Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 101-102

Sponsored links

Bikin Star muna can ana warwasawa Nawwar sai gobe daurin aure zaizo sai waya muke su Wise suna ta zirga zirga,in kaga Star sai kace ba ita bace irin gyaran data sha,Ustaz sai wani bugo waya yake,dare yayi Muna kwance dukkanmu Wanda Suka rage,Yan Uwa suna ta hada hada,Star tana waya da shi tace karfa gobe na ganka da rawani sai kace wani liman ato wannan shaddar da na zabo maka aka dinka ita zaka sako dama itace ta daurin aure ai,Malam yace dama yaushe ni na Isa ranki ya dade ai sai abinda kike so,kayan ke Kika sa na dinka set goma Sha biyar ai sabo da angwanci sai kace na hadawa kaina lefe takalma ma gasu nan kin zaba min na siya,sai nake ganin Kamar lefen da na hada Miki akwati biyar sunyi kadan,Star tace a’a sunyi gaskiya ba makusa Kaya fa ka zuba masu tsada,yace wato ainihin Yayata ce ta hado kayan suna son ki,Star tace na gode musu,sun dade suna waya harda cewa gobe i yanzu muna tare,Star tana ji ta daki Mandula kasa kasa yanda bazai ji ba tace kinji Malam abar kaikayi take Masa,dariya Muka yi tayi sauri ta datse Wayar tana cewa aikin banza sai ya ji ku Kuma ku fa ba a sirri daku.

Washe gari 2pm aka daura Auren Aisha Star da Angonta Abulkhair akan Sadaki dubu dari,Sai Kanwarta Saima da Angonta itama Sadaki dubu dari, Star tana Jin labari an daura taci gayu cikin wani dakakken leshi pink, Fitowa tayi cikin danginsu da take Jin haushin su basu taimaka musu ba a rayuwa sai da biki yazo sun zo sun dame su suna murna Kamar wani kaunar su suke yi, tace Dan bakin ciki sai dai ya sheka lahira ban balbalce ba bamu shiga wani hali ba,Kuma cutar da ake ce min zata kashe ni HIV Allah ya tsare baiwarsa gashi na auri malami Ustaz ma kuwa Kuma me hankali,Kanwata ta samu Ilimi Kuma uwata taci me kyau ta Sha me kyau Allah bai bamu kunya b…Maman Star ce tazo tace wallahi ranki zai baci idan baki bar Maganar nan ba,Star Allah yayita da biyayyar iyaye bata musu ko kadan Shuru tayi ta dinga chasa uban rawa a kidan da su Saima Suka kunna da kawayenta speaker suna bin wakar Auta mg boy kin Zama amarya.

Saima ma shigowa tayi ta rungume Star suna rawar su a haka suna bin wakar ana ta kallonsu,wata tsohuwa tace Yara man kaza Indai Namiji ne ba dan goyo bane,su fa gani suke Yi Babu Kamar su yanzu a dacen miji zaku ci ubanku ku tambaye mu halin maza mu baku labari,Taron abokan Ango gaba daya sunzo Yan Izala sun Sha shaddoji sai kamshi sukeyi,Saima kunya taji ta daina rawar amma Banda Star a gaban abokansa manyan malamai na sunna harda shugabannin Izala sun zo amma Star Hannun Malam biyu ta riko suna facing juna,mu Kuwa da su Wise sai hotuna muke musu da videos tunda yace ba party shi dan Izala ne,Malam kunya ta kamasu,Mandula tace Malam anzo hannu,sai da maza Suka Yi dariya ganin yanda Muka Raina Malam,kidan aka kashe nazo nace video nake Malam,Star tace Abukhair gyara Wai ba wani Malam yanzu ita Kam yanzu ba Malam,daga baya Kuma sai ga Nawwar ya shigo cikin arniyar shaddarsa arsh Kamar shine angon Yan Mata da dukkan Mata sai kallonsa suke,wata na maida Kansa Ina Masa video Ido Muka hada ya harareni Yana Murmushi Wai na saka karamin mayafi,ya wuce Suka gaisa da Maman Star da danginta suna ta Masa godiya,ana cewa Baban Star ne shine ya dauki nauyin komai,

