Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 67

Sponsored links

Juyowa tayi taga daya daga cikin me aikin gidan tashigo parlourn, suna hada ido ta koma da sauri batareda ta dauki abinda aka aiko ta ba, dawo da kallonta kan Deen tayi da har lokacin yaki sakar mata hannu, kamar zatayi kuka tace;

“Dan Allah ka bari mana”….

Dagowa yayi ya kalleta tayi saurin yin kasa da kanta, sake rungumota yayi ya maida yatsun cikin bakinsa ya cigaba da tsotsa kamar wani jariri, idan ya saka guda biyu ya tsotsa sai ya cire ya saka wasu, haka ya dinga tsotson duka yatsun goma, sosai ta fita hayyacinta gashi takasa janyewa saboda tsattsauran rukon daya mata, tsabar jaraba hannun har zugi yake mata ga wani ja dayayi, har gane hakan akeyi ta spaces din da aka bari ba lalle dake lallen irin me yankan celotape dinnan ne…..

Sai da ya tsotsi yatsun son ransa sannan ya saketa a hankali yana sakin hannun….

Saida ta tsorota da suka hada ido dashi saboda yanda idonsa yayi ja ya chanza kamanni, mikewa tayi da sauri tana shirin guduwa idonsa ya sauka akan lallen kafarta, ba shiri ya mai da ita inda ta tashi yana zama a gabanta, kawai sai jin saukar bakinsa tayi akan yatsun kafarta, rintse ido tayi tana jin kamar kanta ze rabe gida biyu tsabar tsoro ga wani zirr da takeji kamar ana mata tafiyar tsutsa, shi ko besan ma tanayi ba dan abinda yasa a gaba shi kawai yake gani….

Sosai ya shayar da ita ruwan mamaki dan bata taba tunanin ze iya stooping low haka ba, tana ganin kazantar lashe mata hannu dayayi shine ze nuna mata bataga komai ba…..

Tana cikin wannan tunani taji lashe lashensa ya fara haurowa saman kafarta, ai batasan sanda ta hankadashi ba Allah ya taimaketa lokacin ya sassauta rukon daya yiwa kafar, ta kwasa a guje tayi hanyar sama, saida ta ganta ta fara hawa stairs sannan ta daga murya da karfi yanda zeji tace;

“Maye! Kazami kawai!”…..

Yajita sarai amma ko motsi ya kasa saboda yanda mararsa ta wani irin rikewa, kwanciya yayi a kasa hannunsa dafe da mararsa…….

Besan minti nawa ya kwasa a haka ba, sai jin muryar umm yayi akansa;

“Lafiya ka kwanta a kasa haka?”….

Tashi yayi zaune cikin muryarshi da bata fita sosai har lokacin yace;

“Lafiya umm, sannu da zuwa”……

Guri ta samu ta zauna tana fadin;

“Yauwa, baka da lafiya ne?”….

“Lafiya lau nake umm, kawai bacci ne ya kwasheni, yaushe kuka shigo?”…

“Tin dazu, muna dayan building dinchan nawa kasan bakin dayawa dole muka bude chan din ma, ka tafi part dinka ka kwanta mana”….

“Banajin baccin kuma, amma umm it’s the taron necessary?”…..

“Anna da bappa insisted”….

“But….”…..

“Shhhhh! Yanda anna da bappa keso haka za’ayi! You can excuse me!”……

Mikewa yayi da niyar tafiya kamar yanda ta umarta, saidai ko kafin ya kai bakin kofa yaji murya mami cikin masifa tana fadin;

“Dawo! Dawo! Dake kasan baka da gaskiya zaka gudu”…..

Dawowa yayi mamaki dauke akan fuskarsa na rashin gaskiyar da akace yayi…..

Hannun baby tee mami ta dago tana nunawa umm tace;

“Kalli hannunta dan Allah , ya za’ayi da girmansa da komansa ya ciji yar yarinya, wannan wani kalan mugunta ne?”…..

Baki sake umm ta kalli hannun tace;

“Cizo? A duka yatsun? Tadai fadi gaskiya ko abu me nauyi ta dauka hannunta yayi ja”……

“Bawani abinda ta dauka, dududu yaushe muka shigo gidan? Kuma ko kwaso kaya ba’ayi a mota ba haryanzu, kawai muguntarsa ce, ai babu abinda baze iya ba”…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button