Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 30

Sponsored links

Wlhy gaba ɗaya kaina ya kulle Akia, shin yarinyar nan wani ƙulli ne take son yi dan ta kuɓutar da kanta saboda tasan babban burin kowa sanin mai kashe matan Abni ne? ko kuwa gaskiya take faɗa? Idan gaskiya take faɗa taya akai tasani mu a tsahon shekaru muka gagara ganowa? Anya kuwa shigowar yarinyar nan cikin masarautar nan tun farko bada wata ƙullalliya ba?”.

 

Shiru babu alamar Malikat Bushirat zatace wani abu, hakan bai damu Jasrah ba ta cigaba da faɗin, “Al’amarin Mammah ya cigaba da bani tsoro a wannan gaɓar. Anya ba akwai abinda take ɓoye mana ba daya kamata mu sani?”.

A karo na farko Malikat Bushirat ta ɗago ta dubi Jasrah. Sai kuma ta miƙe cikin yanayin ƴar zabira. “Kamar mi kike tunani?”.

“Abubuwa da yawa Akia. Ciki harda halayyarta ta yanzu dake bayyanar da ita a mara gaskiya. Zuciyata na rayamun abubuwa da yawa fiye da yanda kike zato. Abin tambayar anan miyasa take goyawa yarinyar nan baya? Miyasa take son bata kariya? Bayan gudan jininta ta shirya halakawa? Ki duba kiga yanda taƙi bamu goyon baya akan shari’ar nan ita da Ammarah. Yarinyar nan ita aka fara kaiwa sashen Abni, kuma ita ta kaita, batai ko ciwon kai ba aka kai wata daga baya ta rasa ranta. Mi hakan ke nufi? Kaɗan daga cikin zarge-zargena kenan”

Kai kawai Malikat Bushirat ke jinjinawa alamar gamsuwa da bayanin Jasrah, dan itama wannan tunanin ya jima yana mata kaikawo a zuciya. Taƙi fiddashi ne saboda tuna halayen Malikat Haseenat ɗin masu yawa kafin yau, amma yanzu kam zuciyarta na mata rawa akan a bubuwa da yawan gaske……

Barbushi dake kwasar dariya bayan gama sauraren Miran Jasim da Miran Arshaan ya tsagaita dan kansa ya tamke fuskar tamau kamar bashi ne yayi ba. “Ƙwarai kuna a tsaka mai wuya, tsakar da in har bakinta ya buɗe ta furta ƙarshenku yazo. Abu ɗaya zamuyi akanta, idan mun taki sa’a kun tsira. Idan akasin hakan ya kasance ku zargi kanku….”

 

Komai basu iya sunce ba, dan zuciyarsu ta fara saka musu shakku akan gazawar Barbushi. Inba gazawa ba taya ƴar yarinya ƙarama zai dinga nuna kamar ta gagaresa. Bayan a da ya musu ayyuka manya da har a yanzu suke taka rawa da bazarsa. Ransu ɓace suka baro wajen nasa, zukatansu na matsanancin ƙuna, kowa kuma da abinda yake tattaunawa da ransa akan matakin ɗauka. Dan ko ana ha maza ha mata bazasu bar Iffah ta cigaba da numfashi ba a wannan gaɓar. Kai hatta da uban gayyar za’ai ƙurun-ƙus a wuce wajen dan sun gaji da gafara sa basuga ƙaho ba. In ba hakaba yarinyar nan zata ɓallo musu aiki….

Tun zaman shari’ar nan ta kasa zaune ta kasa tsaye. Ta rasa makamar kamawa. A lissafi bayan boka Ruƙuƙi ta ziyarci manyan bokaye a ƙalla huɗu amma amsa guda suke bata bazasu iya mata aiki ba ta koma ga UWA. Tsabar takaici har kuka tayi, kuka irin wanda ake kira kuka data ɗauka tsahon shekarun da bazata iya tuna sanda tayi makamancin sa ba ma. Jin tsanar Iffah take fiye da komai yanzu a duniya. A kwanaki biyun nan da suka gabata bayan zaman shari’a ta yanke shawarar gwada kasheta amma duk hanyar da tabi sai ta sameta a toshe. Wannan ne ya sake ƙona mata rai da sake jin raɗaɗi mafi girma.

 

(Ki ajiye komai ki sake komawa ga uwa, karki bari wahalarki ta wuce a banza) shawarar aminiyarta ta sake dawo mata a karo na babu adadi. Jagwab takai zaune, cikin don danne hawayen dake ƙoƙarin zubo mata tace, “Mike shirin faruwa da ni ne haka? Shirin dana ɗauka shekaru kusan arba’in inayi ne wata mitsitsiyar halitta zata zama sanadin rushemin, micece ita? Mi take takama da shi?” hawayen da take dannewar suka zubo saboda radaɗin da take ji. Bata da sauran zaɓi a yanzu face sake nemo UWA. Zumbur ta miƙe tamkar wadda aka tsikara. Ta lalubo kayan surkullen da take kiranyen uwa da su, da ƙyar ta gano robar da hayaƙi ke ciki ta bulbula a burner, take ɗakin ya harmutse har baka iya ganin komai, ita kanta numfashinta har wani fisgar yake tsabar ƙarfin hayaƙin. Idanunta ta rumtse tare da zubewa bisa gwiwunta ta fara hurwa na kiranye cikin yaren surkulle. Amma tsahon lokaci babu alamar uwa, har hayaƙin ya Kore, bata gajiya ba ta cigaba tana mai sake ninka rauninta (Wa’iyazubillah).

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button