Hausa Novels and Stories

Alkawarin Zuciya Complete Hausa Novel

Sponsored links

Ganin baida niyyan amsashi yasa Mamu ya fizge pipe din shisha dake bakinshi yace “kafara ko ina maka magana kamin banza” ahankali yabude idanunshi dasuka wani lumshe sukai yaushi da idanda zai kalli mace dasu sai lissafinta yarikice sanan yazubasu kan Mamu kaman ance yay magana dan dole yace “what”? Dan murmushi Mamu yayi da hannu yamai alamu yace “look over to the counter ga budurwanka chan, stalker dinka tazo sai kallon ka take wlh, haba Zayn kaiko bazakaji tsoron Allah ka kula yarinyar nan koda sau daya bane tunda dai ta kasa maka magana for morethan 2months yarinyar nan kullum binka take tana stalking naka tana kallonka u know she really really likes u waikai maisa kacika wulakanta mata ne eh? Anyway I don’t blame you ni wlh in mace ne banmaga abin so ajikinka ba mutum dukgaka nan kalan asibiti farin fata kalan cuta, duk baku da karfi” dan murmushi yayi dan yasan Mamu so kawai yake yajashi suyita surutu this afternoon shikuma baida time dinan, hannunshi yamikamai alamun yabashi shishi shi, ijiye pipe din shishan Mamu yayi kan table din gabansu yace “Ya isheka hakanan gashinan duk idanunka sun chanza launi, munada lectures yanzun nan fa I think in the next 5min” dan tsaki yaja yasa hannu yadauki pipe din shisha yacigaba dasha abinshi yana daddanna wayanshi yana hura hayakin ta hancinshi batare dayama daga kai ya kalli inda Mamu yacemai yarinyar nan takeba Mamu nabinshi da kallo yarasa yanda zaiyi yaraba Zayn da shisha, shima bawai bayasha bane no but occasionally yakesha, shiko Zayn zai iya wuni yanashan shisha hakanma yasa baya iyacin abinci sosai, ganin yasake lumshe idanu yasa Mamu yaja tsaki yamike tsaye yace “dalla Malam wuce mutafi” bude idanunshi yayi dasuka dan kankance sukaija sanan ya watsama Mamu harara kafin ahankali ya ijiye pipe din yamike tsaye dogon namiji ne nagaske, budadde sanan kuma cikakke irin mazan nanne da ake kira da burin mata, car key dake kan table din yadauka yana rikeda wayanshi yay gaba abinshi batare daya cema Mamu komi ba yay hanyar kanta.

 

 

 

 

 

Tundaga nesa ta hangoshi ya dumfaro gaban kanta, duk taku daya dazaiyi saita jishi har kirjinta yana amsawa, tun kafin ya iso wajen wani kalan kamshin dayakeyi dayake neman sata ta haukace sabida sonshi ya lullube mata hanci ganin ko’ina najikinta yadau kyarma yasa ahankali tasa hannu tadauki cup na drink dinta takai bakinta still tana kallonshi ta gefen idanunta daidai ya iso ya tsaya dab da ita dasauri bartender din yazo yace “u done sir” bai amsashi ba yasa hannunshi a wandonshi yaciro wallet dinshi yabude yana kokarin zaro kudi ko kadan batasan drink din yamakai saman hancinta ba tsabagen yanda take kallonshi kawai numfashin dazata shaka ta shaki wine din wani irin mahaukacin shakewa tayi dabama tasan lokacin data saki cup din akasa ba tana wani kalan mahaukacin tari wine nabin hancinta suna fita idanunta sunyi ja kwalla yacikasu dawani kalan sauri daga Bartender din harshi suka juyo suna kallonta dasauri Bartender din yataho ta saitin gabanta yace “sorry Miss” dudda tarin datake kokarin danne tarin take tana kakalo murmushi dan wanan kwafsin haka har ina baki tabude zatai magana wani tarin yakara sarkaketa wine din na fitowa daga bakinta yana diddiga akan white wandonta duk yay staining sabida Jan wine ne, kaman daga sama taga wani clean white handky agabanta kamshin da ajikin mutum daya tall a duniyan nan takejin kamshi taji yana fitowa daga hanky ahankali tadago kanta sama tanabin Tundaga handkerchief din dakallo harzuwa white hannun dake rikeda shi zuwa kan fuskan Zayn dake kallonta in the eyes, wani sabon bugawa zuciyanta yashiga yi hannunta har rawa yake tasa takarba zatakai kan fuskanta dan sharewa shikuma yajuya ya ijiye kudaden dayariga yaciro daga wallet dinshi yadaura kan kantan yajuya yawuce batare daya kara bata second look ba, ahankali ta janye handky dagakan bakinta tabishi da kallo harsaida yabace ma ganinta sanan tasauke ijiyan zuciya kafin ahankali tasauke kanta tana kallon handky din ko kadan tama manta inda take rungume handky tayi akirjinta tana murmushi sosai.

