Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 45

Sponsored links

“Cewa yayi bata da tarbiyya bayan a gidanmu ta tashi, tin tana karama kuma aka min alkawarin aure da ita sai yanzu yace kuma bazan aureta ba? Wallahi bazan yarda ba”……

Murmushi Abby yayi yace;

“Yaro yaro ne, ka kwantar da hankalinka babu wanda yace bazaka aureta ba”……

Cikin farin ciki khaleel yace;

“Yauwa nagode abby”……

Shiru ne ya biyo baya kowa da abinda yake tinani, shi abby a matsayinsa na babba yasan dole akwai abinda yasa mahaifinsa ya hanashi auren yarinyar musamman yanda ya bashi labari iyayensa ne suka mata tarbiyya, shi kuma khaleel tinani yake ko ya roki abby ya zama waliyyinsu da akace su kawo tinda shi babba ne sai anfi saurin yadda dashi akan sameer…….

“Abby ko zaka iyamin wani alfarma dan Allah?”…

Ya tambaya a darare……

“Ina jinka da’na, in befi karfina ba meze hana in maka?”…..

“Insha Allah befi karfinkaba Abby”….

“Toh Allah yasa, ina jinka”….

Wani gauran ajiyar zuciya khaleel ya sauke sannan yace;

“Dan Allah ka taimaka ka zama waliyyin mu a samu a daura auren mana aure yau”….

Murmushi me kayatarwa Abby yayi yace;

“Au dama itace alfarmar da kakeso ka keta kame kame? Toh karka damu ka dauka andaura aurennan, bama iya ni ba zamuje duka da mutanena”…..

Khaleel besan sanda ya rungumesa ba yace;

“Dan Allah dagaske Abby? Kai amma naji dadi wallahi”….

Daidai lokacin kuma wayar sameer tashigo mishi, sharewa yayi ganin da number Nigeria ya kirasa means har lokacin be tawo ba auren da zaa daura anjima kadan, yaga kawai gwara ya kyaleshi tinda ya samu wanda ya fishi, sai yayi blocking numbersa kawai for the mean time…..

A nitse cikin tausasawa Abby ya sake fadin;

“Amma kuma haka zaa daura auren tana kwance ba lafiya? Son meyasa bazaka bari in taji sauki ba? Kaga sai ayi abinnan cikin farin ciki da kwanciyar hankali”………

Shiru khaleel yayi yana jimamin abin aransa, tabbas maganar Abby gskyne amma zeso a daura ko tana kwancen ne saidai kuma baze iya yiwa Abby musu ba…… Cikin sanyin murya da mutuwar jiki yace;

“Toh Abby Allah ya bata lafiya”….,

Murmushin jindadi Abby yayi ganin khaleel ya fahimce shi ya dafa kafadarsa yace;

“Karka damu my son, zata samu lafiya very soon Insha Allah kuma ina tare daku, sannan shawarar da zan baka ka barta a asibiti taji sauki sosai akan kuna zuwa kuna dawowa”………

“Hakane Abby, Insha Allah haka zaayi, nagode sosai”…..

Nan suka cigaba da hirar duniya…………

Cikin dare jirgin su Deen ya sauka a Dubai, ba bata lokaci ya tari cab ya kaishi gidansa da daddy ya siya masa lokacin da yazo wani course 5 years back, yana zuwa ya tarar da gidan a gyare kamar yanda ya bari dan kullum sai anzo an gyare gidan ga kuma mai gadi da komai, shiga cikin gidan yayi ya nufi bedroom dinsa direct, wanka yayi sannan yayi sallah yasha coffee, shi gabadaya ya manta wani abu waishi abinci dan rabonsa da cin abinci tin ranar data bata, haka yake fama da tea da coffee, shida kowa ya san shi da cin abinci sosai sai gashi ko shaawar abinci bayayi akan yarinyar da batasan me ke mata yawo a ka ba…..

Tracker dinshi ya fito dashi ya gwada tracking wayar offline saidai kash an kashe abinda ze bawa tracker din access to wayar, abinda kuma be sani ba shine Umm ce ta kashe ko kuma ita fatima zainab dince?…

Inko fatima zainab ce lallai she’s too smart, sai kawai ya yanke shawarar nemansu da kansa har ya gansu tinda an tabbatar masa suna dubai…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button