Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 3-4

Sponsored links

Cele ta bata rai tace wlh sai dai muyi shahada a Hanya amma ba gudu ba ja da baya iya wuya sai munje Inshaallah sai munyi kudi,Abdul yace Inshaallah ai Ina zuwa shayi Zan ta Sha muryata ta washe sai kiji yalla yalla…suna dariya Awwalu yace sai kaji Muna ciniki muna Kam Kam,2riyal laa laaa kamsa riyal,suna tafiya kowa ya zaro kayan cinsa Yana ci har suna sake kwana Suka yini Sallah ce kawai ke tsaida su a wasu kauyukan.

Wise tana girkinta a kitchen Papa ya shigo a hankali ya dade Yana kallonta Yana zuba uban murmushi,yanzu sai Fushi take yi da shi bata kulashi ta maza yayi ya rungumeta ta baya,Wise Ido ta lumshe yau sati tana gaba da mijinta an dade ba a hadu ba a hankali cikin kunne Papa ya Shiga furta Mata haba my Game changer,My play maker, Heroes in my book, uhm haba my best goal assistance Allah yaci gaba da tsare min ke,Nayi kuskure ki yafe min ki taya ni da rokon Allah ya yafe min,da me zanji da halin da nake ciki ko da fushin da kike Yi dani,I love you my wife,kalaman Papa sun sanyaya zuciyar Wise ba kadan ba sunyi tasiri a zuciyarta a hankali ta juyo a jikinsa suna facing juna tace na hakura nima me laifi ce na maka karya na shigo rayuwarka badan Allah ba karshe na fada sonka,na taba karuw….shiiiii…Papa ya furta yace bana bukatar Jin komai na San komai Kuma na gano Baku da kudin da kika Zo yaudara ta da shi daga baya na hakura na aureki a haka, bana fata naji zancen kin taba karuwanci a duniya magana ta wuce Allah ya yafe mana, Wise tace na gode lokacin da idonta ya ciko da kwalla,Yana Murmushi yace mene abin kwalla kuma,Wise a kirjin Papa ta kwanta tana nadamar karuwancin da tayi a rayuwa,yace Kinga gama Mana abincin tukun yunwa nake ji rabon da naci abinci ya tsirga min tun kafin Maman Sabreen ta ballo ruwa,Gama girkin muci sai kizo kici gaba da min Shagwabar taki,lokacin da Wise ta danji kunya kenan tun shigarta bariki har mamakin kanta tayi Wai taji kunya,Papa yana fita ta kirani na daga lokacin Ina gyarawa Nawwar kayansa na sawa tace Miracle albishirinki nace goro tace yau naji kunya abin mamaki papan Sabreen yayi magana wai naji kunya,Dariya ta bani nace to congratulations,ta kashe wayar ta Kira Star dake jikin Malam a kwance suna murza juna taji Malam Abulkhair yana wani nishi,Star tace karatu yake Dora min ke Zan kira…ta kashe wayar,Wise ta bi Wayar da kallo tace shegu bari na Kira Seraline Saliha ce ita ta Kira Sera bugu Daya ta daga tana cewa Hero plate din fa daka wanke bai fita ba haka ake wanke wanken,Sabeer Yana dariya yace kin sani Shiga kitchen ni ba aikina ba,ni fa eating you shine aikinaSeraline tana dariya tace Allah ya shiryeka,Wise wayarta ta kashe tace to bari na Kama dattijona nima na hutawa kaina da Yan Iska,Iyamami an warke ras ashe an dawo da ita gida,ita bata rabo da zaga bangaren yaranta sai kace yar iska tana ji da Yamma part din Wise uban kida na tashi a speaker amma ta wani dangala kafa ta tafi wajen Wai zataje wajen danta Yusufa zasuyi magana.

Tana shiga ta iske Papa a zaune yana cin abinci Wise sai uwar rawa take tika Kamar ba gobe ta juyawa Papa mazaunai Yana kala Yana washe baki yana nishadi,Iyamami ta Shiga ko sallamarta ba a ji sai da Papa ya lura ransa ya baci wai ita Kawai sai dai ta shigowa mutum Palo ba knocking,kidan ya kashe Wise bata lura da Iyamami ba ma ta koma ta zauna a cinyar papa,sai da yace Iyamami fa,ba tare da ta tashi a cinyarsa ba ta juya ta kalleta ita kanta Wise tana Jin haushin abinda tsohuwar take mata,kin tashi tayi ta kwanta a jikin Papa sannan tace Ina yini Iyamami,tsohuwar Hannu ta shiga tafawa tace ke mayyar maza dama ance cikakkiyar karuwa ce gashi Kuwa idona Yana ta gani,yanzu idan ba tambadewa ba Kamar Papa babban mutum Wanda ya haifeki ki zauna kina uban murguza Masa tuwon duwawu a gabansa kina karkada su wato harda tura Masa ya gani ke ga tabbatacciya, yanzu idan a Zamanin mu ne yaushe za ayiwa Yusufa wannan iskancin ai sai kunya da kunya amma Kai Yusufa laifinka ne Kaine ka bata Fuska ta rainaka wannan raini ne,da yarka kamar Sabreen ko kunya baka ji,Kuma ta ganni na shigo tayi zamanta ma a cinyarka daram wato na gani da kyau Kuma a haka ta gaisheni ba rusunawa ba komai wato na haifar Mata yaro a banza ko Kai Kuma sai wani gyada Kai kake yi Kamar na jinjirin jaki.

Wise tace Iyamami kiyi hakuri mu ai zamaninmu daban da naku Kuma Banga shigowarki ba irin waje na Yara ai ba a shiga da ka haka sakaka idan da tsirara muke fa ai Kinga bai Dace kiga inda danki yake Shige da fice ba ko ni bazan ji Dadi ba ki kallar min Antainarsa ba sabo da kin Gama kallon rabonki lokacin da Kika haife shi har ya balaga yanzu hurumina ce ni kadai ya kamata na gani,Iyamami salati ta saki kamar me Aljanu tace karya kike karuwa baki Isa ki mallake min Dana ba Kuma sai an sakeki,Papa yace Dan Allah Iyamami ki ja girmanki bazan ji dadi ana fada Miki magana ba ba tsari Kuma ke Kika jawo,Kuka Iyamami ta saki tace shike nan ku kashe ni ku huta wayyo jama’a kuzo mace tafi uwa wayyo Allah laaaaaaa mace tafi uwa Yusufa ka nemi Albarka,nayi tur da Allah wadai da wannan auren.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button