Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 140

Sponsored links

Ko dar Iffah bataji da komawarta sashenta ba. Sai ma farin ciki data tsinta kanta a ciki. Ga hadimanta duk an dawo mata da abinta, a ganinta ma ita wannan wata dama ce da zatai yakinta da kyau a yanzun. Wanka ta farayi bakinta dauke da addu’a, kasancewar duk tayi sallolinta tun a jirgi shirin kwanciya kawai tai ta haye gado abinta sai ko barci.

Cikin barci take jin kamshinsa na sake shige mata hanci, a zatonta mafarki take, sai tai kokarin yin juyi abunta. Jinta jikin mutum a gaske ya sata bude idanunta da kyar. Akan kyakykyawar fuskarsa ta sauke idanun nata. Tashi tai a dan zabure ya rikota, maidata yay ya kwantar yana mai tura yatsunsa cikin gashin kanta, sai kuma ya matso da fuskarsa saitin tata ya daura goshinsa kan nata hancinsu na gogar juna

 

“Yaushe kazo?”

Ta fada cikin muryar barci. Shiru kamar bazaice komai ba, sai da ya mula dan kansa sannan. “Dama zaki iya barci babu ni a tare da ke?”. Kankamesa ta sakeyi tana sakin ajiyar zuciya, itama a hankalin ta furta, “Kawai dan banda yanda zanyi ne”.

“Toni gani nayi yanda zanyi ai”.

Ya bata amsa yana sake matseta cikin jikinsa kai kace amshe masa ita za’ai. Luf ta kwanta kuwa suna sauke ajiyar zuciya a tare. Sai kuma ya hade bakinsu a hankali. Da ga haka labarin ya sauya salo…

Karfe uku nayi ya gudu, sai farkawa tai taga babu shi a dakin. Murmushi kawai tayi ta tashi zuwa bayi tai brush da tsaftace jininta ta fito. Madara mai dumi kawal tasha matsayin sahur. Duk da barcin dake cin idanun nata sai bata kwanta ba tayo alwala ta danyi nafilfili da karatun Alkur’ani. Bata tashi a wajen ba sai da tai sallar asuba, Tana idarwa kwanciyar ta sake yi, bata tashl ba sal azhar. Tayi mamakin barcin da tayi, amma kuma sanin yanayin da take ciki da rashin isasshen barcin da bata samu a Saudiya ba yasa ta fahirci akwai ramuwa dole dama.

Tsaf tai shirinta cikin kyakykyawar abaya kamar ka sace ta ka gudu. Dama ga ko’ina ya sake fita da fitar kwarjini da kyawun haiba na ciki. Cike da girmamawa a gareta hadimanta ke zubewa Rasa gaisheta lokacin data fito. Nuni tai musu da su tashi, cikin sanyin da ciki ya haifar mata yanzu ta basu izinin mata rakkiya zuwa sashen Malikat Haseenat da ga nan su wuce na Malikat Bushirat. Da girmamawa suka arsa mata tai gaba suna take mata baya. Duk da akwal tazara a tsakaninsu bata shiga motar da aka ajiye domin ta ba tunda ta fito, A kafa ta taka hadimanta na take mata baya. Dolene ta birgeka, dan yanda ta fito da kafan ma sal ta kara kima a idanun hadiman. Ta ko’ina kuwa ta gitta hadiman ne ke zubewa mika gaisuwa, hannu kawal take daga musu fuskarta da dan murmushi dan sam bata daureta ba. Yayinda Amintacciyar hadimarta ke amsa musu da baki ita kuma.

Tun kan shigowarta aka sanar da Malikat Haseenat da ke zaune Daneen Ammarah da Daneen Waheeda tare da ita. Sai Iftihal diyar Daneen Waheeda dake zaune a can gefe tana latse-latse a laptop. A nutse ta shigo bakinta dauke da sallama. Dan haka suka dago a tare. Sai dai kuma a hankali Iftihal taja sirrin tsaki da maida kanta ta cigaba da abinda take yi. Babu wanda ya jita, sai dai Iffah kam taga kallon da tai mata sarai. Amma tai kamar ma ita bata ganta ba ta nufi Malikat Haseenat da ta bude mata hannu fuska duke da murmushi alamar tazo gareta. Ita din ta nufa cike da kunya, ta durkusa a gabanta tana murmushi da gaisheta. Cikin murmushi Malikat Haseenat ta ce, “A’a kinga Hafidah tashi ki zauna keda ke fama da kanki, ALLAH dai ya raba lafiya”.

 

 

 

Sosai kirjin Daneen Waheeda ya buga, yayinda Daneen Ammarah ke murmushi kawai tana bin Iffah’r da kalion kasan ido, Bayan ta gaishe da su duk cikin girmamawa Daneen Ammarah ta nuna mata Daneen Waheeda. “Ga wata maman taki nan tazo kuna Saudiyya, nasan kin san dai sunanta da labarinta tun kafin yau”. Fuskar Iffah cike da murmushi ta jinjina mata kai. Kafin ta kara gaishe da Daneen Waheeda din da zancen cikin nan va sata sumar zaune, cikin murmushin yake ta kai hanunta kan Iffah’r ta shafa. Daneen Ammarah ta sake waiwayawa ta nuna mata Iftihal da tai kamar ma bata san mi ake ba “Wannan yar uwarki ce ita kuma, sunanta Iftihal, itace first born a wajen mamanki. Tanada kanne maza har uku”.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button