Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 46-47

Sponsored links

Abincin da yace na dafawa Mami shi na zauna na tsara harda abinda bai sani ba sai da na Mata dambun naman kaza,nayi Mata snacks kala biyu komai a muzubi na musamman na zuba,na shirya komai da taimakon Baba kulu,sai da Muka ci namu Muka koshi sannan nayi wanka na shirya cikin doguwar Riga ya zanyi ya takura min da saka Kaya na mutunci,Ina Fitowa na dauki remote ya shigo da sallama na amsa sai ga Mami ashe tare suke,Murmushi nayi na Fara dariya kadan nace laaa Sannu da Zuwa Maminmu, tana shigo nace zauna dan Allah Zama tayi tana Dariya tare da furta Sannu Yan mata durkusawa nayi na gaisheta da ladabi ta amsa Nawwar ya saci kallo na,Baba kulu tana daki na kwala Mata Kira nace Baba fito ga Mami tazo Mamin Ogana Mamin saurayina tazo fito,Mami tayi dariya sosai tace ohh wannan yarinya,Baba kulu ta fito sun San juna Mami tana ganinta a gidan Khaleel Suka gaisa, nace bari a kawo ruwa,tace tafiya ma zanyi nace dama kwana Kika yi a nan Allah Mamin mu

Tace a’a kamar kin san Hutu zanje wani gidansa a bakin ruwa,nayi kneel down da sauri Kamar ana bani punishment nace laaaa kamar na sani dan Allah ki huta a nan idan ba kya son hayaniya zanyi shuru na nuna sama da yatsa na nace Allah harda dangwalar yawu na daga yatsaya nace Allah,Mami tayi dariya,nace zan Miki girki da komai kullum zaki ji Dadi Mami kin ganni Ina da hankali,kin na nuna kaina nace ni macece me kirki Ina da kirki,Gani da Fara’a,Kuma na iya kula da mutum,yarinya me hankali Irina ga kirki Allah Mami,dariya ta Kama Nawwar yanda na gigice harda hada gumi nake faman yabon kaina nace,Mami dariya take nace Kuma gani da Kamala da nutsuwa Allah ni nutsatsiya ce Zan sake nutsuwa ko Saurayina ai shima ya sani shi yasa kika ga ya nace min Mami yaki barina na tafi ya manne min Kamar chewgum Ina korarsa yana likewa to yaga nutsuwa ga kirki,in yazo Mami abinci in ta ce Masa sai yaci nace ci ci Mana Ina lallabashi ruwa wannan sai na zuba masa sai ya min shagwaba yake sha,Mami sai dariya take Sha Ina tonawa danta asiri,Nawwar ya riko hannun Mami yace tashi mu tafi dare na yi,Hannunsa Mami ta bige karka dameni,amma Nawwar sai ya dinga hararata ya tsare gida dole nayi shuru,a haka Mami ta Mana Sallama da ni da Nawwar Muka kwashe abinci muka zuba a mota Suka tafi na dawo cikin gida

Haka Nawwar yake sintiri a hanya kullum Yana kashe Mana kudi shine gidan Sabreen shine gidana yazo ya dauki abinci ya kaiwa Mami komai nike dafawa Mami yazo ya Kai mata haka yana kaita yawon shakatawa dan taji sanyi a ranta,su Sultana ta barsu suna gida sun dameta da ta dawo gida amma tace musu zata dawo ne su Kara hakuri shi Baffa ma bai San bata nan ba sabo da bai damu da ita ba.

Yau Ina wanka ya shigo sai da nayi wankan tsarki nayi Sallah sannan na zauna shiryawa ban San ma yazo ba suna Palo tare da Baba kulu suna hira sama sama har na fito sanye cikin wasu Pakistan riga da wandon wando ka rantse skert ne wandon wani fari kal rigar Kuma dark green taji ado ta hadu a cikin kayan da ya siya min ne mayafin a kaina na daura na fito tare da neman kujera na zauna sannan nace Ina yini ka yini lafiya,ya Mami? yace tana lafiya nace mashaallah daga haka ban sake magana ba abinda bai saba gani a wajena ba Kuma ba haka ya saba ganina ba ya sanni da surutu,yace lafiya? Nace me ka gani? bana son zancen banza mene ne ke faruwa,dan lips dina na turo tare da furta gidanmu na tuna nayi missing dinsu kasan inda ka taso dole ya zauna a ranka, ni Kuwa a raina so nake yace naje can kauyenmu ta nan zan samu naci uban Dagaci zuga guda zamu yi, Tsaki ya ja tare da furta mutumin da yaso yayi raping naki sune abin tunani, kasan idan ka taso ko me ake maka dole kaji a jikinka,Mikewa yayi yace baki da aikin yi ne komai Kuna da shi ko?nace ae yace to dama tafiya zanyi gabana nane ya Fadi nace zuwa ina? zaka Dade? Baba kulu dama tuni ta koma kitchen wajen girkin da take mana,yace zanyi kamar 3weeks,Ina ne? Umrah zance,wow na furta ayi Mana Addua Murmushi yayi yace wa zai kulaki tunda baza ki shiryu ba Mamina kadai Zan yiwa,nace please ka taimakawa yar tsuntuwa Yar lelenka ce fa ni,harara ya watsa min,nace abincin Mamin fa? Ai ta koma gida Yara sun dameta ta koma sati Daya fa Kawai tayi ae Mana ai ta huta haka,mikewa nayi tsaye nace muje na rakaka kaje Dani airport yace no da matata zanje,dariya ta kamani nace sai kace matar kirki Yarinyar da kirji kamar Allo, Murmushi yayi yace Sabreen ce Yarinyar ki? Shekarun mu daya da ita to mate dina ce,dariya ta kamani nace kace tsohuwar guzuma aka aura maka yanzu nasan local government din ma yayi yaushi ya yamutse,bana son rashin mutunci ya furta yana bata rai ,okay naji idan zaka dawo zanje airport dakkoka na iya mota, dan Allah yace okay,Na tsaya a gabansa Ina kallonsa na furta I will miss you na rungume shi,kin manta dukan da Kika Sha rannan ko,da sauri na ja baya Ina tambaya yau zaka tafi kenan yace ae Inshaallah zuwa dare, Kai na jinjina,Ni Kuwa nace za a sha zam zam a cika ciki shi yasa masu kudi kuke Mana wayo ku dankara laifi ku tafi Saudiya ku nemi yafiyar Allah, juyawa kawai yayi ya fice abinsa.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button