Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 20

Sponsored links

Mami tace Kuma shi baida hankali sai kace yaro ba sai ya samu dattijuwa irinsa ba wannan wanne irin mutum ne, Auta yace bari Ni dai na bar Masa gidansa,Mami tace ya kamata wannan abin a bar Masa gidansa ne wannan ai wulakanci ne aikin banza aikin wofi rashin mace hauka ne Dan wulakanci ma yarinya budurwa ai shike nan ka fadawa Su Sultana su bar Masa gidansa su dawo nan,Auta yace ai Yaya Nawwar ya sani ma yasan da auren Shuru yayi da bakinsa yace tunda ba son Baffa kike ba yanzu mene ma amfanin a fada Miki Kawai yayi aurensa,Mami a ranta tace wato Nawwar baya kaunata ai shike nan a fili tace ba komai Auta jeka kawai, Auta ya juya ya tafi yaga Mami kishi karara ya fito lallai tana son Baffa.

Mami fasa girkin tayi ta kashe gas din gaba daya ta dawo bedroom ta zauna gefen bed ta saki kuka, Nawwar yau da wuri ya dawo gida Yana taya Mami Murna ta gama Idda ni kuwa palon Mami nazo da abinci iri iri Dana shirya na jera Mata a Dining sannan nayi docoration a dining din Muka kawo cake hadadde Muka ajiye table din yaji adon flowers red, munci gayu ni da Nawwar kayanmu iri Daya shadda Muka sa Fara kal mun zuba kyau,nace Baby ka Kira Mami yau ranar murna ce fa,Nawwar kiss ya manna min a saman lips sannan ya haura sama da sauri Yana Kiran Mami na,knocking yayi Shuru Shuru a hankali ya tura kofar ya shiga tun daga bakin kofa yake Jin sheshekar kuka,da sauri ya karasa Gaban Mami dake zaune a gefen bed tana sharbar kukan soyayya,Hannu yasa zai taba ta a zabure tace karka sake ka tabani munafuki ai ban san baka kaunata ba sai yau,da Kai za a hada baki Kai da ubanka kasan da zancen kaki fada min karka sake kulani,Nawwar yace me nayi Mami hankalinsa ya tashi tace ban sani ba Kai da matarka karku sake Shiga harkata tunda Baku da mutunci,Nawwar ya sake Kai hannu zai riketa ta doke Masa hannu tace get out,Jin Nawwar shiru yasa na taho Nima Ina cewa Baby zamu je unguwa fa ko Mamin bata nan na shiga ciki nima,a wajen na daskare ganin Mami tana kuka Nawwar Yana gabanta yana bata hakuri Yana ta lallashinta yana lallabata ta fada Masa laifinsa, ganin haka na juya Zan fita tace dawo kema munafuka Ina Zaki dawo sai ku zuba ruwa a kasa ku Sha dan Sulaiman yayi aure sai me sai akace muku mutuwa zanyi se waiting? sabo da Baffanka yayi aure nace se waiting? So what sai aka ce muku Zan mutu ko mene,namijin banza namijin wofi ni Namiji ya Isa ya bata min rai,Nawwar yace au Baffa aure zaiyi? Kai dalla rufe min baki gulmamme ai kasan komai ai Auta ya fada min komai yace wani satin zaiyi aure ka San zancen ma da sa hannunka kuke boye min to sai me ance maka Ina son ubanka ne,Sai yanzu Nawwar ya fahimci kishi ne yake damun Mami yace Auta ne yace Miki na San zancen? tace ae Auta baya karya,dariya Nawwar ya boye yace wallahi Wallahi kinji na rantse ban San zancen ba amma dai naji su Sultana suna kus kus da zancen na zaci ai gulmar Mata ce shima Nawwar ya sake shigar da Mami,Nace Kiyi hakuri Mami bamu San zancen ba wlh Kuma Inshaallah kece Zaki koma gidanki ne ke kadai wace ma ta Isa ta shiga gidan nan ban ci ubanta ba ai Baffa naki ne ke kadai,Tsaki Mami tayi a ranta ma tafi yarda da Rabi tasan zata iya Hana auren ko da tsiya tsiya,tayi kwanciyarta ta juya Mana baya,nace Celebration din fa? tace Cele what? Ku tafi ku bani waje baza ayi Celebration din ba,tashi mukayi Muka fito nace kai Mami fa wallahi sun koma Yara abinda sukeyi ko mu baza muyi shi ba,Nawwar yayi dariya yace ai auren da mace tun tana karama ake yi musu tare suke tasowa su girma tare shi yasa Suka fi kowa shakuwa auren da akwai shakuwa,Lallai Auta Dan Iska ne shine yace na san zancen yaron nan haushi na yake ji akan na aurar da Wise ga Papa shike nan ya rainani,Dariya nayi nace nidai a samowa Auta wata Kawai mun shiga Uku da shi ya iya hada bom haka,Nawwar a waya ya Kira Auta yace yazo zai aike shi Office.

