Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 68

Sponsored links

Wani irin yarfar da ita Malikat Bushirat da jikinta ke rawa yayi, dan wani irin guguwar bala’i ta hango a cikin idanun Iffah masu matuƙar gigitarwa tamkar ba ainahin idanun yarinyar ba. Akan jikinsa Iffah ta faɗa, dan yarfar da ita da Malikat Bushirat tayi dai-dai da mikewarsa dama, sai dai kalaman Ammien sa da shaƙar da tai mata kawai suka shiga kunensa da idanunsa, baiji komai na da ga abinda Iffah ta faɗa ba ita. Hankalinsa ne yay bala’in tashi da ganin jinin da ke fita a hancin Iffah, yay saurin tarota jikinsa ganin jiri na neman zubar da ita. Sake harzuƙowa Malikat Bushirat tayi. “Please Ammie, Please! Please” ya faɗa da wata irin raunananniyar murya mai sage duk wani kuzarin mutum.

 

 

Idanunta da suka gama juyewa gaba ɗaya ta watsa masa, tana mai nuna shi da ɗan yatsa a kausashe. “Na baka nanda awa ashirin da huɗu in bakabi umarnina ba zakasha mamaki Eshaan”. Fuuuu ta nufi Alevator batare da jiran amsarsa ba ta shige….

 

 

 

Hankalin Tajwar Eshaan gaba ɗaya sai ya rabu biyu. Furucin Amminen sa ga kuma jinin da ke zuba da ga hancin Iffah. Tsabar yanda ya rikice sai ya shiga laluben waya. Hannunsa Iffah da ke ƙoƙarin ganin jinin ya tsagaita ta riƙe dan ba yau ta fara haɓo ba. Kanta ta shiga girgiza masa tana magana da ƙyar dan ta shaƙu a wuyantan nan. “Karka kira kowa Sultan Please. Haɓo ne kawai ka samun ruwa a kaina in munyi sa’a zai tsaya”.

 

Kansa ya jinjina mata kawai, dan duk da ruɗanin da yake a ciki babu abinda ya canja a nutsuwarsa da ƙasaitar nan. Wanda ma zai iya ganinsa a haka sai ya iya ɗauka ai baima wani damu ba. Ɗagata yay cak cikin hannayensa yana tafiya cikin takun nan nasa step by step babu wani gargada ko garaje a ciki. Ɗakin da suka fito ya koma da ita. Kai tsaye cikin haɗaɗɗen toilet ɗin ɗakin ya kaita, faɗa masa duk yanda Ummu ke mata idan tana haɓo tayi, cikin sa’a kuwa sai gashi ya tsaya. Sai dai ba ita ba hatta shima kayansa jinin duk ya ɗan taɓa, nashi ma sai yafi bayyana kasancewarsu masu haske. Dole ya cire rigar dan jini na ɗaya daga cikin abinda bai son gani, yanzu hakan ma tsigar jikinsa sai tashi take yi, dakewarsa ce kawai ta ɓoye hakan a zahiri. Gama cire rigar dai-dai da ɗagowar Iffah da ke son ce masa thanks you. Cikin sauri ta maida idanunta ƙasa ƙirjinta na wani irin harbawa, dan babu komai a cikin rigar, da ya ciren sai ya zam da ga shi sai dogon wandon pyjamas ɗin kawai ya rage. Koda wasa bata taɓa sanin mutumin nan haka yake a murɗe ba kamar wani ɗan wasan danbe ba, ita fa duk tsiwar nan tata haka kawai duk wani mai irin suffar nan tsoronsa ma takeji, shiyyasa bata kallon wristiling koda wasan wasa.

 

Shiko da tun sanda ta maida kai ta duƙar ya fahimci inda ta dosa hanyar fita ya nufa, sai da ya je gab da ƙofa a maganar nan tasa kamar ta dole ƙasa-ƙasa ya furta “kiyi wanka” ya ƙarasa ficewa. Ta jima zaune maganar kiyi wankan na juya mata a rai, tana da buƙatar wankan, amma tana jin kunyar yinsa saboda sanin bata da kaya a nan. To amma tunda shine ya ce tayi tasan maybe ya ɗauka mata kamar wancan ranakun. Da wannan tunanin ta gamsu da yin wankan. Sai da kuma ta kammala ta duba babu bathrobe duk sai towels a bathroom ɗin. Kamar zatai kuka ganin duk basu da wani girma, da ga ƙarshe ta samu ɗan babba da ya kai mata gwiwa da ƙyar.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button