Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 35

Sponsored links

wata kazamar kwanika nayi kafin na Yaye Bilkisu sai na samu wani cikin a lokacin ma Uwa da Abba Basu damu ba sai da Suka ga na haifo yan biyu Nazifa da Nazira,daga nan suka fara guna guni Ina ta haifo musu mata tun Abba baya Jin zuga har ya Fara dauka yana yiwa yaran wulakanci,ana haka na samu ciki sai Suka Fara Allah dai yasa Namiji ne matan nan sun ishe mu,Uwa ba zagin da bata min ta Fara min habaici tace matan ma meye amfaninsu wasu ma Karshe su Zama Yan Iska, Ina girmamata sabo da uwar mijina ce Kamar uwata ce amma bata gani,tun Ina da ciki suke hada kai da Yan uwanta su fa wallahi yanzu baza su yarda a haifo musu Mata ba ehe,Ranar da na fara nakuda Ina Shan wahala Nakuda nake me tsawo Uwa tana kallona Ina wahala taki ko kulani,ciwo ya isheni na fito da rarrafe Ina hawaye nace dan Allah kisa a kaini asibiti,Uwa tace uban wa zaiyi asarar kudinsa ya kaiki asibiti ki haifo Masa mace babu me kaiki sai dai ki mutu,Kafafunta na rike Ina rokonta Ina kuka ta kwace kafafunta ta shige daki haka na koma dakina,Bilkisu lokacin suna Yara ba abinda zasu iya Yi min sai kuka suke na tura Bilkisu ta Kira min makwafciyar mu da muke mutunci wata dattijuwa itama bata nan ranar,Abbanku ne ya shige Uwa tace Wai matarka nakuda take wasu matan suna Kan Hanya,Fuska ya bata yace ai sai tayi ta haifar matan wlh ko ta Haifa bana so ni ba nawa bane ko barka Kar Wanda ya min ya juya ya fice, ana haka sai ga Dattijuwar Attine ta dawo daga unguwa Bilkisu taje ta kirata itace ta taimaka min har Allah yasa na haifo mace katuwa,tana yanke Mata cibi Uwa ta fado dakin lokacin wata Sabuwar nakudar ta taso min bana cikin hayyacina karfina ya kare ban San ma me nake Yi ba, Uwa ta kwace jaririyar ta zazzagi Attine ta fisge Yarinyar ta sakata cikin wani tsohon zani tace bama so wallahi Indai macece shike nan kullum mace mace Ina son jikokina maza a dinga haifo Mana mace sai kace gyada, Dana bazai kare a bauta ba ta fice da Yarinyar Attine tana rokonta tayi hakuri amma ko a jikinta mota ta Shige a yanda tace ita Kano taje ta jefar da yarinyar a wani kauye bata San ma kauyen ba,kafin ta dawo na haifo wata Yar tawa katuwa,bayan na dawo Hayyacina nace Attine yan biyu na Haifa Ina dayar? Attine tace Uwa ta kwace ta fice da ita, me yasa Kika bata Attine na fashe da kuka,kuka nake gashi bani da karfi a jikina da kyar Attine ta taimaka min nayi wanka da ruwan zafi aka gyara ko Ina Kal kal,Bilkisu na aika ta siyo min abinci naci Suma Suka ci,Attine ta wanke jaririya aka sa Mata sutura kuka nake an dauke min yata,Attine tana ta bani hakuri,Abba ya shigo yana zuwa ya shigo ya kafe Cele da Ido ya ja tsaki yace aikin banza aikin wofi,mene a mace in Banda ta dinga jawo maka magana gasu Nan Muna gani duk sun lalace sai fitsara,nace wasu ba amma ba nawa ba,yace nakin fin na wasu Suka yi wa yasan me nakin zasu Yi kika sani ma ko Yan bariki Kika haifa,Salati na saki nace wallahi ka cika jahili Kuma ka sani wannan Baki ka musu wallahi idan naji yarka ta Zama Yar bariki cewa zanyi Allah ya bada sa’a tunda tun a duniya ka musu baki,Tsaki ya ja yace to suyi mana dama tunda Kika haifi mace kin sani wata ma Sai tayi ciki a gabanki ya juya ya fice,nace ta Allah ba taka ba.

Sai cikin dare Uwa ta dawo Babu yarinya,a lokacin na fito nace sai ta fito min da yata,ta zazzageni ni kuwa naci kwalarta na hadata da bango na shaketa a bango Muna haka Abba ya shugo ya kwaci uwarsa ya kifa min mari,Allah yasa dai bai sakeni ba,washe gari Uwa taci gaba da kawowa yata hari zata sace ta,har aka rada suna ko hakika bata Bari an yankawa Cele ba tace ai baza ayi asarar kudi ba,Mijin Attine Malam Jibrin shine ya bada ragonsa da yake kiwatawa aka yankawa Cele,dama su basu taba haihuwa ba,su Yara man ko macen nema suke Allah bai basu ba amma ga wani an bashi baya so shi,Cele taci suna Rufaida sabo da rashin kauna sunan ma Sai dai suce na sa duk sunan da Naga dama su basu damu ba,Yan uwan Uwa ma haka suke zuwa su fada min Maganar da Suka ga dama ban Isa Kuma nayi magana ba,Muazu kuma ga son mace bai da hakurin Jima’i amma Kuma baya so ace Ina da ciki,Rufaida tana da Sati biyu na shiga wanka itace na wanka ma Sai dai na siya da kudina idan Ina so na gasa jikina shi dai bada kudinsa ba,sabulu na manta na dawo daki Kawai nayi arba da Sa’ade kanwar Uwa zata sace min Rufaida ta goyata,riketa nayi Muka dinga kokawa Allah yasa Ina da karfi na dinga jibgarta da kanta ta kwance min yata Saura kadan ta jefar da ita a kasa na kwace abata na ajiyeta a Kan gado na Kama Sa’ade sai da na kusa kasheta a dakina da duka motsi sai data kasa,a ranar Kuma Uwa tasa danta ya sakeni nace ba inda zani Zama daram,Rufaida na dauke gaba Daya naje har gidan Malam Jibrin nace na basu Rufaida halak malak su rike min ita,suka dinga murna har danginsu ba irin godiyar da basuyi min ba.

shi Kuma Abba yasa jaraba baza a bayar Masa da ya ba a dawo Masa da abarsa Kuma Uwa ce ta zuga shi sabo da so suke su sace ta,Malam Jibrin ganin ma Haka sai ya siyar da gidansa ya siyi wani a wata unguwar dama sana’arsa siyar da kayan miya,bayan na Basu Cele sai da na dade sanadin sakin kafin Muazu ya dawo dani dakinsa sannan yazo kuma Yana min naci nayi hakuri a sasanta naki yarda sai da ya Sha wahala sannan sabo da yarana na hakura aka maida auren domin na rigada na saudakar da farin cikina ga yarana sabo da dama wasu matan yawanci yanzu zaman yayansu suke yi.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button