Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Chapter 16

Sponsored links

junaid yace “ae gaskiya na faɗa Abba, kallon ka kawai nake yi kai ta shan ƙamshi kamar baka son momynmu alhalin ko rannan kana bacci cikin mafarki naji kana cewa bana ji bana gani ni makaho ne agame da sonki Momyn junaid in bake ba sai rijiya in na rasa ki zan rungumi transformer akanki zan iya tunkararrrr

 

◻ bai idasa ba saboda jin saukar pillow din da abban nasu ya wurgo mashi, tabbas junaid ya bawa abban nasu dariya sosai

 

◻ “Kai ko? Yaushe akai hakan junaid Ƙaraya kke mun,” ya faɗi yana kara janyo Wani pillow ya wurga masa, hannu junaid yasanya ya ca6e pillow ɗin da Abban nasu ya wurgo masa a ƙinjinsa ya rungumesa yana faɗin “thank u Abbana dole na gode maka domin gashi da hannunka ka miƙo mun juliet ɗita,” ya faɗi hakan yana shafa filon dake ƙirjinsa yayin da yake kallon fuskarshi cikin madubin gabansa,

 

◻ Jin shiru Abban nasu bai sake cewa komai ba, yasanya junaid juyowa da kallonsa, samun sa yayi zaune tsakiyar gadon kansa na kallon ƙasa Allamar da damuwa a fuskarshi

tasowa junaid yayi jiki asanyayye ya haye saman gadon in da abban nasu yake yace “Abbana meya faru naga kashiga wani yanayi na damuwa,

ɗagowa Abban yayi ya kallesa cikin sanyin murya yace “Junaid momynku ! kasan bana 6oye maka komai kaine abokin sirrina, babu wanda ke fahimtar zuciyata kamar kai,” ya dakata da maganar yana dan jinjina kai,

 

◻ “Dad pls tell me may be i ave the solution of it,”

 

◻ “Junaid mom ɗinku ta azabtar dani da soyayyarta, junaid ita tace tana so na tun kafin na fara sonta, amma kalli ynx ta kama hanya da aure na akanta ta koma australlia da zama, junaid ya zanyi?

 

◻ gyara zama junaid yayi suna fuskantar juna kamar zaiyi maganar arziki sai cewa “Abba dole sai ita? Ga zankaɗa zankaɗan mata nan ƴan goma shatakwas ƴan shila kyawawan gaske masu neman sugar daddy irinka wlh abba har rububinka zasu yi ka share ta kawai ka auri wata,” in serious matter junaid yake magana

Takaici ya hana abban magana a tunaninsa junaid zai bashi shawara akan yadda zasuyi mom ɗinsu ta dawo wurinsu da zama, amma sai ga akasin hakan, in banda sangartaccen irin junaid waye zaiso ayiwa uwarsa kishiya”

 

◻ “Abba u didnt say anything, shawarata batayi bane,?.

 

◻ “Eh junaid batayi ba, ashe baka da hankali in rasa wa zanyiwa kishiya sae momynku, bakasan halinta bane, duk da bamu tare da ita amma tayimun gargaɗin cewa muddin na ƙara aure sai ta dasa Bomb acikin gidan kowa ma ya rasa,”

 

◻ Fashewa da dariya junaid yayi, abban nasu yaci gaba da cewa “kuma in banda abunka wani magidanci ne mai ƴa’ƴa irinsu Sgr da Marshal Omar zai kara aure, auren ma ƴar shekara sha takwas ae wlh a ranar da ta sa ƙafarta acikin

Fashewa da dariya junaid yayi, abban nasu yaci gaba da cewa “kuma in banda abunka wani magidanci ne mai ƴa’ƴa irinsu Sgr da Marshal Omar zai kara aure, auren ma ƴar shekara sha takwas ae wlh a ranar da ta sa ƙafarta acikin gidan nan aranar zasu balla ta gutsi gutsi

 

◻ Dariya kawai junaid yake kwasa wato ta ko’ina ba sauƙi, ita mommy tace zata dasa bomb su kuma su Babban yaya in an kawo ta gidan 6arar gyaɗa zasu yi mata,.

 

◻ “Enough junaid dariyar ta isa haka, zan baka lokaci daga yau zuwa gobe kayi tunanin shawarar da zaka bani akan yadda zamu shawo kan momynku ta dawo nan da zama,”

◻ “Kana nufin muyi mata wayau abba,”?

ɗan zaro ido abban yayi tare da cewa “kai ! wannan matar mai ɗan banzan wayau kamar dila tab ae banta6a ganin dakakkiyar mata ba irin momynku ae wannan ba wanda ya isa ya yayi mata wayau,

 

◻ Dariya su kayi gaba ɗayansu sun jima suna fira kafin su kwanta tare Abban yayi musu addu’a yabi ya shafe su duka,

 

◻ _____________________________________________

 

◻ ƙaramar yarinya ce wadda bazata gaza shekara 12 ba ke tafama gudun saman titi sai faman kuka takeyi tana ambaton sunan “Oumma !! Oumma !!! ba tare da ta lura ba wata ƙatuwar motar ƙirar range rover tayi awon gaba da ita, nan take kanta ya fashe jini ya soma kwaranyo wa ta ko’ina

A firgice sehrish ta farka daga mummunan mafarkin da take yi murya na rawa ta furta “Innalallahi wa’ina ilaihirraji’un,” ta faɗi tana cusa hannunta cikin sumar kanta idonta sunyi jawur hawaye na bulbulowa daga cikinsu, tabbas ta tsorata da mafarkin da tayi,

 

◻ Jiki a mace ta tashi ta wuce toilet saboda lokacin sallama yayi, sai da ta watsa ruwa sannan ta ɗaura alwala ta fito tana ta faman sauke ajiyar zuciya,

 

◻ Wardrobe ta buɗe ta dauko hijab ɗinta ta shimfiɗa sallaya ta kabbara sallah, bayan ta kammala ta zauna saman sallayar ta ɗaga hannayenta tana addu’o’i

Bayan ta kammala komawa tayi ta kwanta saman bed batare da ta cire hijab ɗin ba, haƙiƙa mafarkin ɗazu da tayi ya tuna mata wani abu mummuna daya ta6a faruwa makamancinsa,

 

◻ Ta jima hawaye na gangarowa daga eyes ɗinta kafin wani baccin ya sake ɗauke ta, ba ita ta farka ba har sae wurin ƙarfe tara, jiki na rawa ta shirya kamar kullum ta wuce kitchen,

 

◻ tsayawa tayi tana zazzare ido ganin har azmee ta kammala breakfast ɗin, wanda zata je ta jera a dining kawai take shiryawa,

 

◻ “Ina kwana aunty azmee,” tayi maganar tana ƴa kame kame, murmushi azmee tayi tare da cewa “Lafiya lou reesh, fatan kin tashi lpy,”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button