Ya manta yayi gulma yazo da sauri Yana zuwa Nawwar ya mammake shi ya dinga cin uban Auta yace ka hadani fada da Mami,Auta yace Sorry Yaya Kuma sai ka mareni ,fita dalla Kar na sake ganinka tunda Kai baka da hankali,Nace haba Kuma sai ka doke shi na Kai hannu Zan ruko Auta Nawwar ya min tsawa yace ke wannan balagaggen yaron Zaki rike to Auta Yana zuwa ki saka hijab,Auta ya juyo ya kalli Nawwar sai da ya bari yaje jikin kofa yace ni me Zan ci da matarka old version ya fice da gudu,dariya nayi nace kaji yaro wallahi sai naci….Shuru nayi,yace Sorry new version karya yake da za a bashi ke karba zaiyi da gudu yasan bazai samu bane abu lutsu lutsu haka,dariya nayi ya jawoni jikinsa.

Star yau fada sukayi da Malam Abhulkhair Wai ya Dade a masallaci bai dawo gida ba,Star tace kaje kayi ta karatu baji ba gani murya kamar ta zakara haka akeyi ai sai a dinga Yi ana bawa iyali hakkinsu,Malam yace ke ai kin rainani kije masallaci kiga yanda ake gaisheni ana girmamani ke Kuwa ina,Star tace ka gama min kukan kullum,kana rokata local government,kazo tumbir zigidir yanda kazo duniya sannan kace Wai bana girmamaka sabo da Allah ai Ina kokari ma su mutanen kaje musu a yanda kake zuwar min ka gani idan zasu sake saurarka,ai wlh bata kamata ma na gaisheka ba,Ni ya kamata ka gaisar kullum kace ya fargaban jiya,tunda a zauce zaka zo min kana ihu gaka ba Kaya ai abin fargaba ne amma sabo da kokarinmu na Mata washe gari harda gaisuwa wlh bazan gaisar dakai ba ai baizo a musulunci dole ba Kaine ma ya Dace ka gaisheni,bazan gaisar dakai ba fa Abhulkhair yawwa kuma body lotion Dina ya kusa karewa ka min transfer,kullum ka Tara min gajiya Kuma kana jira na tashi na gaisheka cab ashe zaka bushe,Malam Abhulkhair dariya yayi kawai yace ke komai naki yayi kinyi a rayuwa amma idan Kika tashi fadanki Kawai bi kike ta kaina,wa yace ka Dade a masallacin anyi karatu an Gama ka dawo muyi namu mana muma nifa baza a cuceni da malinta ba Dole ka bani lokaci na yawwa Kuma kayanka na gaji da ganinsu dinki kala uku ka Kara tun Aurenmu sabo da haka muje a siyi Kaya sababbi sannan kana Nan kaya ka dinga saka min a gidana Ina kallonka Ina Jin Dadi idan ba haka ba zanyi tawaye wlh,Malam Abhulkhair yace ya zanyi tunda na Zama mijin tace shike Nan naji yanda kike so Haka Zan koma amma kana nan kayan a iya gida Zan saka Miki? tace au da nufinka ka fita da su wata ta gani? Ni zaka sawa fa,an gama Aunty ya furta,tace yawwa Banda cin kudin marayu ko tallafin masallaci da ake sakawa a asusu kaci iya hakkinka albashinka na limanci da Kuma business dinka banda taba hakkin wasu,abinda zamuyi iya karfinka shi zamuyi,Yace na’am malama Tauraruwa wannan wa’azin ya shigeni,dariya Star tayi tace ai dai yau nace bazan yi girki ba a waje zamu je mu ci mu Dan shana,yace Inshaallah taso muje ki cudeni,Star tace wanka Mana please ni bana son gargajiyar nan mene cudewa Maganar dattijai,Malam dai sai yanda akayi da shi gaba daya star ta Gama mallake shi,gashi idan ya Mata laifi tayi ta jaraba,shi baida zafi ba ruwansa shi yayi Dace yasan dole baza ka samu Abu yanda kake so ba tunda kowa a duniya Yana da halin kwarai Dana banza Kuma baza kace zaka samu mutun dari bisa dari ba sai anyi hakuri.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button