Hausa Novels and Stories

Daulatul Arab Hausa Novel Complete

Sponsored links

Danno hancin motarshi yayi kan titi gudu yake ba kakkautawa hakan yasa duk wani mai motar daya hangeshi kokari yake yabashi hanya ya wuce

 

 

 

 

 

” FERAS yakamata ka rage gudun motarnan haka kasanfa layin babban masallaci zamubi kuma gashi kaware kiɗa bayan sallar azahar ake yanzu

Wanda aka kira da suna FERAS ne naga ya kunna sigari ya kalli abokin nasa yace

 

 

 

” to shek yasir mai zai hana na saukeka a masallacin ayi sallar dakai

 

 

 

” gaskiya FERAS bakada dama ina ni ina yin sallah koka manta jiya nasha giya kaga kuwa nida sallah sai nan da kwana Arba,in

Wani murmushi FERAS yasaki yace “tunda kuwa kasan sallah ta haramta agaremu muda muke shan giya karka kara yimin korafi akan tukina, ” ok shikkenan naji yanzu dai muyi sauri mukarasa inda zamu kafin lokaci ya kure mana

 

 

 

 

 

Nan suka cigaba da tsula gudu abinsu suna busa sigari ga tashin kiɗa duk inda suka gifta sai kaji kanka kamar ya tsage saboda karar kidan

Feras ne ya hangi wata jar mota a gaban sa kowa yana matsa masa ya huce amma motar taki matsawa hakan yasa feras cikin fishi da hassala ya karawa motarsa gudu ya daki wannan jar motar

 

 

 

 

 

Gaba ɗaya robar bayan jar motar yacire hakan yasa mai jar motar fitowa cikin bacin rai danganin wanda ya masa wannan ɗanyen aikin

 

 

 

Shima feras futowa yayi yanufo mai jar motar yana zuwa yaga wani dattijo ne yake jan motar

 

 

 

cukume shi feras yayi kan kace kwabo ji kake tass feras ya ɗauke dattijon nan da mari hakanne yajawo hankalin jama,ar gurin kansu

” uban wanene ya ɗaure maka gindi a kasarnan da har zaka gogarmin motata to wallahi sai ka karbi mukullin kaje ka sauyomin wata inba hakaba ka kare rayuwar ka agidan kaso

 

 

 

Dattijon nan yanajin haka ya fashe da kuka ya tsugunna yadafa kafafun feras yace

 

 

 

” dan Allah yallabai kaimin rai kataimake ni taya mai motar milion 20 zai iya biyan mai motar milion 100 na zubda girmana yallabai na dafa kafafun ka kataimaka min kayafemin

 

 

 

 

 

Duk da gurin ya ciki da mutane ƴan kallo amma babu wanda ya iya magana acikinsu bare susa baki feras ya yi hakuri saboda kaf titin babu wanda baisan feras ba dakuma goyan bayan da yake dashi uwa uba ga ɗinbin dukiya kamar baza a mutuba

Cikin isa da izza haɗi da alfahari da girman kai feras yaɗago yana watsawa mutanan gurin wani wula kantaccen kallo yace

 

 

 

” kai dattijo babu wata mota data isa ta gogi tawa kuma tacigaba da moruwa dan haka indai kanaso na yafe maka saikun haɗu kaida waɗan nan mutsiyatan karnukan kun ragargaje motar ka

 

 

 

 

 

Gaba ɗaya wajan babu wanda bai girgizaba amma kowa yasan wannan shine zabi mafi sauki dan idan ba hakaba ta tsoho tagama karewa shima tsohon a karan kansa ya yarda daya salwantar da motar tasa indai feras zai kyaleshi

Gaba ɗaya wajan babu wanda bai girgizaba amma kowa yasan wannan shine zabi mafi sauki dan idan ba hakaba ta tsoho tagama karewa shima tsohon a karan kansa ya yarda daya salwantar da motar tasa indai feras zai kyaleshi

 

 

 

Juyawa dattijon yayi ya kalli jama,ar dake gurin yana zubar da hawayen bakin ciki yace “ya ku ƴan uwana kuzo ku taimaka min wajan ciki sharaɗin yallabai

 

 

 

 

 

Duk gurin babu wanda bai tausayawa dattijon nan ba amma shikwa feras ko a jikinshi haka ya zauna saman motar sa ya kunna taba yana sha har suka gama filla filla da wannan motar tukunna yaja motarsa suka tafi

” Baba baba ka dakata nace maka

 

 

 

Cikin sanyin jiki mutumin ya juyo ya kalleta zuciyarsa cike da tsoran ƴar tasa yace ” naam FAHDA,

 

 

 

Tana karasowa ta cukumi kwalar baban nata tace

 

 

 

” wallahi kai mugune azzalumi shekarata 30 duk nazama uwar mata babu aure duk lokajin da miji ya fitomin sai kace ba yanzu zaka aurar dani ba to yanzu ankai ga ko samarin dazasuce sunasona ma babu duk sun gudu saboda gani suke natsufa bazasu iya aurena ba shiyasa yanzu nazo koka ne meni dakanka kabiyamin bukatata kokuma kafita kanemo duk wanda zai sadu dani ayau ɗinan

 

 

” lahla ya ɗan,uwana dama nazone na faɗa maka dan Allah idan da hali kataimaka mana kaɗan rage karar kiɗannan kasan yanzu dare ya tsala karfe uku kuma inada yakini a unguwarnan bama manya ba ko jinjiri bazai iya yin bacci ba koga hayaniyar ku kadai barekuma kidan

 

 

 

 

 

Lokaci ɗaya fuskar FERAS ta cenza izuwa kalar hassala yaɗaga ruwan giyar dayake hannunsa ya tuttulawa shek,ali akansa nan da nan abokan FERAS suka fara shewa suna tafawa feras

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button