Ni Kuwa Ina ta Masa video duk abinda yake Ina dauka,Ina ji Maman Star tana cewa ai shine waliyyin Aisha shine ya daura Mata aure,a Raina nace iyye su Nawwar an girma harda walicci,angwaye Kuwa ana yin pics a gurguje Suka tafi,Nawwar ya fito dukkan mu Muka tattara har su Yar Zabil aka mana pics sannan yace min tafiya zanyi sauri nake Ina da meeting 4pm ,ku taho fa yau yau naji ana cewa sai gobe za a kawo Amarya ba wannan zancen,Nace Maman Star tace ita ba Wanda zai zauna ayi biki biyu daga yau an gama yanzu zamu taho da Amarya,yace okay danginta mutum nawa? Nace ai har Mamanta sai wata a Dangin uba shike Nan Wai,yace to shike nan hakan ma yayi muje ki rakani,Ina zuwa a motar Airport aka kawo shi ya Shiga ya koma ni Kuma na koma muka ci gaba da bidiri,Ashe Papa ma yazo sai ji Muka yi ya Kira Wise a waya Wai Yana kofar gida,can Muka je Muka gaisa,bai dade ba ya tafi shima.

5pm muka Fara Kai Saima dake a garin take Mama harda kuka,nace yanzu wa za a barwa Mama su zauna tare? Star tace Yar uwarta ce daga Kauye Haule ta dawo wajenta tunda itama Dattijuwar ce tare zasu zauna,nace okay Muna dawowa muka bi jirgi Muka koma,Wise mijinta ya dauki nauyinta,Sera Kuwa Sabeer ya biya,Yar Zabil Ahmad tubabben Saurayinta ne, sai Santana shi ya biya Kansa yazo daurin aure ya koma abinsa,sai Mandula da ni Nawwar ya dauki nauyin mu.

 

A cikin tawagar Angwaye wani yaro Wanda bai fi 26yrs ba matashi ya makale Wai Mandula yake so,Muka ta Mata dariya tace Allah ya kiyaye min,wani ma a yobe Yana sonta yace ita baza ta bar kudu ba ta Saba da can Indai ba a kudu ba baza tayi aure ba,Haka wani Dan Kano shima yace Yana so wlh mutumin arziki da shi tace Sam bata so.

Amma yaron nan sabo da ta ganshi kyakyawa dashi handsome Dan fari Wai shi ya mata Indai Yana da aikin yi shike nan yaron da bashi da bashi da komai yanzu ma ya gama University shima Dan yanzu ana karatu da wuri ne shi yasa har ya gama.

 

 

Mun taho da Amarya a jirgi,jirgin cike yake da mutane Star tace haka ake dakko Amarya ba guda wa yasan Amarya ce da Allah ku girgiza Mana mutanen jirgin nan,Yar Zabil da su Mandula,Sera suka saki guda Suka dinga sharara guda suna tafi dukkan mutanen jirgi kallo ya dawo kanmu,hausawa suna cewa Amarya Suka dakko,Ni dai Ina ta video suna guda da tafi mun dakko Amaryar Ustaz,Mama ce ta gaji tace Kai dalla kuyi Mana shuru muna sararin samaniya rayuwar mu tana hatsari amma ku guda ma kuke,Muna zuwa Muka ce anzo anzo yeeeeeeee sai sabuwar guda ana ta dariya.

Muna sauka Malam tuni an turo motoci uku Muka shige sai gidan Star bamu da wani nisa da ita,Gidane me bene Hawa Daya dan cif cif Kyakyawan gida,gate me cin mota biyu Masha Allah gidan yayi ya hadu kayan daki na kirki itama Nawwar ya zuba Mata ko Ina an tsara mata,mun Kai dukkan kayanta da lefe can,Mama harda kuka taga gidan yarta tayi ta Mata nasiha sannan a ranar Suka juya a jirgi Nawwar yasa Santana ya rakasu har gida ya dawo sabo da tsofaffi ne basu taba Hawa jirgi ba.

 

Star ana gadonta a zaune mun Kara gyara ko Ina mun turare ko Ina da kamshi,9pm sai Malam muka gani ya canja wankan yadi me kyau yayi kyau sosai dama gashi dan Kyakyawan Ustaz, Wise tace to nifa Sweety yazo daukana ta fice wajen Papa yazo daukanta da kansa yau kwananta ne, tana shiga mota yace ko girki baki min ba tace na gaji yau gaskiya mu wuce mu ci a restaurant,yace to Suka wuce hadadden wajen cin abinci a can Suka ci Suka koshi harda take away na kayan makulashe Suka dawo gida.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button