Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 55

Sponsored links

Abu Zainab ya katse masa tunani. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yanda Abu Zainab ya ƙagu ya sashi fahimtar bashi da isasshen lokacin tunani, zai bari sai ya samu nutsuwa ya bi hanyar data dace badan masu kurarin sunfi ƙarfinsa ba. Sai dan kawai baya son bin wata hanya daya jima da kyamatarta a ransa, amma da su ko inda yake basu isa tunkara ba balle jininsa…..

Barrister Abdallah Aas ya ajiye wayar daya janye manne a kunensa alamar waya ya gama. Kallonsa ya maida ga sakatarensa dake ƙoƙarin ficewa saboda ganin yana waya. “Suhail”.

Ya dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa. Amsawa yay tare da juyowa cikin girmamawa.

“Akwai damuwa ne?”.

“A’a Sir. Wani mutum ne dai ke buƙatar ganinka. Nayi ƙoƙarin fahimtar da shi kanada uziri amma bai saurareni ba”.

Ɗan jimm yay kamar mai nazari, sai kuma ya huro iska da kaɗa kai. “Okay ba damuwa shigo da shi kawai na gansa kona minti goma ne dan zan fita ne”.

A yanayin da mutumin ya shigo ya saka Barrister tsira masa ido, yakai zaune tun kan a bashi izini yana cigaba da bin office ɗin da kallo tamkar mai irge kayan cikinsa. Sai kuma ya juya ga Barrister tamkar wanda aka bama umarni ya miƙa masa hannu. Kamar Barrister zai noƙe sai kuma ya miƙa masa shima.

“Am sorry Barrister nasan baka Sanni ba. Na kuma shigo kai tsaye batare da neman damarka ba” ya saki murmushi da cigaba da maganarsa batare da ya bama Barrister ɗin damar cewa wani abu ba. “Kar sani na ya zama damuwar abinda ya kamata ka sani dangane da ni, mafi muhimmanci kawai kasan miya kawo ni”. Ya kai ƙarshen maganar da ɗakko jakkar daya shigo da ita ya ajiye saman tebirin Barrister.

“Waɗan nan kuɗaɗene da zasu isheka tsahon wani lokaci kana amfana, ina son ka manta da zancen aikin da surikinka ya kawo maka, idan son samu ne ma daga yau ka dakatar da shi shiga abinda bai shafesa ba”.

“Duk akan wane dalili zanyi hakan?” Barrister da ɓacin ransa ke yunkurowa ya faɗa cikin son dannewa.

“Ba dalilin ya kamata ka sani ba. Ƙin bin shawarar ne matsalarka Barrister”.

Cikin bayyanar fushin Barrister gaba ɗaya akan fuska ya yunkuro zaiyi magana ring ɗin wayarsa ya dakatar da shi hakan. Atare suka kalli wayar sannan suka kalla juna. Wayar mutumin ya nuna da sakin murmushi, “Bismillah”.

Barrister yaja ƙaramin tsaki da hararsa tare da kai hannu akan wayar dake cigaba da ɓurari……..

…….“Assalamu alaikum”.

Ya faɗa a daƙile saboda rashin sanin wanene. A maimakon amsa masa sallamarsa aka ambaci sunansa tamkar a lokacin ake raɗa masa shi.

“Barrister Abdallah Ibn Adam Aas! Kar kayi taurin kai, dan zaka iya rasa kanka dama waɗan da kake yunƙurin taimakawar. Ni umarni nake baka ba shawara ba kamar shi, domin hatta iyalanka ba zasu tsira ba daga tarko na”..

Ɗan zabura Barrister yay tamkar wanda cinnaka ya ciza. Daga can aka cigaba da magana cike da isa. “Suna hanyar zuwa gareka, ya rage naka tun yanzu ka raba gari da su, ka kuma gargaɗi surikinka. Na barka lafiya”. Yana kokarin yin magana ƙitt aka yanke kiran. Ciro wayar yay da sauri daga kunensa, ganin ta yanke yay ƙoƙarin kiran number.

Mutumin dake tare da shi ya miƙe yana dariya. “Barrister shawara karma ka wahal da kanka dan basake samunsa zakai ba har abada in har a wannan layin ne. Na barka lafiya”.

Da ƙyar Barrister ya kwato numfashinsa gab da mutumin zai fice. Cikin jarumtarsa ya dakatar da shi a ɗan tsawace. “Ni kurari ko gizago basa firgitani ai. Dawowa ka ɗauka trash bag ɗinka zai fi maka alkairi fiye daka barta anan ta zamewa rayuwarka BAYA DA ƘURA. wannan shawara ce”.

Har cikin rai maganganun Barrister sun sokesa. Amma kasancewar sa ɗan hannu a iya bariki sai ya saki murmushi. Batare da yace komai ba yay salute ɗin Barrister dake masa kallon ƙasƙanci yay ficewarsa.

Baya Kaka da Abu Zainab dake yunƙurin shigowa office ɗin suka ja dan kaɗan ya rage suyi gware. Suna masa sallama bai ko amsa su ba yay musu kallon ƙasa da sama yay wucewarsa. Basu damu ba, dan daga ganinsa kaga babban mutum. Barrister da aka bari da juyawar kai ya amsa musu sallama cike da son danne ɓacin ran dake a fuskarsa. Sun gaisa da mutuntawa kamar yanda suka saba. Fuskar Kaka da ɗan murmushi ya ce, “Ashe kuma an dace da sanin inda suke?”.

Murmushin ƙarfin hali Barrister yayi da jinjina kansa, ya jawo wani file dake gefensa. “Nima banyi tunanin abin zai zo mana da sauƙi haka ba Baba. Amma Alhamdullah addu’a bata faɗuwa ƙasa banza. Inaga muyi azamar zuwa ma kar’a samu wani tazgaro kuma kasan halin ƙasar tamu”.

Daga Kaka har Abu Zainab sunyi na’am da hakan. Duk suka miƙe babu ɓata lokaci suka fice kowa da abinda ke masa kai kawo a cikin rai musamman Kaka da Barrister…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button