Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 36-37

Sponsored links

Ahsan har yayi nisa ya juyo da baya Kamar yayi mantuwa ya dawo gida Kawai ji yayi jikinsa na bashi da matsala komawa yayi ko parking bai dai daita ba ya Shiga duba dakuna gaba Daya babu cele babu alamarta, sai da ya duba ko Ina hankalinsa ya tashi matuka ya fito da sauri har jallabiyarsa tana tadiye shi ya kusa faduwa.

motarsa farar da ya dawo da ita ya shiga ya bar gidan yabi hanya kamar yasan Cele Makkah ta nufa yasan nan ne dandazon baki musamman bakake,gudu yake shararawa Kamar zai tashi sama,Lokacin Driver Wanda ya dakko Cele ya tsaya karbar Sako har Ahsan ya wuce motar su bai san su bane .

Yana ta karewa ko wacce mota kallo motar da ya wuce wacce Cele ke ciki sai yaga Kamar itace ta mirror,Slow yayi ya danna reverse tare da dawowa baya yazo saitin motar yaga Cele tana share hawaye a cikin mota, parking yayi kawai bata sani ba sai ji tayi an bude motar tana juyowa taga Ahsan,mamaki ya kamata Hannu yasa Kawai ya jawota da kayanta,driver ya dawo Yana tambaya lafiya cikin harshen larabci,Ahsan yace matata ce fada mukayi zata gudu,Driver yace yayi kyau tafi da ita ku sasanta.

Cele ta fara tirje tirje sai an saketa ita gida zata koma,hannunta ta fisge ta karfi ta tafi da gudu zata tsallaka titi mota ta riga ta shararo da gudu Kawai ta banke Cele ta zube kasa bata ko motsi,Ahsan yayo kanta da gudu cikin tashin hankali.

Kafin kace me Yan Sanda sun cika wajen da wasu tsirarin mutane,driver din kuma tuni yayi nisa ma ya bar wajen,Ahsan ya tabbata wannan driver din yana sani tunda ko titin cele bata hau ba ya shararo da uban gudu ya gangaro gefen kwalta ya make Cele,Kuma a lokacin yaga motar tayi parking gaban ta su Cele da nisa shine ya taho da uban gudu.

Bangaren driver din Maheerah yayiwa waya Yana dariya yace ai ya kadeta sun ma huta wahalar kasheta da makami ya banke ta da mota ko shurawa bata yi,Maheerah dake Office dinta murna ta kamata tace Alhmdllh

Jini ta kasan Cele yana malala,bakinta jini hanci jini,nan take Ahsan ya sureta yana kuka Ambulance tazo sai asibiti suna cikin Ambulance ana bata agajin gaggawa

Suna karasawa asibiti gado aka basu likitoci Suka dukufa akan Cele wacce bata San inda take ba,Ahsan ya rasa inda zai sa Kansa hawaye ke sintiri a kumatunsa,sun dauki lokaci me tsawo kafin likita ya fito ya Kira Ahsan,Office yaje gabansa na faduwa,Likitan ya kalle shi sosai sannan yace da larabci ina baka hakuri yaron cikinta ya zube,wani farin ciki Ahsan yaji sabo da shi dai wannan zaluncin da aka yiwa Cele ya dame shi ya hanashi sukuni a rayuwarsa,likita yace sai dai ta samu rudewar kwakwalwa,shi rudewar kwakwalwa ba Yana nufin loosing memory bane Kawai ta rude na zuwa wani takaitaccen lokaci Wanda zata rasa a inda take,zata rasa me take yi a Ina take duk ta rude ta shiga faganniya,zata dinga Watarana dai dai watarana Kuma zata Yi abu irin na mahaukata,Ahsan yace to rauni fa? Yace bata ji Rauni ba sai dan kujewa da tayi da zarar ta dan murmure za a sallame ku,Ahsan yaji ba dadi sosai rudewar kwakwalwa ai masifa ce.

Auta Kuwa Omaira ta rakashi gidan su Sagir har dakin Sagir na samari ,ita Omaira duk duniya Sagir take so a rayuwarta shi kuma iyayensa sun ce a’a yaro ne bai Isa aure ba kwata kwata nawa yake baida aikin yi ma,shima Yana son Omaira amma Iyaye basa so sabo da sunce gidan su Omaira basu da tarbiyya masifaffu ne a fili kuma Suka ce dansu karatu yake yaro ne suka hanashi kulata,Sagir yayi aboki ya tarbi Nawaf Hannu biyu biyu.

Washe gari da safe 10am kanwar Sagir Zara ta kawo musu breakfast tea,kwai soyayye da Kuma faten wake,Nawaf tunda yayi Sallar Asuba ya koma bacci abinsa,sai da Sagir ya tashe shi sannan ya shiga toilet yayi wanka da brush ya fito ya shirya cikin Jallabiya arsh wacce ya siyo sabuwa dama kala uku ya siyo shima da boxers.

Suna cikin karyawa suna hira sai ga kanwar Sagir ta dawo Zarah nutsatsiya wankan tarwada,Auta a ransa yace idan sun hanani Sahar sai nazo nan a bani Zarah.

Suna karyawa sai ga Rahma itama da kayan karinta daga gidansu ta kawowa Auta.

Ni Kuwa Ina zaune abina Ina Jin su Omaira da Umma suna ta zuba hira Ni ban Saba da su ba suma basu saba da ni ba tunda nazo zancen Cele Kawai suke Yi da sauran yan uwa ni ba a shaku dani ba Nima ban shaku da su ba,idan Umma taga nayi shuru ne sai tace lafiya dai ko? Murmushi nakeyi nace lafiya,suna labarin Yan Uwa ban San kowa ba ni Kam na matsu Auta ma ya shigo muyi hira yafi min,Umma ce tayi magana tace ki tashi kiyi wanka a rakaki gidajen yan uwa nace to,Allah sarki Uwa me dadi abinda nake so take dafa min da kanta, Omaira aka sa ta zuba min ruwa naje nayi wanka na shirya.

A kofar gida na tsinci Nawaf shi da Abba suna hira,Nawaf Yana ta tsarinsa yana tsara Abba yace, Abba I got yah, I got yah, Wai baza ace you ba sai Yah shi ga bature, yana magana da salo but ka fahimta Abba in this life kowa yaci gaba an waye da ne ake ganin Mata Basu da daraja lokacin Jahiliyya amma yanzu Ilimi ya wadata malamai suna ta wa’azi akan darajar mata shi yasa ake so kullum mutum ya kasance Yana saurar wa’azi,Abba yace duk Ina ji na sani Kawai ni ne bana so,kana adawa da fadar Allah kenan,shi yasa akace mace idan da Aurenta to karta bari ta samu ciki ta zubar maybe wani hamshakin me kudin ko na gari ne a cikin ta watsar ta bar lalatattu Wanda zasu sa ma zuciyarka ta buga,Abba yace to itace ai kullum mace mace Dan nan baza ta sirka min da Namiji ko Daya ba sai da na Kara auren Mata biyu amma ko haihuwar basuyi ba bare na samu namiji.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button