Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 8

Sponsored links

“To inane Band’akin?”. Tayi maganar a shagwa6e.

Murmusawa Doc. Fatima tayi sannan tace “muje na nuna miki abubuwanda zakiyi using dasu”

Tare suka shiga toilet.

Ta bata Brush wanda zata wanke bakinta, ta nuna Mata yanda zatayi using da shower idan tana bu’katar tayi wanka da shi, idan kuma seat-B zatayi duk ta nuna mata, kafin nan ta fito, already ta fitar da kayanda Ayush zata sanya.

Falo ta nufa daga nan ta wuce side din Junaid Wanda tin lokacin da Ayush ta sume masa daga nan ya dafe goshin sa, kan sa ne yad’au zafi sai masifar ciwon da yake yiDaman duk lokacin da zai dawo hayyacinsa sai kayinsa da goshinsa sunyi ciwo kafin.

Alluran da Mom d’insa tayi masa da’ace ya juma da yin baccin zai iya tashi cikin hankalisa ba tare da ciwon Kai ba, domin kwakwkwalwarsa ce ta samu Hutu a wannan lokacin,

Ba haka kawai ya tashi daga baccin nan ba

Kwata-kwata bai dad’e da Fara baccin ba ya soma jin qamshin jini mai dad’in gaske da kuma ratsa zuciya,

A cikin baccin yake bud’a hanci yana shan-shane shan-shane, lokaci guda kuwa ya mi’ke daga baccin yana tafe a hankali yana bin wannan qamshin jinin nan kamar Karen da yake bin mushe.,

Yana sau’ka a up stairs jikinsa ba ‘kwari ga dafin alluran da Doc. Fatima tayi mishi ga kuma qamshin jinin da ya ‘Kara kashe masa jiki,

Ido kuwa like tiger still bai washe ba.

A haka har ya iso daf da Ayush yana bibiyar jinin jikinta, ita kuwa flowers sun d’auke Mata hankali…………..

Tana sumewa a gurin kuwa nan take ya dawo hayyacinsa, ya dawo asalin JUNAID d’insa,

Yana dafe da goshinsa yake bin ko Ina da kallo, kamar komai na gidan ya dawo masa sabo, bai Lura da Ayush dake kwance a ‘kasi ba sai daya juya zai bar gurin sannan kyawawan idanunsa suka sau’ka akanta dai dain lokacin Sucuirity sun shigo falon jin ihun da sukaji itama sai ga Doctor Fatima ta nufo waran da gudu tana fad’in “lafiya kuwa mai yake faruwa a gidan”

Junaid binsu yake da kallo d’aya bayan d’aya still ya maida kallonsa kan Ayush tare da fad’in “Mom! Who’s dis girl?? Yayi tambaya tare da Kai idonsa kan Mom d’insa.

Security kuwa komawa sukayi tinda komai normal Tiger ya dawo Mutum.

Cikin ‘kik’kina Mom take fad’in “am daman marainiya ce, inaso ta zauna damu a gidan nan….

Bata ‘karisa maganar ba taji ya katseta da cewa

“Enough, enough Mom! you known bana son kasancewa cikin mutane, bana son hayaniya, bana son ko wani ‘kazamin mutum ki kawo shi gidan nan….

“Junaidddd!” Mom ce ta Kira sunansa cikin jaaa alamar dakatar da shi,

“Meyasa kake haka ne? Wannan Yarinya bafa house worker bace balle kayi tunanin haka, inason maye gurbin mahaifiyar ta data rasa ne”

Kama qugunsa yayi tare da jan dogon numfashi “koma meye ne, I don’t want her to stay wit us, ki San yanda zakiyi da ita ni dai tabar gidan nan kawai, inaso zanyi bacci”. Ya karasa maganar yana tafiya ya haura upstairs.

Cikin mamaki Mom ta Kira sunan sa “Junaid kana bani umarni ne? Shin Kai ka haifeni ko ni na haifeka?”

Juyowa Junaid yayi yana kallon Mom d’insa daga nesa “Ba Umarni nake baki ba, idan kinason taimaka mata ki tabbatar kin nesanta ta daga gareni saboda karai lafiyarta”.

Yana kai karshe ya kule room d’insa.

Mom girgiza kai kawai tayi domin ba yau ta saba jin haka daga gare shi ba,

Junaid asalin miskilin mutum ne marar son mutane, idan yace baya son abu to kuwa bazai ta6a son abun ba, ga tsirin tsira baya son raini, Mom tasha kawo house worker cikin gidan Junaid yana koransu,

Hakan yasa Ayyukan gidan suke yiwa mom yawa, Gashi tana zuwa hospital ta rasa yanda zatayi,

Junaid baya cin abincin kowa inba ta Mom d’insa ba…

Haka Doc. Fatima ta cicci6i Ayush zuwa d’akinta………….

Junaid yana a bakin gado da wata er glass table a gaban sa yanata pressing d’in computer yaji ana knocking

“yes coming” ya furta hakan ba tare da ya d’ago kansa ba.

Turo kofar akayi ta shugo ciki tare da mayar da kofar ta rufe ,

“my Son! anata business kenam sarkin danna computer fatan dai kayi sallar Isha’i?”

Tayi maganar a daidain lokacin da ta zauna a kusa da shi.

“Let me finish dis work be4”. Ya furta hakan yana cigaba da Danna computer!

Mom ce ta juya tana masa kallon ‘kurilla cike da mamaki tace “you finish what?? Junaid are you serious? A tunani na Sallah shine gaba da komai”

“Oh god! Mom nayi sauran sallolin only isha’i ne banyi ba, shi kuwa lokacinsa baya wuce wa da wuri, kinsan dai bana wasa da ibada na KO”

 

Jinjina kai Mom tayi “OK! I known that”

In short amsa ta bada.

Daga nan ta shiga nazari tayi shuru kamar mai yin tunanin wani Abu

Juyowa Junaid yayi yana kallon mom d’insa yasau murmushi sannan yace “let me go and pray, naga kamar ranki ya sosu KO?”

Yakai karshen maganarsa tare da mi’kewa ya nufi toilet.

Itama murmushin tayi jin abunda yace.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button