Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 62

Sponsored links

A guje suka dinga rige-rigen shigowa dan ƙarar tata ta matuƙar ratsa kunnuwansu. Basu kaɗai ba hatta da hadiman dake musu hidima a sashen babu wanda zai ce baiji ƙarar baiwar ALLAHr nan ba. Ganinsu baisa ya dakata da dukanta ba. Cikin wata iriyar fusata babban ɗansa da itace mahaifiyarsa Husam yay wani irin kukan kura ya hankaɗashi baya sai da ya daki bango. Baiyi wata-wata ba kuma ya damƙi wuyan rigarsa ya shaƙeshi dan shima yaron tsageran kanshi ne. Kaf halin Miran Jasim ɗin ya kwaso, sai dai duk da haka yana bala’i bala’in son mahaifinsa. Ya jima da ciwon dukanta da mahaifinsa keyi duk da bata taɓa fitowa fili ta sanar masa ba. Tun yana yaro ko shatin yatsu ya gani a fuskarta ya tabbaya sai tace bakomai ko bigewa tayi. Sai bayan ya girama ne ya fahimci mahaifinsa ne ke marinta kamar yanda suma sauran matansa biyu ba tsira sukai ba.

 

Rawa jikin sauran matan nasa ya shigayi, sun rasa ma wa zasu bama ɗauki, shi da Husam ya shaƙe ko Buhaysah da ke kwance tana madoɗowar azaba. Gwara kansa da bango da Husam yayi yana ƙaraji ya sa matan yin kansa da sauri suna kuka da roƙon Husam ɗin ya sakesa. Amma ina yaron nan ƙara gwara kan Miran Jasim yake yana kai masa naushi kamar ba mahaifinsa ba. Ga wani irin ƙarajin ɓacin rai yanayi mai haɗe da kuka.

Sukam al’amarin nan yafi ƙarfinsu, hankali tashe suka shiga neman number Miran Arshaan amma ba’a daga ba. Har kira uku babu alamar za’a amsa dole suka maida akalar kiran ga Daneen Ammarah domin ta sanar da Mammah da Sayeed Fayzul-haq kasancewar sun san yana ɗan jin shakkarsu, dan daga Malikat Haseenat ɗin har Sayeed Fayzul-haq ɗin basa ɗaukar raini ko wasa a garesu dama masarautar kowa yasan haka.

 

Wayar ta riski Sayeed ne lokacin da yake fitowa daga sashen Tajwar Eshaan bayan masa rakkiya daga sallar la’asar da suka idar. Itama Daneen Ammarah lokacin tana ƙoƙarin tashi da ga abin salla. Hankali tashe duk suka nufi sashen Miran Jasim ɗin har da Malikat Haseenat ɗin da aka saka a mota, dai-dai da shima Miran Arshaan ya nufi can dan shima yayi mamakin rashin ganinsa wajen tattaunawar da akayi duk da yasan dai ransa a ɓace yake matuƙa. Dan tun jin Tajwar Eshaan bai fito fada ba da safe ransu ke’a jagule. Yanzu kuma a wannan zaman ashe ma akansu ne akayisa duk da dai shi Tajwar Eshaan ɗin bai fito fili ya ambaci suna ba, amma duk da wannan sanin da yay akan Miran Jasim ɗin ya zaɓi yimasa zamba cikin aminci dan a ganinsa lokaci yayi da shima zai dakata da ga rakkiyar Miran Jasim ɗin ya fara yaƙin kansa…

 

Da ƙayar aka ɓanɓare Husam da ga shaƙar da yay ma Miran Jasim, yaraf ya zube ƙasa hannunsa kan maƙoshinsa yana kakari. Idanunsa sunyi ruƙu-ruƙu tsabar yanda yaji shaƙar nan, ga kansa daya fashe saboda ƙuma masan daya dinga yi sai jini yake yi. A gefe ga Buhaysah da ke kukan wahala Husam ya je ya rungumeta yana kuka da alama dai yaji mata ciwo a baya koma ya karya ta ne oho. Malikat Haseenat da ta ɗan girgiza kanta da duban Sayeed. A matuƙar ruɗe Sayeed Fayzul-haq ya jinjina mata kai. Waya ya ciro yay kiran clinic ya bada umarnin a kawo ambulance ƙofar sashen Miran Jasim ɗin…..

 

A gaggauce aka miƙa Miran Jasim da Buhaysah asibiti. Husam kuma Malikat Haseenat tasa Daneen Ammarah su wuce da shi sashenta, yaron sai kuka yake mai matuƙar cin rai da zai baka tausayi, dan duk wanda ya kalla mahaifiyarsa yasan akwai babbar matsala a bayan nan nata da mahaifinsa ya taka

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button