Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 46

Sponsored links

Sai da ta Gama komai ta fito daure da towel,ta tako gabansa ta zauna a jikinsa tana zumburo baki tace Wai ta kasa goge kanta,a gefen bed din ya zaunar da ita ya goge Mata gashinta tas,ya dakko Mata Riga cikin kayan Maheerah sabo da an bar nata a mota,lotion ya bata sannan ya shiga wanka abinsa,ya dade kafin ya fito, Yana Fitowa shiryawa yayi ya makara a Sallah ya tada Sallah da sauri ta bishi sallah amma sai ta Shiga gabansa ta tsaya kyaleta yayi Suka Yi Sallah a haka Suka idar tana kwaikwayonsa tana zaune, sai Maheerah ta fado mata kuka ta saki tana shesheka,Ahsan Jin tana kuka yasan kamar ta dawo hankalinta ita tunanita ma cikin nan Yana nan tunda Sanda mota ta maketa bata hayyacinta,Hajiya Hauwa tace a Nemo mata,sai yanzu ma ya tuna da Hajiya Hauwa ya kirata Kuwa ya fada Mata Cele tayi hatsari cikinta ma ya zube,Hajiya Hauwa sai Murna take ya bata labari da larabci tace gata nan zuwa.

Minti baifi Rabin awa ba tazo tace Cele,Cele ta fashe da kuka tace ni dai cikin nan ya dameni bana Jin dadin jikina,Hajiya Hauwa tace Allah sarki ai ya zube Sanda mota ta bigeki,yanda Ahsan ya bata labari,Cele ta washe baki tace Maheerah shegiya gantalallen Sperm dinki ya tarwatse Allah ya kiyaye na hada jini dake na haifo Dan jininki Watarana ya kashe ni har lahira Yar iska me hakora kamar munjagara a hargitse,ta juyo ta kalli Ahsan tace ki fada Masa yaje ya saki Maheerah Matukar Yana so na kulashi sai ya saketa, ashe rudewar kwakwalwar bata saki Cele ba tana nan a rudenta,Hajiya Hauwa ta fadawa Ahsan,tsokanar Cele yayi yace ai matata ce Ina sonta ta ya Zan saketa,Rufeshi tayi da duka tana kuka tace sai na bar gidan nan wlh Makkah Zan koma na nemi kudina,ya zaci Wasa take shi Kuma tsokanarta yayi,Hajiya Hauwa dai ta Dan dade kafin daga bisani ta tafi gida.

Cikin dare Ahsan Yana bacci Cele ta sake fecewa tace wallahi tunda bazai saki Maheerah ba na rantse da Allah tafiya zanyi Makkah naje na nemi kudina wannan ya Gama Zama lusari tayi tafiyarta ta Shiga taxi sai Makkah a daren nan dake su komai dare ba wahalar mota.

Sai washe gari da safe ta sauka a garin Makkah ba Wanda ta sani gaga a rude babu lafiyar kwakwalwa,Kawai cewa tayi Shari mansir inda taji ance bakake nan suke zama ta biya driver kudi ta fara dan zaga layikan unguwar.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button