Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 41-42

Sponsored links

Lokacin Dana Gama abincina wanka nayi na canja zuwa Abaya arsh color me kyau,Sabreen na samu a Palo tana kallo da fara’a nace uwar gida ga abinci a dining na gama, ai Kamar sabon kamu haka ta mike tana nuna da yatsa ta furta babu ni ba ke Allah ya Isa idan Kika sake min magana na tsaneki,abincinki din banza to Dan uwarki bazan ci ba,tsayawa nayi Ina kallonta har wani fisge fisge takeyi da kanta tana girgiza kanta sabo da cocaine ta motsa, banyi magana ba Kawai na wuce dining na zuba abinci na na Fara ci hankali kwance sai ga Nawwar ya shigo, Sabreen mikewa tayi ana cewa oyoyo ta rungume shi sai yaga abin wani banbarakwai Kawai sai kallonta yake Yi da mamaki,ko kallonsu banyi ba harda zaunar da shi a kujera tana Masa Sannu da zuwa,baki ya tabe ya mike tsaye,hannunsa ta rike tare da furta Hubby ka tsaya ko indomie ce na dafa maka,kallonta yake kawai ko kunya bata ji yace yaushe Kika Fara bani abinci? da duk zaman me kike baki min girkin ba ya wuce abinsa dining tana kallo ya zauna a dining tare da ce min serve me,na zuba Masa lafiyayyen girki sannan na zuba Masa lemon da na hada Ina cewa Sannu da zuwa,yawwa ya amsa kin shirya yanzu zamu tafi Ina gamawa,to na furta,wani wawan Tsaki Muka ji Sabreen ta ja ta haura sama abinta,tana shiga daki biscuits da lemo taci ta koshi ta Fara shaye shayenta ta kwanta sai bacci,shi kuwa Yana gamawa na dakko kayana muna tafi.

Mama tana komawa gida bangaren Iyamami ta shiga da kuka,Iyamami ta tambaya lafiya? Nawwar ne yau ya Kare min tanadi ya zageni yau ba zagin da ban Sha ba akan karuwarsa Kuma tana gidan har yanzu Babu alamun zata tafi,Iyamami Nan take ta Kira Baffa yana gida yazo wanjenta tace to danka dai ya nuna Mana bamu Isa ba ya zazzagi surukarsa sannan karuwa dai yace Zama daram tana nan,Baffa ransa ya baci wayarsa ya daga tare da Kiran Nawwar lokacin mun dakko Baba kulu Muna Kan hanyar zuwa Estate din ya dauki wayarsa Baffa fada ya balbale shi da shi yace kasan Allah idan baka maida karuwar nan inda ka dakko ta ba sai kaga abinda Zan maka,Nawwar yace kayi hakuri amma bata gidan ta tafi ma tsaki Baffan ya ja tare da kashe waya.

Mu Kuwa hadadden Estate din muka shiga har gidan, gidajene masu kyau flat duk irin daya sun Kai dubu a bakin gidan yayi parking Fitowa nayi da sauri na zaga tare da bude Masa kofa Ina murmushi,Fitowa yayi fuskar nan a daure,Baba kulu na budewa itama nace Babata fito,Baba Kulu tayi Murmushi tana kallona da kaunar yanda nake girmamata tun ganin farko yanda na gaisheta ya tafi da imanin Baba kulu sai kace Wanda ta Haifa a cikinta ta zaci wata ta kirki ce ni.

 

 

 

Gidan ya bude muka shiga bai ma shigar da motarsa cikin gidan ba,gidane yayi kyau sosai nace wow furniture din yayi kyau,Baba Kulu sai ki dauki daki daya na dauki daya shike nan,yace sai gobe za a kawo muku kayan abinci,Baba kulu ta furta yau ma ni cikina a koshe yake yace mashaallah,yanzu sai ku gyara gidan Abinda kuke bukata sai ki turamin text,nace Banda waya ka manta ,Oops bari na kawo miki wayar nace kafin ka fita sa min number Seraline a wayarka na kirata yanzu zasu kawo Mana kayan,Ido ya zaro yace dare fa yayi,hmm ai mu ba ruwanmu da dare Kuma darenmu shine ranar mu,f yace sai kace Aljanu fada min number, na karanta Masa ya shiga tare da Danna kiran bugu daya ta daga tace hello waye, Wayar ya Mika min nayi magana nace Selarine miracle ce,an sake tabaki ne ko Yaya?na lissafa Mata abinda nake harda turarukan kamshi sabo da a layinmu duk akwai ana siyarwa,tace to bari na siyo amma kin San za a kashe dan kudi musamman turarukan kamshin dakin nace no wahala ki siyo sai ki fada nawa Kika kashe Zan Miki transfer,angama yanzu zamu zo dasu pretty, address din gidan na tura mata sannan na Mika Masa wayarsa,ya karba sannan ya fice,kafin ya dawo Seraline, Star da pretty sun siyo komai sun kawo ,Seraline tace gaskiya kina Jin Dadi shegiya,wani fari nayi da Ido sai ga Nawwar ya dawo kamshinsa ne yasa Muka juya Muna kallonsa mikewa nayi na karasa gabansa Kamar zan shige jikinsa nace ga saurayina na nuna shi nace wannan da kuke gani na Correct man,dan Albarka kenan,Allah zai masa Albarka,abinda yake min Allah ne Kawai zai biya shi,Seraline tace da shewa Yesssss…..Muka kyalkyale da dariya na sake juyawa Muna facing juna nace Seraline Saurayina me kudi ne akwai kudi,hannunsa na riko nace kalli agogon nan na diamond ne ki fada min wanne Namiji kuka gani Yana sa diamond sai saurayina ga kyau ga Naira ga addini ga kirki ga kyauta ai nasan ma Sai yaga daidai a rayuwarsa na karasa a sanyaye,shide kallona Kawai yakeyi yanda muke nishadi da kawayena sabo da yanda su Seraline suke amsa min da cewa ai Allah zai masa albarka,

Star tace irinsu Allah ke so,nayi girgiza da kafadata nace wace duk garin nan da saurayi irin nawa,Murmushi Kawai yayi ya Mika min karamar Wayar a kwali da layina ya juya zai fita yace ki tabbatar Kun kulle gida kafin ku kwanta nace Ohhhh kaji caring ahhh kana fasa min kai you be better person, barin gidan yayi Muka ci gaba da gyaran gidan tare da su Star babu kida ma rawa muke yi Muna aiki dama gidan baiyi dirty ba sai da Muka Gama,Mun hana Baba Kulu aiki munce ta zauna ta huta abinta sai kallon abin mamaki take yi tace a ranta kamar karuwai ne fa,a ranta ta bawa kanta amsa da cewa tabbas sune Amma ba ruwana ni Kam bari na Kama bakina.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button