Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 133

Sponsored links

 

…. Suna barin sashen cikin tashin hankali tashige ciki tai kiranye uwa. Cikin kankanin lokaci kuwa sai gata ta bayyana alamar dama a kusa take. Ido rufe Malikat Bushirat ta zayyanema uwa duk abinda ya faru

 

tsakaninta da Iffah. Yanda uwa ke huci sai ya koma tsorata Malikat Bushirat din, tuni nata fushin da harzukar suka bace. Zabura tai gefe jin sautin kakkausar muryar uwa mai tsananin amo acikin

kunnenta.

 

 

 

“Wannan fadan ba naki bane damu takeyi!!! Lallai damu takeyi. Ita wacece? Yar wacece? Mitake takama da shi?! Zan tabbatar da ba uwarta kawai ba, hatta dukkan ahalinta sai sunyi nadama da dana sanin kasancewarta jininsu!!!!. Wanda suka fitama sunja bata kai musu ba balle ita haihuwar jiya-jiya.”.

 

 

 

Ta fada cikin wani irin karaji da dukan kasa da tafin hanunta, tare da rantsuwa da wani kasurgumin gunkin da take bautawa wanda sam Malikat Bushirat ita bama ta fahimta ba. Ji Malikat Bushirat din tai hatta dakin girgizawa yake, tamkar tashin guguwa uwa ta bace bat a dakin. Wani irin numfashi ta sauke mai nauyi, tare da zama jagwaf. Ta jima numfashinta na kai komo kafin ta samu daidatonsa, sai kuma ta saki murmushi mai matukar kayatarwa da dan tabe baki ta dage kamafada irin ko’a jikinta din nan,wanna kuma fadan yimata shi za’ai.

Kasancewar ba’ a ga wata a jyan ba basu wuce ba. Hakan sai ya saka Iffah yini a sashen Malikat Haseenat. Sai bayan sallar la’asar ta dawo. Lokacin su Tajwar Eshaan da was manyan masarautar na’a can saman ginin da agogon da duk ta inda ka bullo ta birnin Dahab City din zaka gansa da na’urorin ganin wata, Cikin amincewar UBANGIJI kuwa sai gashi an gansa, Dan danan kafofin yada labarai suka fara sanarwa da yawn Shahan-shan, dan shi da kansa yake duban wata tun hawansa mulki babu wani wakili.

Alhamdullah washe gari an wayi gar da azumin watan Ramadan a bakunan mutane. Yayinda jirgin Tajwar Eshaan da Iffah sai hadimai hudu mata shida maza. A ciki akwai hadiman sashen Malikat Haseenat da Iffah ta roka ta bata su su biyu har da hadima Banou. Lokacin da akace mata zatabi Iffah rikicewa tai harda kukanta a boye. Sal Diwa amintacciyar hadimar Malikat Bushirat ta zahri, wadda itama dai Iffah!r ce ta nema ta bata a gaban Tajwar Eshaar babu yanda ta ya ta bata, sai hiyu da suka kasance daya a cikinsu hadimar da Uwa tace zasu batane samun wanna damar yasa suka cusata a ciki.Tafiyace ta sirri dan haka babu wanda yasan da ita a Kasar, ko’a cikin masarautar a ba kowa ya san da Shahan-shan din za’ai ba. Kowa ya dauka Iffah’r ce kawai zatai gaba kafin su Malikat Haseenat da ake hasashen kila sue su samesu acan tunda suma sukanje duk kusan bayan shekara uku, tun bayan hawan Tajwar Eshaan din kuma sau daya sukaje,shiko tunda ya hau mulkin ma bai taba ma zuwa ba sai yanzu.

Lokacin da jirgi ke barin kasa wani irin kudindinewa Iffah tai a jikinsa na toro. Ta bashi dariya dan ya fahimci duk irin abubuwan nan tsoronsu takeji. Ga Elevator ma in zata shiga yanda take kasancewa balle kuma anan, tafa gwammace tabi stairs duk wahalarsa idan ita kadai ce. Rungure kayarsa yay dan su kadai ne, hadiman na nasu sashe daban. Koda jirgin ya gama dai-daita bata bar jikin nasa ba: sai ma barci da yay awan gaba da ita mai nauyi. Ajiyar zuciya ya saki yana mai sumbatar idanunta. Azuciyarsa ya ce, (Fitinanniyar yarinya nima nadan huta da surutunki) a zahiri kam sai ya gyara mata kwanciya nutsuwa na sake saukar masa. Shi kadai yasan kaunar da yakema yarinyar nan, ALLAH dai yasa karta zama ajalinsa.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button