Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 121

Sponsored links

Tunda suka shigo idanunsa kyam a kansu, yana zaune a falo zama na kasaita da izza da jiran ta inda zata bullo. Tun bayan dawowarsa sallar isha’i ya duba bai ganta ba. Shegen miskilanci ya hanashi tambaya har sai bayan kusan awa daya sannan ya bincik

a ta cctv camaras. Anan yaga fitarta harma da nufar sashen Malikat Haseenat ita kadai ko tsoro babu tattare da ita duk da darene. Yayi tsammanin zuwan bamai jimawa bane, amma sai gashi har yay wanka yaci abincin dare yay yan ayyukansa babu labarinta, harya kwanta da tunanin zai iya shareta sai hakan ya gagara, gangar jikinsa da zuciyarsa suka tabbatar masa bafa zai iya rayuwa babu mahadinsa ba. Shine ya dawo falo yay zaman jiran ganin ta inda zata bullo kusan awa daya kenan.

Gaba daya sai Iffah taji ta tsure da kallon nasa, dan haka ta koma da baya-baya ta labe a bayan Malikat Haseenat. Idanunsa ya dauke daga kanta ya maida ga Malikat Haseenat din shima. Cikin dan motsa lips dinsa ka dan ya furta, “Barka da dare Jaddah”.

Amsa masa tai cike da kulawa, tare da juyawa ta kamo hanun Iffah da ke labe a bayanta ta maidota gabanta. “Ga matarka nan tane tare dani tun dazun, ALLAH ya tashemu lafiya”. Daga haka ta saki hannun Iffah ta gara kekenta ta nufi Elevator.

‘”ALLAH ya huta gajiya”. Ya fada a hankali yana dan lumshe ido da risinar da kansa alamar girmamawa a gareta. Shiru falon bayan tafiyarta babu wanda ya sake kwakwkwaran motsi. Shi ya

 

zuba mata idanun nan nasa masu kaifi, ita kuwa tana tsaye a inda Malikat Haseenat ta barta kanta a kasa tana wasa da yatsun hanunta, tsigar jikinta sai yamutsawa take dan har cikin jininta takejin tasirin kallonsa a kanta. Sun kwashi mintuna masu dan tsaho a haka kafin ya mike, gabanta yaje ya tsaya, ta rumtse idanu da karfi a tunaninta saukar mari ko wani abu dai mara kyau zata ji daga garesa. A mamakinta sai jin tattausan tafin hannunsa tai a saman nata ya zare jakkar hanunta, cikin takun nan nasa daddaya cike da izza ya rabata ya wuce.Numfashin da ta rike a kirji da makoshinta ta saki da karfi, sai kuma ta bude idanunta tabi bayansa da kallo har ya bace ma ganinta. Dan tarin dake neman rike makoshinta ta fara, dole ta nufi dining room ta samu ruwa ta sha. Daga haka takai zaune tana sauke numfashi. Sai da ta dan samu nutsuwa sannan ta tashi tabi bayansa tana addu’a a ranta.

 

Bata da tabbacin a inda yake, dan haka kawai ta nufi inda zuciyarta ke raya¬† mata¬† da fatan ALLAH yasa ba’a nan din yake ba. Sai dai kuma da alama ta taki rashin sa’ar. Dan tana shiga taci karo da shi zaune a kan gado da lap-top kan cinyarsa. Dakin babu haske mai karfi, sai hasken screen din laptop dinne ya haske kyakykyawar fuskarsa ma’abociyar kamewa da

kwarjini. Sum-sum ta wuce hanyar bathroom tana dan turo baki. Sai da ta gama tsaftace kanta ta fito cikin bathrobe, yana a yanda ta barsa, hakan sai ya bata damar tsayawa ta bayansa ta shirya cikin kayan barci masu dan kauri da turarruka. A take kamshin dakin ya sake karfi. Fahimtar kamar fushi yake ya sata takowa inda yake cikin sanda, zaune takai gefensa amma ya share abinsa bai ko nuna ya san da zamanta ba. Cikin dan bata fuska da jin haushi sharetan da yay ta zame ta kwanta tare da dan ture lap-top din tasa kadan ta daura kanta a cinyarsa ta kwanta. Da kyar ya iya cigaba da rike kansa yaki kulata. Ganin ya cigaba da aikin dai ya sata kurama fuskarsa idanu, sai kuma ta kai hanunta kan kwantaccen gashin kumatunsa ta fara masa tafiyar tsutsa. (@) Yarinyar nan da tsokale-tsokalan masifa kike * ). Yayi kokarin ganin ya danne ya cije amma aikin na neman gagararsa, baima san sanda ya cije lips dinsa da rumtse idanunsa da dan karfi ba.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button