Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 8-9

Sponsored links

Cele ta kalle shi tace dan ubanka Kai kayi Mata kishiya baka San dadin komai ba baki duk cin zuma ya gama da shi me zaka ji,Idon Maheerah ta faka suka hada Ido da Ahsan ta Masa zancen kurame Wai ya samo wata a daura Masa aure da ita tana hada yatsa biyu tana kullawa Wai aure,Kai ya girgiza da sauri wai a’a ya maida hankalinsa ga matarsa suna jira ta tafi taki tafiya ta dawo ta samu kujera ta zauna har da mikowa Maheerah bra dinta tace ungo ni karbi abarki,Takaici ya Kama Maheerah ta rasa wacce irin yarinya ta samo da ace ba cikinsu a jikinta da tuni ta sa an kamata,ko ta Mata wata muguntar ita da gidanta ta hanata sakewa rana Daya ko kwana daya ba ayi ba,haka ta ja mijinta suka shige bedroom abinsu,Lokacin Cele ta tashi ta koma daki ta kwanta duk bata Jin dadin jikinta Sam Jin jikinta take Yi ba yanda ta Saba ba.

Santana mutumin Adamawa ne amma a Sokoto suke da zama,gidansu su goma cif iyayensu Suka Haifa Mata uku maza bakwai Santana Kuma shine na takwas a gidansu sauran kusan duk yayyensa ne mutum biyu ne kannensa,suna da rufin asiri babansu dan kasuwa sannan yayyen Santana mutum uku duk suna da rufin asirinsa su ke kula da iyayensu da sauran marasa karfi duk da cewa Suma ba a wahala suke ba,Santana tunda ya taso yake kwaikwayon Mata ko ya dinga daura zanin babarsa tun suna Masa fada baya ji har ya girma daga nan da kyar ma aka samu ya Gama secondary yace Sana’a zaiyi ya Fara soya doya da kwai,daga nan ya koma wata state din ya koma har waina da miya Yana Yi ta siyarwa,ya koma cikin tasha Yana dafa shinkafa da miya da wake ga waina da miya ga su doya da kwai,tun Yana karairaya Yana canja magana a hankali ya shiga daudu komai mata amma inda Allah ya taimake shi bai taba neman maza yan Uwansa ba shi,Yan da kyankyami Wai sai yace warin maza suke,sosai cikin kawayensa Yan daudu sune suka bashi shawara cewar a kudu an fi samun kudi, sai Suka koma Kwara state,daga nan sai Ibadan,tafi tafi suna Zama sune Tasha Tasha bariki bariki har Suka goge a Iskanci Suka fada sana’ar Mata masu Neman maza suzo su zaba su darje abinsu,Santana bai gama tuba da saduda ba sai da Su Manduwa Suka rasu ya girgiza da mutuwarsu Kuma yaga tasa karara Allah ya tsallakar da shi tun daga lokacin ya saduda ya tuba ga Allah Harkar ma baya son tunawa sai dai iya shegen a baki wannan kuma kafin mutum ya dena to sai a hankali wasu ma ko matan ne har abada basa dena iya shege sabo da Sabo dole ko Yaya sai kaga bariki tayi musu yawa a wani wajen.

Mudai bikin Santana tunda Namiji ne can gidansu Muka je sokoto a gidan nan bayan murnar biki har da murnar ya shiryu Yan gida suka hada kida na gaske Suka dinga tika rawa yanzu duk da Aurenmu Munyi rawa amma bada yawa ba Kar mazajen mu su gani,Mandula data auri yaro yake juyata kasa shiga tayi tace ba ruwana ya hanani Star tace ke ni da nake matar malami ma gashi na cashe bare ke,Mandula tace in ya fara min fada Ni bana son abinda ransa zai baci,dariya ta kamamu Dan yaro karami, ango Santana da abokansa duk kusan Mata ne sai Yan Uwansa maza sai abokansa da Suka taso suna tare su biyu rak Mata sunzo bikin Santana daga gari gari duk ba na kirki wai sune abokansa can aka je aka dauro auren Jamila Jamcy da Abubakar Santana akan Sadaki dubu dari da Hamsim,Jamcy bata bari ma taga ango ba su Sabreen sune Kawayen amarya, ana gama daurin auren ango ansha babbar riga ai ganin kida da girgiza ya tako ya shigo filin rawar ana ta ihu da dariya domin Santana yafi Mata iya girgiza,ya tiki rawa ya chashe Kamar tsohon dan club ne, aure da yamma likis Suka Kai Amarya lokacin mun koma zamu karbi Amarya a gidan Ango suke iske mu mamaki ya Kama Sabreen ta radawa Jamcy tace kin Shiga uku duk kungiyar su Miracle a bikin gasu nan suna ta iyayi sunzo bamu San a gayyar wa Suka Zo ba, Star ce taga suna kuskus guda tayi tace a matsayinmu na manyan abokan Ango muna yiwa Amarya barka da zuwa,Wise tace duk inda aka je mune dai,nace Rana zafi inuwa kuna,Yar Zabil ta saki guda tace mune a wajen,Barka da zuwa Amarya cewar Mandula Muka shiga dakin,Bayan mutane sun watse sai Sabreen sai Jamcy sai Kuma mu,Su Sabreen sunyi mukus sun San basu Isa ba,Mandula tace amarya yau zata karbi Antaina sai a amsheta hannu bibiyu mune masu siyen baki,wayata na dakko a jakata na Kira Santana,yace Kun taru gani nan, Namiji daya ne ya sauke shi a mota ya juya abinsa yana masa tsiya,mu Kuwa Muka tashi muka fice a motar da na zo da ita nina sauke kowacce a gidanta na wuce gida Nima,Nawwar yayi Shirin bacci tun Yana jirana har bacci yayi gaba da shi,Ina zuwa abinci naci nayi wanka tare da Shirin bacci na kwanta a bayansa tare da hugging nasa.

Har nayi nisa a baccina Kawai sai zuciyata ta Fara tashi da sauri na tashi cikin daren na shiga toilet sai amai amai Kawai nake shekawa,Nawwar ne ya farka ya shugo toilet din da sauri yace ko dai wani abin Kika ci a gidan biki Kuma, ya rikeni na gama amai na sannan na kuskure bakina nayi flowshing Muka fito Yana min Sannu cike da kulawa, ko saman bed ban kai ba na koma toilet na fara sheka sabon Amai yace ko asibiti zamu je ne? Idona cike da kwalla nace a’a,sai da na gama har wanka ya sake min ya canja min kaya,yace me Zaki iya ci yanzu Kinga cikinki ba komai nace Data Kawai nake nema ko goba idan ba su ba bana son komai,yace a Ina Zan samo wani Data yanzu,nace kyaleni to na kwana haka na koma saman bed na kwanta,yace ni yanzu Ina Zan samu goba a Daren nan,to ga Apple kici Mana,bana sonta ni ga abinda nake so nan kawai,Kaya ya saka ya fita wajen me gadi yace Dan Allah Ina Zan samu goba ko Data yanzu,Ido me gadi ya zaro yace Sha biyu fa ta wuce Oga akwai dai Wanda na sani Yana siyar da goba sai dai muje gidansa,Nawwar ya shiga mota tare da me gadi Suka je har gidan mutumin Suka kwankwasa Masa kofa ya fito,Suka ce goba suke so idan akwai yace Amma wannan me nema me ciki ce kunyi sa’a a kwai ya shiga ya fito da ita kwali guda manya lafiyayyu Nawwar ya siya min ta dubu uku Suka dawo.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button