Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 72

Sponsored links

A cikin masarauta tako ina an gama baza kunnuwan jin fito da gawar Zawjata-almilk. Hatta da Malikat Haseena bata tare da nutsuwarta gaba ɗaya. Tun ana ƙirga sakanni a bayan sallar asubahi har aka koma mintuna, mintuna suka koma awanni babu wani labari. A take aka koma ƴar ƙus-ƙus tun daga kan hadimai har manyan masu faɗa ajin masarautar.

Yayinda suma Hadiman sashen Shahan-shan suke zaune jigum-jigum na jiran tsumayen abinda kowa keda tabbacin zai kasance. bakunansu cike yake taf da abubuwan faɗa akan abinda suka wayi gari da shi mai matuƙar rikitarwa da zai maimaita faruwa bayan ya faru ga duk wata Zawjata-almilk data kwana ta tashi a wannan sashen. Duk ɗunbin yawan abin cewar iyakarsa zukatansu dan ko’a tsakaninsu bai faɗuwa balle gulmantawa a waje saboda tako ina camara ce zagaye da su…..

Ba’a safiyar yau ba, ita tun ma a daren jiya tai hanun riga da nutsuwa. Gaba ɗaya a daren ko sau ɗaya bata iya ta rintsa ba. A maimakon barci ma idanunta akan sashen Shahan-shan da kowa ke iya gani daga nasa sashen a cikin masarautar suka kwashe mafi yawan awannin daren na jiya. Tayi yunƙurin kiransa amma wayar a kashe, hakanne ya sake ɗaga mata hankali da jin zafin wannan hukunci na Malikat Haseenat a karo na farko. A ganinta ganganci ne miƙa nagartacciyar yariya irin Iffah hannun gudan jinin nata bayan Mamma tasan minene makomar yin hakan ga rayuwar yarinyar. Duk jarumtarta a duk sanda ta tuna zuwa safiya gawar yarinyar ce zata fito takanji ƙwalla sun cika idonta. Amma takan danne ta hanasu fitowa har garin ALLAH ya kammala wayewa…

Tun idar da sallar asubahi bata iya ta motsa ba, ƙirjinta ne ke matuƙar bugawa da jiran tsammanin mummunan labari.

…Ƙarfe takwas da rabi dai-dai agogon ƙasar ɗaya daga cikin amintattun Hadiman dake gyara ɗakunan barcin na Tajwar ta iso cikin faɗuwar gaba hanunta ɗauke da akwati da aka kawo yanzun nan daga sashen Malikat Haseenat matsayin kayan da Iffah zatai amfani da shi. Zuciyarta har wani zallo take na fargabar abinda take da tabbacin

 

tozali da shi kamar yanda sukayi a baya ga sauran Zawjata-almilk da suka shuɗe. Ta tura ƙofar cikin sanɗa tana mai ambaton sallama da rawar harshe badan tana tunanin samun amsa ba. Ganin Iffah kwance a saman gado, lulluɓe da lallausan bargo baisa taji ƙwarin gwiwa ba. Tai yunƙurin ajiye akwatin hanunta, cak ta tsaya dukkanin idanunta na fitowa waje dan firgici ko sumar tsaye sakamakon juyi da Iffah tai alamar gyara kwanciya. Akwatin ta saki ƙasa ta shiga jan jikinta dake ɓari baya-baya harta dangane da ƙofa gab…..

Iffah dake ƙoƙarin gyara bargo idanunta rufe ta buɗesu da sauri saboda jin ƙarar bigewar hadimar. Da mamakin jinta kamar a gado ya sata shashshafa hannunta. (Tabbas gadonne) ta ayyana a zuciyarta tana sake buɗe idanunta da ƙyau tana mai yunƙurin tashi zaune. Tuni hadimar nan ta sake firgicewa, da lalube ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fita a guje. Kallon ƙofar Iffah tayi, sai dai hadimar ta gama ficewa bayanta kawai ta ɗan gani kaɗan da wulgawar mayafinta. da sauri ta yaye bargon da bata san ya akai yazo jikinta ba. Ta dire ƙasa mamakin duniya na cigaba da dabaibaye ta. “Wacece wadda ta fita? Mi tazo yi? Wai ta yaya ma na dawo saman gadon nan bayan a ƙasa na kwanta?”. Ta shiga jerama kanta tambayoyin da bata san inda zata samu amsarsu ba. Sai kuma ta ɗan kamo rigar jikinta ta kai hancinta. “Ya ALLAH, da gaske fa wannan mayataccen ƙamshin a jikina ne?”. Ta sake faɗa a fili tana sake shinshinar rigar……

A ɓangaren jama’ar masarauta dake a zaman jigum-jigum kam fitar hadimar nan ya isar da saƙon Zawjata-almilk na raye. Da farko duk wanda zancen yaje kunensa ɗaukewar numfashi na wucin gadi ne ke riskarsa, sai kuma rashin gaskatawa a zahiri ya biyo baya. Hatta da Malikat Bushirat da Daneen Ammarah yanayi da ruɗanin jin hakan bai tsallakesu ba suma. A kusan tare suka ɗauka wayoyinsu domin neman Iffah ko zasu samu jin gaskiyar zance. Cikin Sa’a kuwa ta Daneen Ammarah ta fara shiga….

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button