Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 3

Sponsored links

Cikin tausayawa Ayush ta kamo hannun Uman tana rarrashinta “Umma ki daina kukan nan, ki sanar mun abunda ya faru bayan nan”

Umma ta d’ago da rinanan idanuwanta tana kallon Ayush wanda itama kukan take ta gagara rarrashin kanta domin abun da ciwo,

Cikin karayar murya Umma tace “Ayush! Bayan na haifeki na nuna cewa ke d’iyar Alhaji ce, wanda hakan ya jawo rashin jituwa tsakaninsa da matarsa, nasa Alhaji kuka cirr da idanunsa yana rantsuwa akan shi bai ta6a kusantar zina ba, baisan ya akayi na samu cikinki ba, naji tausayinsa alokacin sai dai inaso ya amince da ke a matsayin d’iyarsa” bata karisa maganar ba taji Ayush ta katseta da cewa “tayaya Umma, taya zai yadda ni diyarsa ce bayan yasan ba alakar data shiga tsakanin ku, haba Umma”

Cikin kuka Umma tace “toh ki tsaya mana ki saurareni, ai a lokacin matarsa cewa tayi bazata cigaba da zama dashi ba, naji dadin hakan sosai saboda nasan ko bai Aureni ba zamuyi zaman dadiro ne da shi, Amma sai dai kash yana cikin bawa matarsa hakuri zuciyarsa ta buga lokaci guda Alhaji ya rasa rayuwarsa,

Innalillahi wa inna ilaihi raju’un Allah sarki Alhaji ka gafarce ni” ta Kara fashewa da wani irin kuka,

Ta cigaba da cewa bayan rasuwar Alhaji an gano cewa karya nake Anyi mun korar kare a gidan nan, har hukuma sai da ta kulleni daga baya mahaifinki yazo ya yi baili na,

Mutane sun kyamaceni, wasu har tofa mun yawu suke da zaran nazo wuce wa, gaba daya zaman cikin garin ya gagareni hakan yasa mukazo nan dajin da zama,

Na kuma yanke alakata da mahaifinki babu ni babu shi amma duk da hakan bai daina bibiyata ba saboda ke, yanzu haka yana kallon mu ta cikin madubinsa kuma yana jin duk abunda nake fad’a,

Rauninsa kuma kece”

Wani irin juya ido Ayush tayi tana wani yamutsa fuska kamar mai jin kyama tace “ni kuma? Tayaya rauninsa zai zama daga gareni yake, can’t believe”

Murmushi Umma tayi sannan tace “kwarai kuwa, duk wani abun cutarwar da zai sameki to shima haka, idan kika ji ciwo a jikinki toh shima zaiji zafin ciwon a jikinsa, shiyasa tin kina karama idan kikayi laifi bana dukanki saboda zai d’au fansa ne domin shi zaiji zafin dukan, idan kikayi zazza6i toh shima a ranar zai kwanta jinya, duk abunda ya faru da ke shima zai faru da shi, sai dai kuma shi ata 6angarensa duk abunda ya faru dashi babu abunda zakiji”

Ayush ido ta zaro waje still tayi tambaya atakaice “Umma duk meya jawo hakan?”

“Saboda rauninsa yana daga gareki ne, akwai abunda ya ajiye a jikinki wanda shine rauninsa, da zarar kin cire wannan abun toh duk wani tsafinsa zai lalace, duk wani sihirinsa zai karye, kuma daga karshe zai iya rasa rayuwarsa”

A firgice Ayush tace “Umma meye abun dake jikina? Inason saninsa”

Numfashi Sama-sama Umma take jaa saboda ba karamin azabtar da ita bokan nan yake ba domin tanaso ta fad’awa d’iyarsa sirrinsa wanda ba kowane ya sani ba,

Ta cikin madubin yake watsa mata tafashashshen ruwan zafi, duk jikinta yayi jawur ita kadai tasan irin rad’ad’in da takeji, amma ita Ayush bata san da hakan ba, ta zubawa mahaifiyar ta ido tana kallon ikon Allah “shin meyasa Umma taketa yunkurawa ne kamar wacce jikinta ke Mata kyaikayi”

Muryar Umma na rawa take fad’in “Zan gaya miki wani Abu Ayush ko zan mutu,

Junaid yana cikin mawuyancin hali, sun bada jininsa a wani tsohon DAMUSAN SU wanda yake bukatar jinin yaro, Damusan yana taimaka musu waran tsafinsu,kuma zai iya mutuwa indai ba’a bashi jini yasha ba, jinin mah sai wanda ya za6a bazai sha jinin kowa ba sai wanda ya burge shi, ankai mishi jinin yara da yawa amma ya’ki shan jinin kowa, duk jinin da bai sha ba yaron mutuwa yake, anyi asarar rayukan yara maza da dama, sai da aka kawo masa jinin *JUNAID* kafin Damusan nan yasha, atake Damusan ya samu lafiya ya mi’ke, jinin Junaid yana gudana ne a jikin Damusan,

Shiyasa da zaran ran Damusan ya 6aci shikenam za’a nemi hankalin Junaid a rasa”,

Tashin Hankali ya Junaid zai kasance???

Labari Umma take badawa!

“Tin lokacin da Damusa yasha jinin Junaid daga lokacin Junaid ya zamo ‘Karfafan Namiji, yanzu shekarunsa 30 cif Amma bai San sha’awa ba, ko kallon mace bayayi balle yaji sonta a ransa, sun gusar masa da duk wani tunaninsa,

Idan ran Junaid ya 6aci to kowa ya shiga uku, domin zai iyayin kisan Kai ba tareda saninsa ba,

Zai zamana duk wani ire-ire na Damusa zai rinka yinsa hatta kalar kukan Damusa zai rinka yinsa tareda gurnani kalar na namun daji,

Idanunsa zasu koma irin na Damusa, kukansa irin na Damusa, sannan ko wani lokaci zai rinka jin kamshin mutum,

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button