Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 56

Sponsored links

Dariya abun ya bata, tai murmushi idonta a kan wayar da yake miƙo matan. Kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa a zuciyarta tana faɗin (Miskilanci ma ai cuta ce gaskiya), a zahiri kam sai ta ɗan taɓe baki tana rubuta, “Miyasa randa na haɗu da kai a Eira garden ban ganku tare ba?, bayan kuma shi ya kirani ne dan na haɗu da Ajmaal?” ta mika masa wayar. Rubutun kawai ya tsirama ido harta fara ƙosawa, dan bashi da alamar zai bata amsa. Sai da ya gama shan ƙamshinsa sannan ya amsa a rubucen shima. “Dama banyi niyyar mu haɗun ba, dan ina son na fara sanin waye ke”.

 

Sosai ta waro idanu tana kallonsa lokacin da ta gama karantawa. Bama ta san bakinta ya suɓuce wajen faɗin, “Saboda mi to?”. Shiru yay kawai ya tsira mata idanu, sai kuma ya ɗago a hankali ya zare wayar daga cikin hanunta.

 

“Saboda yamun bayanin manufarki da kai tsaye ni ta shafa batare da shima ya san hakan ba” ta karanta. Sake kallonsa tai mamaki na bayyana a fuskarta. Nan ɗin ma bakinta ne ya suɓuce wajen faɗin, “Anya mutumin nan bada saka hanunka aka kawoni gidan nan ba?”.

Wani irin lumshe idanu yay cike da salo ya sake buɗewa a kanta, sai kuma ya saki wani makirin murmushi yana kauda kansa.

“Ka amsa min Please”.

Ta faɗa tana matsowa karshen kujeran da ya maida zaman nasu gab har ƙafanta na gogan nashi. Nan ma babu alamar zai tanka matan tsahon wasu sakkani, kafin ya fiskanceta da kyau kaifafan idanunsa a kanta. “Idan na matso da makashina kusa da ni sai ya zama laifi?”.

 

Zumbur ta miƙa tafukan hannayenta duk biyu akan fuskarta ta furta, “Ya arrahaman ka kasheni, wlhy ka gama dani. Na shiga uku ni Fhareedah wace irin MAKAUNIYAR ƘADDARA ce kuma wannan ɗin?”. Yanda take kaikawo da sambatun jikinta na rawa kaɗan ya rage ya kwashe da dariya. Amma ya danne da ƙyar, sai dai duk da haka sai da ya kauda kansa gefe yana murmushi. A mamakinsa sai yaji kawai ta fita a wajen da ɗan gudu-gudu. Sosai ya zaro idanunsa, sai kuma kawai ya saki murmushi mai faɗin da har haƙoransa na bayyana a bazata. Murmushin yake shi kaɗai yana faman kare baki idanunsa akan hanyar da tabi..

A yanda hadiman leƙen asirin nata suka shigo yasa ta bama duk sauran hadiman dake zagaye da ita umarnin barinta. Jikkunansu har rawa suke suka fice, a yanda ta zuba musu ido yasa bama su tsaya wani jan jeni ba suka shiga sanar mata komai dan sun san bata buƙatar jan zance da tsaho.

 

“ALLAH ya ƙara miki lafiya mai amfani uwargida shugabar matan wannan daula. A yau Malikat Bushirat ta baƙunci Uwar masu gida. A yanzu haka ma suna a garden ɗin ta tare har da Daneen…”

 

Wani irin kallo take watsa musu da kai tsaye suka fahimci manufarta. Sake gurfana sukai a gabanta cike da girmamawa. “Kamar yanda ki ka fi buƙata mun kasance da su a wajen muma, duk da kaɗan ya rage Daneen ta ganemu”.

 

Fuska ta yatsine alamar ba wannan take son ji ba. Fahimtar hakan ya sakasu cigaba da faɗin, “Sun tattauna abubuwa da yawa, sai dai gaba ɗaya a dunƙule sun ta’allaƙa ne a neman afuwar Uwar masu gida da Malikat tayi. Ta faɗi maganganu masu yawa itama na nuna fushi, sai dai da ga karshe ta sakko harta yafe mata abubuwan da suka farun da dorawa da bata shawara game da al’amarin Zawjata-almilk. Da ga ƙarshen zancen sun kuma dai ya ƙare akan son ƙarin auren Shugaban wannan daula….”

 

A karan farko Malikat Ashwaq ta miƙe zaune sosai tana kallonsu. “Sai me ya faru?”. Ta faɗa kamar idanun nata zasu faɗo a kansu.

 

“Babu alamar dai Uwar masu gida ta bada goyon baya, daga hakanne kuma Daneen ta fahimci motsin mu a wajen iyakar abinda muka ji kenan”.

 

Hannu kawai ta ɗaga musu alamar suje. Suna ficewa itama ta miƙe, da ƴar sassarfa ta bar falon hutawar tata zuwa ɗakin barcinta mafi zama sirri gareta har kafafunta na neman harɗewa….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button