajiyar zuciya, hankali tashe ta kalli Mami tace;

“Wallahi nima na dauka ya dena, especially yanda naga yana tolerating yarinyar chan, normal him nasan tuni yayi zuciya da lamarinta koda yayi niyar taimakonta”…..

 

“Nima dai abinda nagani kenan naga ko sau daya betaba nuna mata bacin ransa ba, har ina godewa Allah ya chanja, ashe halinnasa na nan”…..

 

“Wannan halin nasa na damuna Umm, kullum addu’a ta akan Allah ya yaye masa wannan muguwar zuciya gashi yanzu ya jiwa bawan Allah ciwo, daga baya yazo yanajin ba dadi kuma”…….

“Ameen ya Allah, Insha Allah ze dena, kawai muciga da masa addu’a, yanzu meya bata masa rai? Kuma ina ya nufa?”…….

“Abinda naketa tinani kenan, ko dawa yayi waya haka?….Allah ya karesa a duk inda yake, Allah karya hadasa da wannan ze shiga sabgarsa bare ya masa illa”…….

“Ameen ya hayyu ya kayyum, ki kwantar da hankalinki yaya Insha Allah he’ll be fine”…..

“Allah yasa Jamila, muna fama da batan yarinya ga wani abu kuma, ni narasa tinanin da zanyi ma”….

“All is well Insha Allah, karki tada hankalinki, mushiga ciki musan abinyi”……..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button