Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Chapter 13

Sponsored links

At same time heart ɗinsu ke beating da karfi, ya jima yana mamakin wata zararriya ce wannan ta faɗo masa a ƙirjinsa haka, this is d first time da mace ta faɗa masa a jikinsa, wadda ba muharramarsa ba, babban abunda ya ɗaure masa kai yadda yarinyar ta ƙanƙamesa bama Alamar zata sake shi, yana jin duk wani moving ɗinta ajikinsa, hatta numfashi ta dake fita cikin sauri sauri, kamar jinjira haka ta kwanta masa luf tana sauke ajiyar zuciya,

Mutanen dake wurin kowa yayi zuru yana kallon ikon Allah, wasu kam sai godiya suke wa Allah daya kawo masu sauƙi, har aka amshe gun ɗin dake hands ɗinta,

Jahad kam wadda ke cikin matsanancin tashin hankali, ganin bala’en da hosana ke ƙoƙarin ja musu, cikin yanayi na firgici ta ƙarasa inda hosana ke jikin bawan Allahn nan ta ruƙo hannunta da ƙarfi ta fisge ta daga jikinsa tana cewa “Dan Allah kayi Haƙuri bawan Allah, ba da sanin ta tayi hakan ba, she did it unintentionally, tana da ta6in hankali ne…..’ muryar na rawa Jahad ke kora masa bayani,

Har time ɗim bai cire face mask ɗinsa ba, kuma bai janye idonsa daga na Yarinyar ba,

 

“Ki rabu dani !!!!” honasa ta faɗi tare da cire hannunta daga na Jahad ta matsa wurin mutumin nan, da ta faɗa mawa ta sa hannunta cikin nasa ta riƙe kam tana kallonsa cikin muryar kuka tace “dan Allah ka rabamu da waɗannan masu baƙaƙen kayan wlh sun takurawa rayuwarmu, duk inda mu ke bin mu suke yi, wlh ba mu bane muka kashe ta ba, mun faɗa musu sunki yarda, ni dai kace su rabu ni in ba haka wlh zuciya ta bugawa zatayi na mutu kowa ya huta…..’

“Hosana !!! Ba ki da hankali ne !! Kinsan wanene shi ki !! meyasa ki ke tona mana asiri ne agaban mutane,” jahad ce tayi maganar ranta a 6ace ta janyo hosanar da karfin gaske ta dawo gefenta,

 

Su dae mutanen dake tsaye tare da police ɗin sun zuba ido suna sauraron su,

 

Rai a 6ace hosana ta sake fisge hannunta daga na Jahad cikin ƙunar rai tace “ki rabu dani, ki ƙyale ni nace !!! meyasa kowa bai son mune !! Laifin me muka aikata, babu mai ƙaunar mu wlh Jahad ba zan koma cell ba sai dae a shigar da gawa ta, amma bani ba,’ tana gama fadar hakan ta koma wurin mutumin nan dae dake a tsaye, ta zura hannunta cikin lallausan tafin hannunsa ta rike gam, ta marairaice masa da kyawawan

idanuwanta tace “Dan Allah ka tafi dani,ka da kabarni anan, bana son ganin waɗannan masu fararen kayan (wato likitocin dake tsaye da nurses ɗin dake wurin) kuma bana son waɗannan masu bakaken kayan,” ta faɗi tana nuna ƴan sandan dake tsaye baki asake suna kallonta,

 

kwantar da kanta tayi a damtsen hannunsa, sannan tasanya dukkan hannayenta ta rungumo nashi, (mutu ka raba kenan)

 

Lumshe idonsa yayi a hankali, sai lokacin kallon police men ɗin dake tsaye a wurin yace “wane irin shashanci ne yasa ku kabar yarinya harta kwaci bindiga daga wurinki!!”? Ya tambaya yana kallonsa,

Rai a6ace wani inspector yace “kaga malam ka iya bakinka, mu jami’an ƴan sanda ne munsan me muke…” tunkan ya ƙarasa major ɗin dake bayansa wanda ya fusata rai a6ace yace “Ka iya bakin ka !! Kasan wanene shi!!!”?

 

“maganar wanene shi bata shafe mu ba, mu dae a bakin aikin mu mu ke,” wani inspector ne ya bashi amsa a yayn da ya fiddo da ankwa alamar zai sanya masu hosana,

 

Itakam ƙara kanƙameshi take yi, gaba ɗaya ta gama kashe mishi jikinsa, daurewa kawai yakeyi,

 

“Laifin me suka aikata”? Ya tambaya yana kallon ƴan sandar,

Wannan copral ɗin ne yayi saurin cewa “ana suspecting ɗinsu da kisan wata tsohuwa wadda take riƙonsu,”

 

Shiru ya ɗanyi tare da jinjina kai, kafin yace “Cancel the case (akashe case ɗin)”

 

ɗagowa su kayi jami’an ƴan sandan suna kallonsa cikin mamakin jin abunda yace, a fusace wannan inspector ɗin yace “malam wai wanene kai !! dame kake taƙama ne !! kaga ka kama gabanka kawai cikin salama, in ba haka ba, zamu haɗa dakai mu tafi police station…..’

 

Jikin major ɗin dake bayansa har tsuma ya ke yi wurin cewa,” Shut Up Stupid !!! ka iya bakin ka ƙaramin ƙwaro ko kuma nayi ƙasa ƙasa daku a wurin nan….’ cikin hanzari ya dakatar dashi tare da cewa “i did not allow u to talk again, last warn,’

Shuru major ɗin yayi sai faman huci yake yi tamkar zaki, rai a6ace ya wurgawa ƴan sandar bindigarsu ƙasa,

 

Matsawa Inspector ɗin yayi da nufin yasanya wa hosana ankwar dake hannunsa, amma sai mutumin ya dakatar dashi da cewa “karka kuskura !!! domin ban bada izini atafi da yarinyar nan cell ba, kamar yadda ta roƙe ni cewa bataso ta koma, daga nan ba inda zata je,”

 

Mamaki ne ya rufe ƴan sandan, inspector ɗin yace “idan ka cika shisshigi zamu sa bindiga mu kashe ka !! A wurin nna,”

Jinjina kai mutumin yayi tare da cewa “idan kuka kashe ni, ba hukumarku kaɗai bace zata shiga haɗari ba, gaba ɗaya sai an tada nigeria saboda raina kawai,”

 

Kansu fa ya gama ɗaukar zafi kowa mamakin wannan mutumin ya keyi, ganin ya toge yaki bari su ta6a yarinyar dake kwance ajikinsa yasa inspector ɗin cewa “wai dan Allah wanene kai!!”?

 

“Yanzu naji bayani” acewar mutumin bayan ya faɗi hakan ya zura hannunsa cikin aljihunsa ya zaro ƴar waya nokia, ya yi dialing wasu numbers da basu fi 5 digits ba ya miƙa wa, inspector ɗin wayar yace “Ka kira numbers ɗin dana sanya ka tambaye su*WANENE MARSHAL OMAR* za ka samu amsar da kake so,”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button