Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 91-92

Sponsored links

Malam kunya ta Kama shi bai taba ganin irin wannan rashin kunya ba,Wise ce ta mikawa Santana Hannu Suka kawo zasu tafa sai Suka janye tare da hada Baki suka furta ba kyau kowa ya maida hannunsa, ana Mana babin wanka Mandula tace ai ni bana wani gaggautawa da cuccudawa ai kawai Malam na kwara da roba na wuce wajen to Yar

 

degree faranti ce ni, Santana da su Star harda shewa,Star tace ashe a ruwan ma akwai me tsarki da tsarkakewa to idan Mata da miji suna wanka fa amma dai shi ba matsala,Malam dai yace ai Yana da kyau sunna ce wanka da matarka,Wise ta rufe baki tana kunshe dariya tace Malam to kaima kana Yi wai,yace ae Alhmdllh Muna dan tabawa,Ido Muka zaro ai mun zaci banda ustazai yo Ustaz yayi ma bare tubabbun karuwai Papa kaga ta kanka cewar Wise ,Star ta kalli Malam tace Abul khairi Mazarawi? Yace naam dariya tayi tare da kifa kanta a saman cinyoyinta tace ya amsa wlh gaskiya Ina sonka ni Kaine ka birgeni da gani dai dai dani kake tana karewa wandon Malam kallo tace amma Malam daga wajejen Isra’ila kake ko, Malam ya Sha kunu Kawai irin ba Wasa, nidai Nace Malam ni Ina da aure ya mazaunin mace yake idan tana yiwa miji kukan shagwaba,Malam yace ba laifi wannan Abu ne me kyau duk cikin kara dankon kauna ne,nace tab Nawwar ka shiga Uku Malam yace da kyau,ya daina Wasa yaci gaba da biya mana Muna ta iya shege ya gama da sauri ya sake Mana nasiha sosai sannan yace gobe cikin darasi harda tarihin annabawa,Star tace toooo an kusa zuwa Suratul Yusuf suna ta murna Ina jinsu Dan ni na fisu ilimin addini da Wise ma tana da nata ba laifi,Malam ya tafi da yamma Me English tazo,tace banda hausa a nan ta Mana darasi Muna ji,tana ta Mana iyayin turanci,tace zamu Fara da Noun,nace now ta yanzu yanzu ko kuwa wata Hajiya Now din ce daban,Wise ta dinga dariya da malamar ma haka,munyi nisa da karatu Nawwar ya shigo a mota yayi parking cikin jerin motocinsa,a fili nace Excuse Zan karasa Ilimina a can tare da dafe kirjina nace My life ya dawo,Malama tace karatu muke fa, baki na bude nace Man of the world fa ake ce miki,My Hero,My Star haba malama ko daga birtaniya kika zo ai kya saurara min,tashi nayi na wuce abina,fitowarsa kenan na taho da gudu na fada kirjinsa nace I wanna be in your life,dariya ya saki yace ko karatun ne ya Fara aiki,dariya nayi nace a street na tsinta, daukana yayi kamar Baby a haka Muka wuce part dinmu

Bedroom na tayashi ya cire kayansa ya fada toilet,lekowa yayi yace Miko min key din can,daukowa nayi na Mika Masa ya damko Hannu na tare da jawoni cikin toilet din,nace yanzu fa nayi wanka,ai tayani zakiyi Yana min rada a kunne haka na hakura Muka yi wankan tare yana Wasa da sassan jikina haka Muka Gama muka fito tare da shiryawa,ya sa Kaya marasa nauyi sea blue ni kuwa guntuwar gown na saka peach and green me kyau sannan na fita kitchen na kawo Masa abinci,nice na ciyar da shi Yana danna waya har ya gama ci Muna hirar masoya, yace jibi zanje Abuja,murna nayi sabo da dama na gaji da irin yanda baya barina na huta,nace ai kuwa sai muyi ta karatunmu Allah ya dawo da Kai lafiya,Kallona yayi ganin Ina ta Jin dadi,kwafa ya ja wato murna ma kike yi to na fasa kuma ma Zan iya tafiya dake ai kina da ilimin addini, wani dukul naji yace ki hada Mana kayanmu sati zamuyi amarci sabo,tagumi na zuba haka na kumbura baki tare da cewa to,Murmushi ya shiga yi,Ashe tsokanata yayi dama ban sani ba haka na shiga hada mana kaya yace Wasa nake Miki,nace Allah ba matsala muje ko da gaske ne ai kana so Ina son abinda kake so,tsokanarki nayi tsakanin kafafunsa na dawo na zauna tare da maida kaina da gadon bayana saman kirjinsa, Wayar dake hannunsa ya ajiye gefe ya shiga Wasa da jikina sai da ya murzani son ransa sannan ya kyaleni lokacin malama ta gama darasinta har ta tafi ma,suna part dinsu sun saki kida sai cashewa suke yi Kamar basu ji Nasihar Malam ba Santana Yana can Yana ta faman murguda duwunsa Kamar na dan tsako.

