Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 1-2

Sponsored links

Lokacin da Suka tsaya a mota an wuce gamborin gala dake Maiduguri anyi nisa an nutsa ana ta wuce kauyuka masu hatsari, Rufaida ce ta Fara dirgowa daga cikin mota wacce da ganin Kalar motar tayoyin kadai kasan suna bin Sahara gata Samanta a bude yake Kamar akori kura amma katuwa ce motar idan ana ruwa sai dai a lulluba musu tempol,ga Rana ana kwalawa,tace Kaka dirgo kaima Kar zafi ya kashe min kai mu dai ko Makkah ko kafar katako,Makkah ko a buhun kunama sai munje Inshaallah ba gudu ba ja da baya,mutanen motar ne Suka firfito Dan guzirinsu na ruwa da na ci suka Fara Dan gurgura,Kaka yana gefe Rana ta ishi tsoho yace Jikalle dakko mana ruwan muma mu jika makoshinmu,baki Rufaida ta zumburo tace tun yanzu sai ka shanye mana guzurin ba a san ranar tashin motar nan ba fa,Wani matashi Wanda bai da aiki sai kallon Rufaida Kamar maye yace ke da Allah ki bawa bawan Allah ruwa ya Sha ke wacce irin azzaluma ce ne,Cele tace kaci darajar a hanya muke cikin Niyyar shiga Makkah nake bazan ce komai ba,Ido matashin ya zaro yace yau naji fitsararriya rashin kunya Zaki min,Kaka ne yace in Banda shishiginka Ina ruwanka da ita,matashin yace haka ma zaka ce na barku ta kasheka yace naji dan ubanka jikata ce fa matsiyacin yaro.

Ana haka Kawai mota ta tashi Rufaida ta kwarara ihun murna tayi tsalle tare da fadawa motar tace Kaka Miko hannunka,tsoho ya taka da kyar tana taimaka Masa ya shiga shima Suka zauna sannan ta dakko ruwa ta bawa Kaka ya Sha sosai ta mayar Bayan ta Sha itama,Chin chin da Tayo da meet pie na guzuri suna tafiya ita da Kaka suna ci tana kallon mutane dai in ka cika kallonta ma Sai tai maka gwalo Wai su kayan dadi suke ci,suna gama ci ta ebo dabino Suka ci sabo dabino Yana rike cikin matafiyi ko yaya kaci sinadarinsa Yana rike mutum na wani dogon lokaci,suna tafiya sai da dare yayi sosai Suka karasa wani kauyen suna murna za a huta amma Agent din ciki wacce tana gaban mota da wasu maza biyu Suma suna gaban mota Suka ce ba a tsayawa a wannan kauyen hatsari ne da shi kuyi Addua ma mu wuce lafiya,Rufaida aka jawo carbi ana hailala da istingifari tana cewa Allah ka tsallakar damu Allah Makkah ko a buhun barkono ne ka kaimu

Suna tafiya a garin suka iske gawarwakin mutane birjik a gefen Hanya an karkashe su gasu nan,Cele ta tsorata da ganin gawar mutane birjik bata taba gani ba,suka ci gaba da tafiya har dare yayi sannan Suka zo wani kauyen da shi kuma ana yawan ruwa ba a tsayawa a wajen ruwa sai ya shanye motar gaba Daya su kansu mutanen wajen a saman dutse suke Kan tsauni,ana sauri za a bar wajen ruwa ya kece me karfi gashi ba batun ma a rufa musu tempol Dole sakkowa sukayi da yawansu sosai sabo da shake suke dam a cikin motar wasu sun iya daukan guzirinsu wasu basu iya dauka ba,ga wata Mata harda danta karami a baya dan wata uku,Agent dince ta karbar Mata yaro sannan ta sakko daga motar Suka hau gudu suna gudun tsira,Kakan Cele ya Fadi ya tashi Cele ta daukar musu guzirinsu ta Goya jakar a baya,suna gudu Kaka ya sake faduwa ta dawo ta dagashi ta taimaka Masa Suka ci gaba da gudu Allah yasa Cele Riga da wando ta saka amma rigar iya gwiwa, sai da Suka Yi tafiya me uban Nisa sannan Suka samu saman tsaunin da zasu fake,sai lokacin aka tuna da wata tsohuwa tukuf,aka dinga tambaya Ina Baba Ina Baba, Cele tace ai kuwa an barta a mota,sai da ruwa ya tsagaita Agent da driver da maza Uku Suka koma wajen motar tasu wadda ruwa ya shanyeta gaba daya,Baba suka hango Allah yasa iya kanta ne ruwan bai shanye ba,Suka Yi dabara aka dakkota.

Suna dawowa inda su Cele suke aka hau jinyar Baba Kamar zata mutu ana so ruwa ya tsotse na Hanya su samu su iya fitar da motarsu daga cikin tabo,sai da Suka kwana biyu a saman tsaunin duk sun fita a hayayycinsu ga ruwa ga sanyi sai da suka samu ruwan ya dauke sannan mazan suka dinga canja kaya dama jakan kayansu duk ta Leda ce wacce ruwa bazai Shiga ba,Sauran matan Suka dan fake daga Bayan tsauni Suka canja Kaya Suka shanya kayan jikinsu,Cele tana zagawa zata canja Kaya maza wasu samari suka dinga leka ta,tana daga Riga Suka yi Ido hudu da wani matashi Mustapha nan take tace uwarka ka kalla Mustapha shege me idon ungulu Mustapha ya koma inda yake da sauri,Agent ta hau zaginsu tana dura musu ashar sannan Cele ta samu ta canja wasu riga da wando t-shirt fara da jean blue duk a gwanjo ta siyo abinta sabo da tunanin tafiya irin wannan sai da Riga da wando,cikin Yan matan wata Wasila tace kin huta wallahi Rufaida da nasan haka tafiyar take Nima duk kana nan Kaya zan kwaso,Cele tace ai ni Nan da Kika ganni akwai maths Ina da tunani da lissafi kayansu duk ya Fara bushewa sabo da rana ta kallen, a ranar Kuma Baba tsohuwa da ake jinyarta Allah ya karbi rayuwarta suna sauri sai mutanen yankin Suka samu a ciki akwai musulmai sosai Suka Basu Gawar Baba suyi Mata sutura su binne ta,suka koma motar tasu kafin ta tashi sai da Suka yini tun safe suke abu Daya sai kusan dare sannan ta iya tashi,bayan ma ta tashi fitar da ita daga tabon sai da Suka hadu aka turata sosai sannan Suka tafi,Cele sai ihun murna take Makka ko da kafar katako ne,tace Alherin Allah ya Kai Miki Saudiyya wuuuuuu tayi tsalle ta dane bayan mota ta kamo Kaka Wanda yaji wuya cewa yake mu koma gida nidai na fasa zuwa Jikalle

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button