Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 153

Sponsored links

Da kyar da kyar aka samu kotun ta lafa, yayinda kalaman Daneen Ammarah dake kuka sukai matukar daukar hankalin kowa. Fadi take, “Wlhy Mammah shine, shine wanda suka cutar da mu a tare. Bazan taba yafe musu ba, wlhy bazan yafe musu ba, sun haddasa bakin ciki mai ciwo a zuciyata. Sun nisanta ni da shi bayan sun alakanta mu”.

Sosai hankalin Malikat Haseenat dama duk wanda ke’a kotun ya tashi, dan yanda take kuka haka Babiy make kuka sai dai shi kansa duke yake a kasa. Ummu ma dai tasan komai da ya faru, dan a lokacin bai boye mata ba. Hakama lyyani. Iffah nason tashi taje garesu amma babu dama, dan ita Zawjata-almilk komai nata nada ka’ida da son nutsuwa. Dole ta hakura ta zuba musu ido kawai musamman Babiy da Ummu da Daneen Ammarah.

Tajwar Eshaan ya nisa tare da motsa lips dinsa a hankali, “Wannan kotu na bukatar Daneen Ammarah a gabanta, da son jin fassarar kalamanta”.

Sayeed Hanifud-Din ne ya maimaita abinda Tajwar Eshaan din ya fada, dan haka Daneen Ammarah ta fito da taimakon Daneen Waheada,dan da alama abubuwan kanta ma neman sukeyi, idanunta har sun kada.

“Ko zamu iya sanin abinda kike nufi da kalamanki Daneen Ammarah. Sannan ko kinada alaka ne da wanna shari’ar?”

“Bani da alaka da wannan shari’ar face a farkon ta mai bada kariya ga Zawjata-almilk. Sai dai inada alaka shudaddiya da wannan bawan ALLAHn”. Ta nuna Babiy.

Shiru kamar batace komai ba, sai kuma ta nisa da share hawayenta. “Komai ya faru ne a cikin littafin kaddara ta. Na san duk wanda yake anan in har ya kai shekara talatin da biyar zuwa sama yason tabon da ke a jikin bangon littafin labarina da duka shafukan cikinsa. Bazan kirasa abin kaico ba, amma zan kirasa zalunci mai ciwo a gareni dama duk wanda yake cikin wannan masarautar. Faruwarsa kuma ta fara ne a bisa son zuciyar dan uwana Jasim dake a gaban shari’a a yanzu. Sun kulla min aure da wan nan bawan ALLAH bisa umarnin wata mushirika da ta shude ita da labarinta a wannan masarauta. Sai dai aure ne na kwanaki goma sha uku kacal suka saka ya sakeni. Bisa kudirar UBANGIJI kuma ya samar da haihu a tsakaninmu batare da shi ya sani ba ma, dan ban sake ganinsa ba tun wannan ranar sai a yau, sai dai ALLAH yayma yarinyar rasuwa a kwana uku da haihuwarta…

“BATA MUTU BA!!”.

Kalmomi uku masu razanarwa da ga bakin kaka. Wani irin zabura Babiy da Daneen Ammarah, da Malikat Haseenat, da Iffah, da Ummu, da Daneen Waheeda, da Malikat Bushirat, da Miran Jasim sukai a lokaci guda kuma a tare kamar wanda aka saita da camara.Su dukansu kuma suka zubama Kaka da yay maganar idanu kowanne da irin kalar luguden dakan da zuciyarsa ke masa a zahirance da badini. Cikin karfin hali Malikat Haseenat ta furta, “Taya wadda naima wanka, na shirya a cikin likafani, aka sallaceta a gaban kowa, aka gina kabari aka sakata za’ace bata mutu ba. Kai wanene? Ya akai kuma kasan hakan?”.

“ALLAH ya kara miki lafiya da tsohon rai mai albarka. Nine mutumin da ya kora waccan bokanyar mushirikar a waccan raar dai da nasan bazaki manta ba”.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button