Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 21-22

Sponsored links

Nawwar ficewa yayi daga part din Mami wayarsa ya dakko ya Kira Auta,Yana dagawa yace ka samu Baffa ku warware matsalar Mami wlh ta damu, Auta yace kana ganin ba matsala yanzu? Kai karka raina min hankali ka fadawa Baffa mana, Alright yace Auta ya nufi part din Baffa sanye yake cikin gajeren wando da yar rigarsa wasu farare ya saka hannaye biyu a aljihu wando haka ya shiga part din Baffa,Ya samu Baffa da Papa a Palo suna hirar su ta zumunci,Auta gaida su yayi,Baffa yace Auta ya akayi ne? Yace Baffa zaka iya zuwa daga yau,Baffa yace to Nawaf dina farin ciki ya ishi Baffa bakinsa yaki rufuwa har sai da Papa ya tambaya Wai lafiya dai ko? yace Mamin Nawwar kasan tayi Idda to yarana sun wuce min gaba yanzu haka a saukake za a maida auren nan,Papa yace mashaallah na tayaka murna Yaya ashe har tayi Iddar, yace ae Mana yau ma,yace to tun kafin zawarawa su fara kawo hari ka koma ko ka turani na Fara share maka hanya ko abokinka Alhaji Muaz,Baffa yace a’a ni kadai ma zanje gwara naje Ido da ido, Papa yace to ba damuwa ka bari sai gobe ko ka Kara Mata kwanaki tunda yau ta Gama Idda,Baffa yace hakane a bari to ta Kara kwana ukun zai fi.

Bangaren Mami kuma Jin Baffa bai zo ba shuru Shuru sai hankalinta ya sake tashi a Haka ma tana kokarin dannewa sabo da kunyar yaranta.

Auta ne ya shigo bayan Sallar Isha da Sallama anci wanka cikin kana nan Kaya hannunsa Daya a cikin Aljihu Daya Kuma da ledarsa,Mami tana Palo a zahiri kallo take Amma a zuciyarta ta fada tunani,Auta ta gani tace Nawaf daga ina haka? ya gaida Mami ta amsa ya ajiye Mata ledar yace Mami gashi siyo Miki nayi,Mami tana dariya ta bude ledar ta duba sai taga tsire lafiyayye yaji hadi da fruits salat da wasu snacks,Mami tace Autana na gode Allah ya maka Albarka a Ina ka samu kudin? Ni shike nan ban Isa nayi abu ba sai ace Ina na samu kudi to Baffa ne ya bani,Ni yanzu sai abinda nake so a wajen Baffa yace zai siya min mota kwana nan,Mami tace to na gode Auta a wajen ta bude tsirenta tana ci Mami akwai son tsire,tace ka je wajen Nawwar yace yanzu zanje ,jeka ka dawo muyi hira yace to ya mike ya fice, motar da kankabarsa ke sawa ya dakko ta ita ya koma ya Bude ya dakko wata ledar ta su Nawwar ma tafi girma Wai su ba mutum daya ne zai ci ba,Muna Palo Nawwar yayi matashi da cinyata Muna kallo Muna hirar mu Auta ya dinga Danna door bell sai da Nawwar ya kule yace wai waye ya shigo Mana,Auta ne ya shigo yace wlh nasan sai kai,yace to gidanku na ango da Amarya ai ba tsari na fado muku ciki Baku shirya ba ko,Uhm munji sarkin iya zance cewar Nawwar,Nawaf Zama yayi ya kalli Nawwar yaki tashi Yana kwance yayi matashi da cinyata,kasa kasa yace da wani ne da yanzu an dame shi ance bashi da kunya, Aunty Ina yini? Nace lafiya kalau Auta ya gajiya ya labarin aurenka ne,Auta yace hmm ya Mika min Leda tare da cewa gashi Aunty,Nawwar yace ya fasa Auren ai,inji wa?  Auta ya tambaya da sauri yace aure Yana nan ba gudu ba ja da baya,Nawwar yace yaro rikon aure da wuya kawo kawo ma ta isheka me aiki babba ma yaya ya Kare bare Kai,yace karayayye ba shine ke tsoro ai Allah ne yake ciyarwa ba dabara da wayon mutum ba,Kai nufinka kudinka ne yasa kake ci da Aunty kana bushasha, Nawwar yayi dariya yace a’a kudinka ne Auta, yace Allah ne dai da badan Allah yaga dama ba sai ya baka kudin Kuma ya hanaka ka bawa iyalinka Aunty da yanzu kyawun Nan ya fece ta dagargaje ta lalace da idan ance ma ka kwanta a cinyarta baza ka je ba,amma yanzu Allah ya baka ikon kula da ita shine zaka ce ni bazan iya ba to Allah ne zai bani nima,Nawwar yace 1-0 Auta Ina ta dariya na dauki ledar nace Auta mun gode,yace kullum ke ba a Maganar kirki dake sai yawu sai kace maye yaga wani ransa ya biya,nace Nifa bana son wulakanci Auta Kai ba a abin kirki da kai sau daya fa kazo kaga yawun nan shike nan ka sani gaba,Nawwar tashi yayi ya bude tsiren Auta Muka durfafi tsire da ci,yace Yaya yau anci madari,Nawwar yace Allah naso na kalli wasan nan,yace Wasa yayi baka ga yanda aka wulakanta Madrid ba yau,modric duk kyansa yau jahilci yayi, suna ta hirar ball har Auta ya tashi yace wajen Mami zai je,Nawwar yace to mun gode Auta yau anyi abin kai,Naga alama ko na mutu Auta zai rike matata,Auta yace in aureta kuwa wlh ba ruwana mantawa zamuyi da Kai tsaf,Nawwar Yana dariya yace to bazan mutu yanzu Dan Iska Ina nan sai na tsufa tukuf ni da ita,Nace Inshaallah aniyarka ta bika Auta,yace Ameen tunda aniyata me kyau ce ni bana gudu ta bini, yau a bangaren Mami ya kwana dakinsa daban bai koma gida ba Suka Sha hirarsu.

Iyamami ce taje Kauye ta samo yarinya bazawara sakin Wawa a danginsu ta kawota har gidan bangarenta tace ta samowa Papa matar aure lallai sai ya aure ta,Papa yace wallahi bazai Aura ba Iyamami ta dage sai Papa ya Kara aure ga Sabreen ta samu Iklima sun hade kai sai sun kori Wise,sun hana Wise sakat a gidan nan tun bata damuwa har ta fara damuwa a ranta,Seraline ta Kira tace tazo Dan Allah sabo da Indai Shawara ce sai Seraline Allah ya bata fasahar yin abu cikin hankali idan Kuwa Star ce cewa zatayi Kawai aci ubansu a musu dukan tsiya,Nima Haka zance,Yar Zabil ma bare Mandula mijinta ne Kawai ya Isa da ita shima darajar so ne tana mugun sonsa shi yasa sai yanda yayi da ita,Seraline ce ta Kira Sabeer ya tafi Katsina wajen Yan Uwansa baya gari tace Baby dan Allah yau zanje gidan Wise,yace ban son yawo kin sani kullum fa sai Kun hadu a makaranta.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button