Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 20

Sponsored links

Doctor dai da Sayeed Fayzul-haq kawunansu a ƙasa mamaki na ratsa su, dan ba abinda sukai zaton gani ba kenan musamman idan akai la’akari da laifin Zawjata-almilk ɗin. Daneen Ammarah kam idanunta ta lumshe tana mai sakin murmushi da addu’a mai girma a ƙasan zuciyarta. Duk da tasan gane ainahin abinda ke cikin zuciyar wannan gwarzon nasu abune mai wahala, mutum ne miskili da ya gajesa wajen uwa da uba. Ga zurfin cikin tsiya uwa uba jinin mulki dake yawo a jikinsa. Sai dai hakan baya nufin taƙi son tabbatuwar abinda take fata ɗin….

 

“Wannan ya huce a canjashi da wani Mamy”. Ya faɗa a can ƙasan maƙoshi yana miƙewa tamkar bashi ne yay maganar ba. Da alama Daneen Ammarah ta fahimci abinda yake nufin, dan kallo ta bisa da shi mai tattare da ɗan murmushi har ya fice Sayeed Fayzul-haq da Doctor suka take masa baya.

“Muna godiya da wannan karamci”. Ta faɗa dai-dai zai fice a ɗakin.

 

A yanzun ma Sayeed ne ya amsa mata da tausasawa, yayinda shi ya fice abinsa. Daneen Ammarah ta sake sakin murmushi da zaunawa a gefen Iffah, kofin shayin ta amshe tana ƴar dariya. “Haba Ibnati, irin wannan rawar jiki haka! Ki kwantar da hankalinki insha ALLAHU babu abinda zai faru sai alkairi. Abni adalin shugaba ne mai son kwatanta adalci wa kowa koda kuma maƙiyinsa ne”.

Kalmar ƙarshe da ƙarfi ta zabiri Iffah. Sai kawai ta sake fashewa da kuka tana mai jujjuya kanta lips ɗin ta na rawa. “Mamy nayi kuskure, kuskure irin wanda bazan iya yafema kaina b…..”

“Ya isa haka”.

Daneen Ammarah ta faɗa tana mai ɗora mata yatsa akan baki alamar tai shiru. Shirun kuwa tai sai dai hawayen basu bar zuba ba, ga jikinta na ɗan tsuma har sai da ta rungume ta cike da lallashi..

Da ƙyar take shaƙar numfashi da fesarwa sakamakon warin da ƙarin harma da tsamin dake tashi a cikin kogon dutsen mai tsananin saka hautsinawar ciki. Cikin son danne aman da ke ta yunƙuro mata ta sake gyara mayafin dake jikinta ta ƙarashe zancenta da, “Ruƙuƙi mai cika aiki na yarda da dukkan al’amarin ka tunda ƙawata ta bani labarinka. Na yarda zaka iya ƙarashemin abinda uwa ta fara, na yarda zan ƙarasa samun cikar burina a gareka, ina son a kawar min da duk wanda yace zai min karan tsaye ko wanene shi a duniyar nan…..” (Wa’iyazubillah. Ya rabbi ka hanamu ɓata akan son zukatanmu😭👏)

Wata irin basamudiyar dariya Boka Ruƙuƙi ya kece da ita, hakan ya bama hamami da ɗoyin bakinsa damar sake busowa a cikin hancin ta ƙurya da takejin cikinta na hautsinawa, tun a shigowarta kogon dutsen sihirtaccen ƙamshin turarenta mai narka zuciyar mai shaƙa tuni warin kogon dutsen ɗakin boka Ruƙuƙi ya disashe sa. Amma ta jure ta danne domin samun cikar burinta ya shafe kowanne ƙalubale da zai iya shafarta.

Boka Ruƙuƙi ya gimtse fuska bayan ya gama kwasar dariyar tamkar bashi ba. Ya ƙara juya jajayen idanunsa da ke sake fidda munin fuskarsa yana mai girgiza ƙaton kansa. “Duk ƙasar ruman babu wani boka mai ƙarasa miki aikin da uwa ta fara. Ki ɓace, ki ɓace gareni butulu inba hakaba zan ruguza duk wanda tai jajircewar gina miki. Uwa uwar kowa ce mai share kukan masu kuka, butulu ki ɓace gareni, maza ki ɓace!!!!”.

 

Ba ƙaramar gigitata tsawar tayi ba, tuni ta manta da matsayinta ta fito a matuƙar kiɗime har tana gware da dutsi ALLAH dai ya taimaketa kan bai fashe ba. Tana gama fitowa ta fara kwara amai, amai matuƙa tamkar zata amaryar da ƴan hanjinta. Kasancewar daji ne ga kuma dare ya tsala daga inda amintacen hadiminta ke jiranta ya dinga jiyo kakarin amanta. So yake yazo ya taimaka mata sai dai yana matuƙar jin tsoro, jin dai ta cigaba dayi yay ƙundunbalar nufarta cikin matuƙar sassarfa hannunsa ɗauke da gorar ruwa. Ƙasa ya zube duk da duhuwar da wajen ke da shi, cikin rawar jiki yake jera mata sannu da miƙa mata gorar ruwan. Amsa tai dan tana matuƙar buƙata, ta ɓalle murfin ta shiga sheƙama fuskarta batare da ta damu da yanda yake jiƙa har jikinta da tsadaddun kayanta ba. Sai da ta kusa juyesa tas kafin ta kuskure baki da sauran ta tsillar da robar tana sakin numfashi da ɗaɗɗaya. Batare da tace da hadimin ko ci kanka ba ta nufi motar da suka zo bayan ta maida norse mask ɗin fuskarta batare data bar hadimin ya ga ainahinta ba. Da gudu ya miƙe ya rigata isa, shi ya buɗe mata murfin har sai da ta shiga sannan ya nufi mazaunin driver…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button