Baffa kwana biyu ya rasa inda zai ga Mami Kawai sai ganinsa nayi a gidan yayi knocking Ina Budewa na ganshi na kalle shi Muka hada Ido kallon palon yayi ko Ina Kal Kal Yana zuba kamshi yace Yana nan Kuwa? Nace ae,shigo Mana,ya shigo ya zauna na durkusa na gaida shi sai kunyata yake ji ya tuna sanda ya kaini hotel,nace Baffa ya kawata Kuwa Star, har gumi yake yace dan Allah ki rufa min asiri karku fadawa iyalina da yarana ki rokar min kawar taki ta rufa min asiri,nace wlh ya wuce har abada baza mu fada ba amma idan ka daina fa,da sauri yace wallahi daga Sanda nasan kina tare da dana ban sake ba Kuma na tuba sahihin tuba bazan sake ba har abada Inshaallah,nace to ka dauka komai bai faru ba dan Allah ya wuce har abada Allah ya Kara kiyayewa ya Kare mu ya shirya mu,yace ameen Yar Albarka sai yanzu nasan Zina bata da amfani,ga zunubi,ga zubar da mutunci dama Indai sana’ar mutum kenan to Watarana sai yaji kunya zai iya Neman yarsa ma bai sani ba,nace wlh ai mu Kam Allah ya Kare mu yanzu ma duk su Star sun dauki hanyar tuba Nawwar ma ya samo Mana malami Yana koya Mana yaki da jahilci, Baffa yace madalla kaji Dan Albarka Allah yasa wannan ya Zama shine silar shigarsa Aljanna,nace Ameen Ameen Baffa Inshaallah damu daku a Aljannar ma a GRA muke,yayi dariy tare da furta ameen ameen,nace da anyi mashahuriyar Yar giya a aljanna,Baffa ya dinga dariya yace kin San inda Mamin Nawwar take kuwa? Nace Baffa ya akayi haka ta faru har saki uku kayi ganganci wlh uwar yaranka guda,Baffa yace to ba a kaunata a gidanmu shi yasa aka kyale ni babu me fada min gaskiya gashi nan yanzu kullum ‘yata sai nayi kuka,dariyar Baffa ta kamani Kamar ba surukarsa ba sabo da a bariki Muka hadu shi yasa,nace kaga ko ni ban San inda take ba wlh Amma Watarana tana zuwa nan,Baffa yace kiyi amfani da damarki a wajen dana ki samo min inda take dan Allah Hakuri Zan bata Kawai ta yafe min tun kafin hakkinta ya kamani Allah yasa dai tayi aure da wuri mijin Kuma ya saketa ta dawo wajena,Nace Baffa ai ko ba’a saketa ba sai mun kaddamarwa mijin dole ya sako maka matarka,Baffa yace da kuwa bani da kamarki a duniya Allah ya Miki Albarka bana so ma ta fito ta hanyar da ba daidai ba Indai Allah yayi za’a saketa ne again Kinga dama kuskurena nake so na gyara,cikin magana kasa kasa nace an gama Inshaallah zata dawo muyi ta Addua Kuma zan tsaya maka iyakar iyawata Baffa ai Kai namu ne tun a baya,

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button