 

kaman numfashinta sai dauke, kirjinta nawani irin racing, this is the first time take ganinshi ahaka, ganin still kallonta yake ba yabo ba fallasa kuma bai fasa abinda yake ba wato sharekanshi da karamin towel din dayake rikedashi, yasa taji wani bala’in fargabanshi na cikata jin baice komiba dakyar tadaga hannunta tamai pointing kofan dakinta dake kallon nashi tace “actually that’s my flat, yanzun nan naganka shine nace uhmmm bari nakawo ma” dan yatsine fuska yayi amugun wulakance ya kalli handky datake mikamai tundazu har hannunta na neman sagewa yace “I don’t need it, discard it” yaja kofan zai maida yarufe da sauri tace “uhmmm wait please” chak ya tsaya yana kallon fuskanta da fuskanshi dababu alamun rahama akai face dinshi looking kaman zai maketa, tagefenshi taleka tana kallon indomie da taga yafito dashi zai dafa yacika ruwa a babban pot yazuba albasa aciki ya fasa kwai aciki ruwan na kumfa sosai, dan murmushi tayi cikeda shakkanshi tace “are you trying to cook indomie”? Yana kallonta still a bala’in wulakance yace “uhn” kaman dole akace yay maganan, murya chan kasa cikeda shakkan abinda zatace tace “that’s not how to, lemme cook it for you p…..please” wani kalan wahalallan tsaki yaja ko kunyanta baijiba yace “banso” sanan yay slamming door din on her face batare dayama jira maitake shirin cewaba, kuka taji yazo mata wuya tadaure tahanashi fitowa tadade ahaka awajen sanan ahankali tajuya tawuce takoma dakinta zama tayi tana kallon handkerchief din tama rasa meke mata dadi, tunda take bata taba shakkan wani namiji ba sai wanan menene shi? Jibeta fa tanada kyau babu namiji da bazata iya daukemai hankali ba shi waye, enough of all this, tashi tayi fuu tai kofan tabude tafice sanan direct tai dakinshi ta danna door bell baa wani dauki lokaci ba wanan karan tabude kofan koyana expecting wani ne oho, churus ya tsaya ganin yarinyar dazu, wani irin faduwa gabanta yayi ganinshi dagashi sai dogon wando na Jean da Riga a hannunshi dabai Riga yasaba yanada wani irin broad chest ga cikakken shoulder parts garai, kasa magana tayi saiwani kalan kallon kirjinshi datake lips dinta na rawa tana kallon dark aroelas dinshi, ahankali tace “l…..l….ove……you…..Z….Zayn” Tundaga sama har kasa yake kalleta sanan yace “ke kikama kanki” wanan Karan wani slamming kofan yayi on her face saida yataba goshinta ahankali tajuya kaman an kashe mata yaran ciki tawuce side nata ta zauna dirshan akasa, tana zaune awajen taji fitowanshi yafice, kiri kiri kasa zuwa class din datake dashi tayi sabida yanda komi baya mata dadi.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button