Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 130

Sponsored links

Tunda ta fito a mota hadimai ke fama zubewa gaisheta. Kafin ma ta karasa ciki an kaima Malikat Bushirat labarin zuwan nata. A zahirance dai batace komai ba har Iffahn ma ta karaso. Gaba daya hadiman dake zagaye da ita ma wani irin zubewa sukai bisa gwiwunsu lokaci guda, dan wani irin kwarjini Iffah’r ta musu naban mamaki, sannan koba komai ita din dai Zawjata-almilk ce. Hannu kawai ta dan daga musu dai-dai tana kaiwa cikin kujera da wani irin salon zaman kasaita na kafa daya kan daya. A hadiman babu wanda bai girgiza da salon Iffah’r ba, dan kowa yasan duk da take matsayin Zawjata-almilk a gaban Malikat Bushirat dole ta risina kuma kasa ne wajen zamanta. Sunta satar kallon Malikat Rushirat din da tunanin ko zatace abu, amma sai sukaji shiru, hasalimal sau daya bata motsa da ga zamanta ba balle a karanci wani abu da ga gareta.

Wani irin kallo Iffah ta watsa musu da masu alamar fita da yatsunta. Har ko rige-rigen fitar suke duk da sun so ganin yaya wasan zai kare. Falon ya dauki shiru na tsawon lokaci batare da wani cikinsu ya motsa ba, hasalima ita Iffah ta maida hankalintane ga wayar Tajwar Eshaan da ke a hannunta tsabar rainin hankali ma browsing abu takeyi hankalinta kwance kamar ta manta gaban wanda take.

Malikat Bushirat ta dago idanunta da sukai wani irin kadawar bacin rai ta zuba mata, tsahon sakanni kafin ta nisa da kyar cike da zafin rai. “K har kina ganin kin kai wani matsayin da zaki iya jayayya da ni kenan?”.

Duk da sarai Iffah ta jita sai batako motsa ba tsahon wasu sakanni. Kafin ta motsa lips dinta batare da ta daina abinda take a wayar ba ta ce,”naga ai bakya bukatar amsa tunda har kin fahimci hakan Mother in-law. Kuma duk abinda kikaga Iffah tace zatayi sai ta yishi ki rubuta ki aje, dan hakan halitata ce bana manta gabar daukar fansa musamman akan jini na”.

“Humm ki taka a hankali, na fiki hatsabibancin yariya. Ki kama kanki kodan cigaba da rayuwar ahalinki a doron kasa”.

*murmushi mai sanyi Iffah ta saki tare da dagowa ta dubeta ido cikin ido. “Barazana ne hakan in-law? To in barazana ce ki sanarma bokanyar taki bata iya aiki ba tunda har bata sanar miki ahalin Iffah sararin samaniya ne ba ganinsu sai da ga nesa akan yaro da babba. Ki fada min miyasa kika kirani da ina da yan ayyuka a gabana masu muhimmanci, idan kuma kin kirani din ne dan kawai ki jajjadamin karfin ikon naki da kasancewarki damisa da bata da banbanci da damisar takarda a wajena to”.

 

 

 

Ba karamin dukan zuciyar Malikat Bushirat kalmar (Bokanya) nan yay ba, dan maganganu ma da suka biyo baya sam bata jisu ba ko fahimtarsu, amma sai ta dake ta basar kamar shima bataji ba. Sai tama saki wani murmushin kasaita cike da izzarta tana ma Iffah’r kallon ke karamar kwaruwa.

 

 

 

“Bazan hanaki wasa da Zakanya ba, koba komai zan ajiye darasin da zai zama izna ga yan baya gareki yarinya. Ina son sanin dalilinki na shiga hurumin da ba naki ba kan shiga bital mali ki fidda kayan azumi”.

 

 

 

Dan murmushi Iffah tayi yanzu ma, sai kuma ta ajiye wayar hannuta ta sauke numfashi mai nauyi. “Ammie na yarda ke Zakanya ce, sai dai ki sani duk karfin bajintarki da iya farauta a saman kowa watarana tsufa kan iya sa ki rissina ji inki ta zama sarauniya bisa karfin ikon Ni bance nafi karfin kaddara ba, sai dai ki sani a tafin hannunna kike ke da komanki. Bana son cigaba da jayya da ke ko nuna karfina akan karfin ikonki da har mutane zasu kalla gazawarki ko kaskancinki a cikin idanunsu saboda daraja. Eh tabbas daraja, darajar abinda kika haifa ya zama mai daraja a cikin al’umma badan yafi kowa ba a wajen ALLAH ko ke da kika haifesa kinfi wani. Ammie why inada abubuwan ban mamaki da daga labulen sirrinki sau daya kawai sai ya hana wannan idanun naki barci. Sai dai bazanyi hakan ba, bazanyi ba saboda mutunci da kimar danki har sai in kin bijirema hanyar da nake son ki dawo. Kwana biyar da suka wuce naci karo da bakon ganyen shayi mai hadari matsayin wanda Shahan-shan zai sha. Na kuma cin karo da madara itama, dana bincika sai na gane da ga sashenki madarar take, ba kuma na raba dayan biyu shima ganyen shayin naki ne. Na gagara fahimtarki ko inda kika dosa a zahirance. Kowa dai ya kalla fuskar Maleek da taki basai ya sake kallo ba yasan jininki ne shi,dan kamminku a bayyane suke ta abubuwa masu yawa. Kema a karan kanki kin fada kin kuma maimaita shi din danki ne. To wai nikam wane buri ne kike son cimmawa mai alaka da makiyi a tsakaninki da shi? Kin ko san da ace yasha ganyen shayin nan ko madarar nan illar da zatama rayuwarsa sai tafi wadda zatama tawa rayuwar? Sannan ke da kanki sai kin dawo kina kuka da dana sani. Idan ma wani ke baki wadan nan abubuwan matsayin wani kariya washi ko gurbata tawa rayuwar to tabbas ki farka. Ki farka why tunkan guri ya kure miki ki rasa kofofin fita a wannan masarautar. Na rasa mikike nema? Mikike bukata? Mi kekike son zama bayan abinda kike a yau dinki da har in kika rike zata jagoranceki zuwa gobanki cikin salama kamar yanda Jaddah take a yau ga kowa”. Taja numfashi mai nauyi tare da dafe kai cikin kunar rai, sake dagowa tai tamkar bataga kallon wutar bala’i da tsanar da Malikat Bushirat din ke binta da shi ba ta cigaba da fadin…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button