Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel

Sponsored links

Ruwan sama ake yi sosai garin, yanayin yayi wani irin daɗin gaske, ga wata irin ni’imtacciyar iska wadacciyar da ta gauraye ko’ina, wurin ƙarfe 5 na marece ne amma sai kayi tunanin dare ne sosai saboda Lullumin da garin yayi, a wannan yanayin kowa na ƙumshe a bedroom ɗinsa saman gadonsa, lullu6e da bargo, baka jin hayaniyar komai ko’ina tsit a cikin gidan 😊

 

zaune suke acikin mota suna tattaunawa su biyu, Hafsat ce tare da wata Hamshaƙiyar mata wadda bansanta ba, jikinta na sanye da tsadadden leshi Ash colour, fara ce kana ganinta kasan taji hutu Over ya zauna mata, ita ce a mazaunin driver yayin da hafsat ɗin ke gefen ta suna tattauna wa,

Hafsat ta natsu tana sauraronta ” Naci sa’a da nasamu address ɗinki kuma na same ki cikin sauƙi, kuma ina fata zaki taimaka mun wurin cimma burina,’ matar ta faɗi tana kallonta,

Hafsat tace “ina sauraronki me kike so inyi miki ne “?

Murmushi matar tasaki kafin tace “Kafin na faɗa miki abunda nakeso, pls ina so ki fara bani acct number ɗinki,”

Bin ta da kallo hafsat tayi cikin mamakin jin abunda matar tace,

Amma batayi musu ba, ta shiga karanto mata numbar acct ɗin, ita kuma tana kwashe wa a wayarta dake hannunta,

Bata jima da gama karanta mata numbar ba sai ga Alert ya shigo a wayarta ƙirrrr!

Cikin sauri hafsat tasa hannu ta ɗauki ƴar purse ɗinta dake asaman Laps ɗinta ajiye, ta zugeta ta ciro wayar jiki na rawa ta duba, gabanta ne taji ya faɗi rass !! Ganin Alert na 6millions abun kamar a mafarki take ganinsa

Cikin tsananin mamaki ta ɗago ta kalli matar tare da cewa “Wannan fa? Na menene?

dariya matar tayi kafin tace ” akwai wasu tagwayen Yara da Marshal Omar ya kawo gidan nan, Sunan su Hosana da Jahad,’

Jin sunan da ta ambata yasa hafsat kallonta cikin mamaki,.

Taci gaba da cewa “Ba wani aiki bane mai wahala, so nake subar gidan nan ! Suyi nesa da Marshal Omar……….’

 

Cike da mamaki hafsat ke kallonta , babban abunda ya ɗaure mata kai shine yadda akai tasan cewa Marshal Omar ya kawo yara acikin gidan,.

Daker ta iya cewa “Saboda Me za’ae hakan?

“Saboda basu da amfani,” matar ta bata amsa a taƙaice,

Shiru hafsat tayi tana kallonta acikin zuciyarta tana Was wasi akanta,

“Wacece ke? Taya akai kikasan sunan Tagwayen tare da kuma sunan Omer?

“Ba buƙatar wannan, Kawai kiyi mun abunda nace in aikina yayi kyau nayi maki alƙwarin zan ninka miki abunda na baki har sau uku

tana shiga cikin babban falon ba kowa kai tsaye bedroom ɗinta ta wuce, cire kayan jikinta tayi shaf shaf ta canza izuwa riga da wando, ta ɗaure gashin kanta a baya, tana tsaye gaban Mirror tana tunanin maganar Matar nan data kawo mata ziyara sai ga Aunty Babba ta faɗo ɗakin tana faɗin “Hafsat wacece waccan matar da tazo wurinki yanzu”?

Juyowa hafsat tayi tana kallonta tace “Nima bansanta ba address ɗina aka mata shine tazo da buƙatarta,”

“Wace irin buƙata kenan”? Aunty babba ta tambaya tana kallonta,

Hafsat tace “Tayi mun magana akan cewa tana so in raba twins ɗincan da Omar ma’ana subar gidan nan gaba ɗaya, Suyi nesa dashi”

tsoki aunty babba taja tare da cewa “Ita kuma wacece ita isasshiya? halan Omar take so ne shiyasa ta biyo ta wurinki?.

“Bana tunanin hakan, Nafi tunanin Tasan Yaran ne shiyasa take son azubar dasu,”

“To ke kuma kin amince da buƙatarta kenan”?

Murmushi hafsar tasaki tare da cewa “eh mommy na amince da hakan, saboda anan take ta bani miliyan shida kuma tace muddin aikinta yaci ka zata ninkamin abunda tabani ynx,”

tuni aunty babba ta haɗe fuska rai a6ace tace “Amma ke shashashar ina ce? Kawai daga zuwan mata sai ki amince mata da buƙatarta? matar nan fa Omar take so shiyasa takeson a salwantar mata dasu,”

“Koma dai menene Mommy ni bazan bari kuɗin nan su wuce ni ba, saboda ina cikin buƙatarsu, daddy baya sakarmun kuɗi yadda ya dace ke kuma tanadin ki na zuwa wurin bokane kema fa bakya bani ko sisi Burinki akan hayaam da Abrah ne,” .

Matsawa Aunty babba tayi kusa da ita tana cewa “Hafsat Anya kina cikin hayyacin ki kuwa? Ni kike faɗama haka”?

“Na faɗi wani abune daba dai dai ba? ta tambaya tana kallon mommyn nata, Ido cikin Ido

Sassauta Murya Aunty babba tayi a ƙoƙarinta nata fahimtar da hafsat tace “duk wannan tanadin da nake saboda kanmu ne fa ! Ƙaruwar mu ce, in har naci nasara akan burina Hayaam tasamu RAFAYET ita kuma Abra tasamu MARSHAL OMAR mune zamu ji daɗi, don haka am commanding u ki tattara kuɗin da tabaki ki mayar mata dasu yanzun nan !!!! ta faɗi a tsawace

Dariya hafsat ta kwashe da ita hada tafa hannu bayan ta tsagaita tace “Mommy kenan !! nima fa lashe Money ce kamarki, bazan bari garabasar nan ta wuce ni ba!! Akace da arziƙi a gidan wasu ƙwara agidanku, kai agidan nakuma kwara a ɗakinku, a ɗakinku ɗin ma ya faɗo akan ka, don haka ni baxan mayar mata da kuɗinta ba!!!!!!!!!

Gaba ɗaya hankalin aunty babba ya tashi don alamu sun nuna cewa Hafsat fa kamar bata cikin hayyacin ta, cikin ruɗi tace “Hafsat anya kina cikin Hayyacinki kuwa”?

Shu’umin murmushi hafsat tasaki sannan tace “Kwarai kuwa! nice dae ƴarki Hafsat ɗiyar general ishaq, jika ga Abban sojoji”

Jinjina kai aunty babba tayi tabbas an samu matsala, domin kuwa tasan Hafsat bazata ta6a fasa abunda tayi niya ba,

Huci kawai take yi tana jinjina kanta a ƙarshe ta fuce daga ɗakin,

Duk wannan suratan da Hafsat su kayi da aunty babba a kunnan Hosana wadda ke la6e a ƙopan ɗakin, jin Takon tafiyar Aunty babba yasa ta gudu izuwa cikin store ɗin da suke,

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button